Muhimmancin amfani da man kade ga fata
Man kade (kadanya) yana da matukar amfani a fata domin yana dauke da sinadarai da dama har da sinadarin bitamin A da E. Wannan man na magance kurajen fuska da gautsin fata da kodewar fata da kuma kyasbi. Yawan amfani da wannan mai na sanya santsin fata. Ga kadan daga cikin amfanin man kade. […]
Man kade (kadanya) yana da matukar amfani a fata domin yana dauke da sinadarai da dama har da sinadarin bitamin A da E. Wannan man na magance kurajen fuska da gautsin fata da kodewar fata da kuma kyasbi. Yawan amfani da wannan mai na sanya santsin fata. Ga kadan daga cikin amfanin man kade.
• Hadin magance kyasbi
A samu man sandal da man ‘labender’ a zuba a cikin man kade sannan a kwaba shi sosai sannan a samu murta a zuba hadin. A mayar da wannan man shafawa a kullum. A yi amfani da shi na tsawon wata shida za a ga canji.
• Magance fata mai gautsi
A samu man kwakwa da man zaitun da man ‘almond’ sai a zuba a murta a kuma zuba man kaden a ciki sannan sai a kwaba da cokali ya kwabu sosai sannan sai a rika shafawa a jiki. A mayar da man, na shafawa bayan an yi wanka.
• Domin magance bushewar labba
A samu zuma da man zaitun sannan sai a zuba a kan man kade a kwaba su sosai. Sannan a sa a wuri mai sanyi. Sai a rika shafawa a baki a kullum za a samu sauki.
• Domin magance kurajen aski ga maza
A samu man ‘rosemary’ da man kwakwa sannan a zuba a kan man kade a kwaba. A rika shafawa a kullum bayan an aske gemu. Yana warkar da kurajen da ke fesowa a gemu bayan an yi aski.
• Domin kodewar fata
Kodewar fata na faruwa ne a duk lokacin da mutum ya kasance mai yawan shiga rana domin gudanar da wani aiki. Ko kuma a wuni a cikin rana. Hakan yana haifar da canjin launi ga fata inda sai a ga fata ta yi launi biyu; ga dishewa ga kuma kodewa. Idan aka kasance wajen shafa man kadanya kafin a shiga rana, yakan rage illar rana a fata.