Muhimmancin biya wa juna bukata a tsakanin ma’aurata (3)

Ita kuwa wata cewa ta yi, babban abin da ke damunta shi ne yadda aka hada ta aure da wani tsoho wanda ya girmi mahaifinta ma.  Ta ce abin bakin ciki shi ne wannan miji nata tsoho bai iya biya mata bukata a matsayinta na matashiya mai jini a jika.  Ta ce iyayenta ne suka […]

Muhimmancin biya wa juna bukata a tsakanin ma’aurata (3)

Ita kuwa wata cewa ta yi, babban abin da ke damunta shi ne yadda aka hada ta aure da wani tsoho wanda ya girmi mahaifinta ma.  Ta ce abin bakin ciki shi ne wannan miji nata tsoho bai iya biya mata bukata a matsayinta na matashiya mai jini a jika.  Ta ce iyayenta ne suka yi kuskuren hada ta aure da shi, amma saboda biyayyar da take musu ne ya sa ta amince amma a gaskiya hakan ya yi matukar cutar da ita.  Ta ce sukan shafe wata da watanni ba tare da ya kusance ta ba, kuma ko da ya kusance ta din ma, ba ya iya biya mata bukata yadda yakamata.  Ta ce ta ci gaba da rokon Allah a bisa mummunan halin da ta tsinci kanta a ciki, don ita mabukaciya ce kuma idan ta yi yunkurin fita waje don neman wasu mazan sai ta ji tsoron Allah ta fasa.  Ta ce yanzu maganar da ake Allah Ya karbi ran mijin nata kuma tana fata idan za ta yi wani sabon aure, bayan ta gama idda Allah Ya hada ta da mijin da zai biya mata bukata musamman a wajen kwanciyar aure.

Sai dai matsalolin da ake yawan samu daga wajen wadansu mazaje a wajen rashin biya wa mata bukata a rayuwar aure ba ya rasa nasaba ne da rashin lafiya da kuma tsufa.  Wasu mazan sukan fuskanci matsalolin rashin samun karfin kusantar iyalansu saboda rashin lafiya irin su ciwon suga ko ciwon basir da sauransu.  Likitoci sun tabbatar masu fuskantar irin wadannan ciwo suna samun raguwar sha’awa da kuma karfin mazakuta.  Amma duk da haka ya dace irin mazan da ke fama da irin wannan matsala su nemi magani, kuma su zauna da iyalansu su yi musu bayani dalla-dalla irin halin da suke ciki.  Na tabbatar idan suka tattauna da juna za a samu mafita insha Allah.  Amma ga mazan da ke neman matan banza (karuwai) a waje don matansu na gida ba sa biya musu bukata, wannan ba hujja ba ce.  Akwai hanyoyin da za su iya ladabtar da irin wadannan mata cikin sauki.  Alal misali, za su iya kai su kara wajen magabata don a ja musu kunne, ko kuma idan suna da hali su kara wani auren. Amma ba daidai ba ne maza su rika daukar irin wannan danyen hukunci na fita waje suna yin lalata da matan banza da sunan yi wa matansu na gida horo.

Sannan wasu mazan sukan auri irin matan da ba kuruciyarsu daya ba.  Duk mutumin da ya tsufa sannan ya auri yarinya kacal, tilas a samu matsala a wajen kwanciyar aure in ba sa’a aka yi ba, don zai kasance karfinsu ba daya ba ne. Ta yaya mutumin da yake da yawan shekaru zai hada kansa da yarinya matashiya mai jini a jika?  Kamar yadda karin maganar da Hausawa ke yi ne “kwarya ta bi kwarya”.  Ma’ana kowane abu ya dace a ajiye shi a muhallinsa. 

  A gaskiya irin haka ne ke kawo matsala a wajen rayuwar aure, tun da ita macen tana ji da kuruciya alhali mijin nata shekaru sun yi nisa.  Don haka a wajen kwanciyar aure sai ka tarar ta fi mijin nata bukata.  Don haka  ina kira ga maza masu yawan shekaru da su yi wa Allah su san irin matan da za su rika aura, musamman a bangaren shekaru, kada ka auri macen da ka san ka girme ta nesa ba kusa ba, wasu ma sun yi jika da ita, duk da dai ba haramun ba ne, amma za a iya samun matsala a wajen kwanciyar aure.

Haka kuma wata matsalar da wasu mazan ke janyo wa kansu ita ce ta yin aure da yawa alhali ba su da karfin da za su iya biya wa dukkan matan da suka aura bukata musamman a wajen kwanciyar aure.  Za ka iske akwai namijin da ba ya iya biya wa matarsa guda bukatar kwanciyar aure, amma sai ka tarar ya auri mata biyu ko uku ko ma hudu.  A nan wadansu sukan yi haka ne saboda yin gasa, watakila abokinsa ko wani na kusa da shi ya kara aure, ko kuma wanda yake ganin bai kai shi a matsayi ko samu ba, don haka sai ya ce tun da wane da bai kai ni karfi ta fuskar samu ya kara aure, me zai hana ni ma in kara.  Sai ka tarar ya kara, daga karshe a yi ta samun matsala a wajen matan saboda rashin wadatuwar kwanciyar aure daga wajen mijin nasu.  Hakan kuma babbar matsala ce. 

  A nan ina kira ga irin wadannan mazaje masu karambani su daina yin haka.  Su sani rayuwar aure ta fi karfin yin gasa. Su rika gudanar da harkokinsu daidai ruwa daidai kurji.  Wadansu sukan yi haka ne saboda gasa, watakila abokinsu yana da mata biyu ko uku ko hudu, su ma bari su kara,  wasu kuwa suna yi ne saboda sun samu wadata alhali wasu kuma na kara aure ne saboda matansu suna yawan bata musu rai, don haka bari su kara aure don su huce takaici.

Shi dai aure ibada ce, kuma sunna ce ta Annabi Muhammad (SAW) don haka bai kamata mu rika yin sakaci ko wasa da shi ba.

Shawara:

Yakamata a duk lokacin da ma’aurata suka yi aure, to su rika kyautata wa juna musamman a bangaren kwanciyar aure.  Kwanciyar aure ita ce jigo a rayuwar aure, kuma ana aure ne saboda samun karuwa, kuma babu yadda za a yi a samu karuwa ba tare da an yi ibadar aure ba.  Idan ma’aurata suka fahimci ba za su iya biya wa juna bukata a rayuwar aure ba, to mafi dacewa su yi rabuwar arziki don kada wani bangare ya cutar da wani.  Ina ganin idan aka bi wannan shawara ba za a rika samun irin matsalolin da ma’aurata suke fuskanta musamman a wannan zamani da muke ciki ba.

Allah Ya sa mu dace, amin.

 

Za a iya samun Ahmed Garba Mohammed a 08028797883