Muhimmanci da hukunce-hukuncen noma a Musulunci (1)
Hudubar Injiniya Isma’il M. Cindo Gotomo Masallacin Juma’a na Haliru Abdu, Birnin Kebbi Huduba ta Daya Yabo da godiya sun tabbata ga Allah, wanda Ya zuba mana ni’imominSa a bayyane da boye. Kuma Ya hore mana gaba dayan abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin kasa a kan baiwa da falala daga […]
Hudubar Injiniya Isma’il M. Cindo Gotomo
Masallacin Juma’a na Haliru Abdu, Birnin Kebbi
Huduba ta Daya
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah, wanda Ya zuba mana ni’imominSa a bayyane da boye. Kuma Ya hore mana gaba dayan abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin kasa a kan baiwa da falala daga gare Shi. Lallai a cikin wannan horewar akwai ayoyi (masu nuni ga kadaitar Allah) ga mutanen da suke yin tunani.
Ya Allah Ka yi salati da sallama ga wannnan da Ka aiko shi yana matsayin rahama da jagora ga talikai – Annabinmu, masoyinmu, macecinmu Muhammad (SAW) da jama’ar gidansa da sahabbansa baki daya.
Bayan haka, ya ku masoyana a cikin Addinin Allah! Ba shakka sana’ar noma tare da makekin fadinta da yawan rassanta da yawan dabarun yinta, musamman na zamani da matakan yinta a nazarin kimiyya da kuma a aikace da gwababan amfanoninta; tana daga cikin mafiya girman sana’o’i tun a da, da kuma a yanzu! Allah Madaukakin Sarki Ya ce: “(Allah) Shi ne Wanda Ya sanya muku kasa horarra, to, ku tafi a cikin sasanninta, kuma ku ci daga arzikinSa, kuma zuwa gare Shi ne tashin (domin Hisabi da sakayya) yake.” (Al-Mulk:15). Game da wannan ayar, wadansu malaman tafsiri sun ce “A cikin wannan ayar akwai nuni zuwa ga (kokarin) neman arziki da kuma (himmatuwa ga) sana’o’i” (Attafsirul Muyassar). Ba sai na fada ba, kowa ya san cewa sana’ar noma tana daga cikin mafiya karfin hanyoyin samun arzikin Allah na halal. Kuma ku lura da zancen Allah da Ya ce: “Kuma Yana sassaukar muku da arziki daga sama.” (Ghafir:13).
Ma’ana: Allah Yana (saukar muku arziki daga sama) ta hanyar yawan saukar da ruwan sama, wanda yake da ruwan saman nan Yake fitar muku da nau’o’in abincinku daga kasa da kuma na dabbokinku (Tafsirin Dabari).
Har ila yau kuma, Allah Ya ce: “A cikin sama ne arzikinku yake (fitowa) da kuma abin da ake yi muku alkawari.” (Az-Zariyat:22). Wato sababbin arzikinku da na abin da za ku ci ku rayu daga sama yake; shi ne kuwa ruwan saman da yake sai da shi ne garuruwa da bayin Allah ke rayuwa. Haka nan abin da ake yi muku alkawarinsa na lada da na azaba – shi ma rubuce yake a sama. (Safwatut-Tafasir).
Daga cikin falalar aikin noma, akwai fadar Manzon Allah (SAW) cewa:
“Ba wani Musulmin da zai dasa wani (abin) dashe, face ya kasance duk abin da aka ci daga gare shi (abin dashen) sadaka ne; haka abin da duk aka sata daga abin dashen nan sadaka ne. Ba abin da wani zai tauye (ko ya rage) daga abin dashen nan face ya kasance sadaka ga wanda ya yi dashen. (Muslim ne ya ruwaito)
A wata ruwayar ta Muslim daga Jabir din dai, Manzo (SAW) ya ce:
“Ba wani Musulmin da zai yi wani dashe, ya kasance wani mutum ko wata dabba ko wani tsuntsu ya ci daga abin da aka dasan nan, face (abin nan da aka ci) ya kasance sadaka gare shi (wanda ya yi dashen) har zuwa Ranar Kiyama.”
A ruwayar tasa (shi Muslim), aka ce:
“Ba Musulmin da zai yi wani dashe, ko ya yi wata shuka, sai ya zamani wani mutum ko wata dabba, ko wani abu, su ci wani abu daga shukar nan, face abin (da aka cin) ya kasance sadaka a gare shi (wanda ya yi shukar ko dashen).”
Bugu da kari, a zamanin Sayyidina Umar (RA), aikin noma shi ne babban hanyar samar da kudin shiga ga gwamnatinsa. Kuma gwamnatinsa ta karfafa, kuma ta taimaka wa manoma – da Musulmi da wadanda ba Musulmiba! Kuma Sayyidina Umar (RA) ya sa an haka manya-manyan hanyoyin ruwa da madatsun ruwa (saboda noman rani), da manya-manyan gonaki; dukdai saboda muhimmanci da ya bayar ga sha’anin noma! Don haka, kukan kurciya jawabi ne! Amma mai hankali ke ganewa!
Yaku ’yan uwa! Ba shakka, akwai fa’idoji masu yawa tattare da harkar noma. Daga ciki akwai fa’idar wadatar abinci da samun na-kai da bunkasa tattalin arziki, kamar yadda muke shaidawa a yau; da tsaron mutunci da fa’idar kiwon lafiya saboda motsa jiki da kuma samun farin ciki, (saboda ganin yabanya da sauran alheran da Allah Ya ba mutum a gonarsa) da kuma tsira daga daukar wasu zunubai – irin su zage-zage ko gulma da sauransu (saboda ka kaurace wa jama’a ka fuskanci aikinka kawai); da kuma fa’idar samun lafiyar tunani.
Sai dai kada a manta, aikin noma yana bukatar kokari da kuma himmar gaske. Wani malami yana cewa (a wakensa da Larabci):
“Kokari yana kusanto da abu komai nisansa,
Kokari yana bude duk kofar da take rufe.”
(Daga littafenTa’alimul Muta’allim).
Tsira da Amincin Allah su tabbata ga Shugabanmu Annabi Muhammad (SAW) da jama’ar gidansa da sahabbansa bakidaya.
Huduba ta Biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin talikai. Tsira da Aminci su tabbataga Annabi mai karimci da jama’ar gidansa da sahabbansa baki daya.
Bayan haka, yaku bayin Allah! Lallai kasar nan tamu ta Najeriya tana daga cikin kasashen da Allah Ya ni’imta da fagagen noma masu yawan gaske. Masana sun ce daga cikin makeken filin kasar nan na hekta miliyan 98.3, (Magaji, 2016) hekta miliyan 83 duk sun kyautatu a nome su. Kimanin kashi 81 ke nan daga cikin 100. Amma yanzu haka kimanin hekta miliyan 30 zuwa 34 ne kawai ake gudanar da noma a kansu (kimanin kashi 28 kawai ke nan a cikin 100). (Aseogwu, 2017). Kuma Allah Ya ba mu yanayi da dausayi mai kyau na noma, ga kuma ruwan sama mai yawa (bayan na koguna, gulabe da koramu, ga kuma na karkashin kasa)! Shin don me ba za mu gode wa Allah ba a kan duk wadannan ni’imomi? Alhamdu lillahi Rabil alamin.
Ku tuna fa yaku ’yan uwa! Cewa a duniyar nan, akwai kasashen da ba a ba su irin ababen da aka ba mu ba na sinadaran noma (irin su kasar noma, kyakkyawan yanayi da wadatar ruwa), amma duk da haka suka nace a kan sha’anin noma ta hanyar dabarun fasahar noma da suka kirkiro (ko suka runguma), sai ga shisuna cin amfanin nacewarsu sosai. To, idan haka ne kuwa, me ya fi wannan kira da wannan gwamnati ta Shugaba Muhammadu Buhari take yi a yanzu na mu koma gona alheri?
Al-Allama Abdullahi Dan Fodiyo yana cewa a littafinsa KitabunNiyyat: “Ita (sana’ar noma) ita ce mafi karfin sana’o’i, saboda amfaninta ya wuce mutane ya kai ga tsuntsaye da dabbobi da kwari.
Don haka, abin da ya dace shi ne manomi ya gudanar da sana’arsa a kan binciken kimiyya da fasaha, tare da nasiha da kuma tsarkake niyya; a lokacin nan ne aikinsa zai yi albarka. Haka kuma, manomi ya gina aikinsa a kan tsoron Allah (wato kiyaye dokokinSa). Don haka, manomi ya yi kokari, ya binciki irin shukarsa, ya tabbata na halalinsa ne, haka nan kayan aikinsa (na hannu da na injin da sauransu), duk dai ya tabbata komai halalinsa ne, domin kada ya wahalar da kansa a banza ga abin da bai halatta gare shi ba; kuma domin aikinsa ya yi albarka…” (Ba iyakar zancen ke nanba).
Ya ku ’yan uwana! Kada ku manta da zancen Allah Madaukaki cewa: “Wanda (duk) ya zo da abu mai kyau, to, yana da mafi alheri daga gareshi, kuma wanda ya zo da mugun abu, to, ba za a saka wa wadanda suka aikata miyagun ayuka ba, face da abin da suka kasance suna aikatawa.” (Al-Kasas: 84). Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce: “Mafificin mutane shi ne wanda rayuwarsa ta tsawaita, kuma aikinsa ya yi kyau.” (Tirmizi ne ya ruwaito shi).
Ya Allah! Ka sanya mu cikin mafifitan mutane. Ya Allah! Ka ba mu abu mai kyau a duniya, kuma Ka ba mu abu mai kyau a Lahira, kuma Ka kare mu daga azabar wuta. Ya Allah! Ka ba mu lafiya da zama lafiya a kasarmu da dukkan kasashen Musulmi, amin. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga ShugabanmuAnnabi Muhammadu (SAW) da jama’ar gidansa da sahabbansa baki daya.
Wassalamu alaikum warahmatullah.
Injiniya Isma’il M. Cindo Gotomo (MNSE, MNIAE) ya gabatar da wannan huduba ce a ranar Juma’a 14 ga Shawwal, 1440 (14/08/2019) a Masallacin Juma’a na Haliru Abdu, Birnin Kebbi, za a iya samuna ta tarho mai lamba: 08181059714 da 08036049452