Muhimmancin bututun gas na Ajaokuta-Kano ga arzikin Najeriya
Bututan gas masu nisan kilomita 614 da aka kaddamar da aikin shimfidawa daga Ajaokuta zuwa Kaduna zuwa Kano (AKK) za su kawo ci gaba mai dorewa da bunkasar tattalin arziki ga Najeriya. Shugaba Muhammadu Buhari ne ya bayyana haka yayin kaddamar da aikin wanda zai lashe Dala biliyan biyu da miliyan 592 ranar Talatar makon […]
Bututan gas masu nisan kilomita 614 da aka kaddamar da aikin shimfidawa daga Ajaokuta zuwa Kaduna zuwa Kano (AKK) za su kawo ci gaba mai dorewa da bunkasar tattalin arziki ga Najeriya.
Shugaba Muhammadu Buhari ne ya bayyana haka yayin kaddamar da aikin wanda zai lashe Dala biliyan biyu da miliyan 592 ranar Talatar makon jiya.
“Wannan rana ta yau [wani] babi ne mai muhimmanci a tarihin wannan kasa tamu mai girma; rana ce da bututanmu na iskar gas da suka tashi daga Obiafu a Jihar Ribas, da Escravos a Jihar Delta, da Lekki a Jihar Legas, za a hade su da jihohin Kaduna da Kano, lamarin da zai kara bunkasa wadatuwar makamashi a kasa baki daya”, inji Shugaba Buhari.
- Buhari ya kaddamar da aikin bututun iskar gas a Arewa
- Kasuwanci: Darajar Najeriya ta daga duniya —Buhari
Shugaban kasar, wanda ya kaddamar da aikin ta intanet daga Fadar Shugaban Kasa a Abuja, ya kuma ce idan aka kammala aikin, bututan za su samar da iskar gas wadda za ta bayar da wutar lantarki ta kuma samar da makamashi ga masana’antu, sannan su taimaka wajen farfado da masana’antun da suka kwanta dama da kakkafa sababbi a garuruwan da bututan za su ratsa a jihohin Kogi, da Neja, da Kaduna, da ma Abuja, a Yankin Babban Birnin Tarayya.
Muhimmancin bututan ga tattalin arziki
Shugaba Buhari ya kara da cewa sarrafa dimbin albarkarun iskar gas da Najeriya ke da su don amfanin harkokin kasuwanci abu ne mai muhimmanci wajen habaka tattalin arzikin kasa cikin hanzari da kuma fadada hanyoyin samar da arziki.
A cewarsa, wannan wani muhimmin buri ne na gwamnatinsa ta fuskar samar da kyakkyawar, ingantacciyar, kuma yalwatacciyar makoma mai dorewa ga al’umma.
Ya kuma ce aikin zai samar da ayyukan yi da dama sannan ya yi tasiri wajen bunkasa kwarewa da basirar mutanen da ke zaune a wuraren da abin zai shafa sannan ya habaka masana’antun yankunan.
Shugaban kasar ya kuma yi kira ga gwamnonin jihohin Kogi da Neja da Kaduna da Kano da kuma ministan Yankin Babban Birnin Tarayya da su samar da kyakkyawan yanayin da ake bukata don gudanar da aikin, su kuma bayar da goyon baya.
Makasudin aikin
Shugaban Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC), Mallam Mele Kyari, ya ce suna aiki don tallafa wa yunkurin gwamnatin Shugaba Buhari na fadada hanyoyin samun kudin shiga a kasa.
Daya daga cikin hanyoyin da suke bi don tabbatar da hakan, inji shi, shi ne kara yawan hanyoyin rarraba iskar gas a cikin gida.
Ya kara bayani da cewa an bayar da kwangilar aikin shimfida kashi na farko na bututun mai nisan kilomita 303 ga gamayyar kamfanonin Oilserv da China First Highway Engineering Company, yayin da aka bayar da kwangilar gaba ta biyu mai nisan kilomita 311 ga gamayyar kamfanonin Brentex Petroleum Services da China Petroleum Pipeline Bureau.
Za a samar da kudin aikin ne ta hanyar wani tsari na rancen jari wanda Bankin China da kamfanin inshora na China, SINOSURE, za su samar, wanda kuma za a biya da kudin da za a samu na harajin da za a saka a kan sayar da gas ta bututan.
Mallam Kyari ya kara da cewa an cimma dukkan sharuddan da ake bukata don karbo rancen kuma kamfanonin da ke neman lamunin na ci gaba da bin matakan neman amincewar da ta dace don ganin kudin ya samu nan da watan Agusta.
Ya kuma ce yana da kwarin gwiwa cewa ’yan kwangilar za su iya kammala aikin a kan lokaci, daidai yadda aka zayyana kuma a bisa kasafin da aka yi.
Sannan ya ce idan aka kamala aikin, a kullum za a samar da iskar gas wadda yawanta ya kai gangar mai sama da miliyan 391, sannan a samar da megawat 3,600 na wutar lantarki.
Tasirin aikin
Gwamnonin jihohin Kogi da Kaduna ne dai suka kaddamar da aikin a madadin Shugaba muhammadu Buhari a wuraren da za a fara aikin a Ajaokuta, Jihar Kogi, da Rigachukun a Jihar Kaduna.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya ce gwamnatinsa ta dauki nauyin koya wa matasa da dama aikin walda, don haka ya bukaci kamfanonin da aka baiwa kwangilar su dauke su aiki.
A nashi bangaren, Gwamna Nasir el-Rufai na Jihar Kaduna cewa ya yi akwai kyakkyawan fata saboda dimbin alfanun da wannan aiki zai kawo wa jiharsa.
Aikin dai zai rage yawan iskar gas din da ake konawa a Neja Delta, lamarin da zai taimaka wajen samar da tsaftatacciyar iska a yankin mai albarkatun man fetur.
A cewar NNPC, bututan, wadanda aka kaddamar da aikin shimfida su da nufin samar da iskar gas ga arewacin Najeriya daga kudancinta, shi ne aikin raya kasa mafi girma a tarihin kasar na baya-bayan nan.
Abin da za a kashe
An dai kasa aikin kashi uku: kashe na farko, wanda ya kunshi shimfida bututai masu nisan kilomita 200 daga Ajaokuta zuwa Abuja, zai ci kudi Dala miliyan 855.
Kashi na biyu kuma mai nisan kilomita 193 daga Abuja zuwa Kaduna, an kiyasta zai lashe Dala miliyan 835.
Sai kuma kashi na uku mai nisan kilomita 221, wanda kuma zai tashi daga Kaduna zuwa Kano; shi kuma zai tashi a kan Dala biliyan daya da miliyan 200.
Daukacin aikin kuma bangare ne na gagarumin aikin shimfida bututan gas ta cikin Sahara wanda zai ba da damar fitar da iskar gas din zuwa Turai a cewar NNPC.
Sauyin da ake fatan samu
Da yake tsokaci game da aikin, mukaddashin darakta janar na Kungiyar Masu Masana’antu ta Najeriya (MAN), Ambrose Oruche, ya ce shimfida bututan gas din daga Ajaokuta zuwa Kaduna, in har aka kammala kamar yadda aka tsara, zai farfado da masana’antu da dama, musamman a arewacin Najeriya.
“Mun dade muna neman a yi irin wannan aiki a arewacin Najeriya saboda masana’antu da dama a yankin sun durkushe; ga shi kuma wutar lantarki ba isa take yi ba sam”, inji shi.
‘Kada a yi kitso da kwarkwata’
Najeriya ce dai kasa ta bakwai a duniya a yawan iskar gas. Sai dai shekara da shekaru ta fi mayar da hankali a kan man fetur, duk da cewa gas ya fi samar da kudin shiga, ko da yake ya fi wahalar sarrafawa.
Tuni dai masu fafutukar kare muhalli suka yi kira ga ’yan kwangilar, da ma gwamnati, da su yi taka-tsantsan wajen gudanar da aikin don kada a gurbata muhalli.
Da take tattaunawa da Aminiya a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa, jagorar kungiyar Global Care Rescue Mission, Gimbiya Elizabeth Egbe, wadda ta yi wannan kiran, ta kuma gargadi gwamnati da ta tabbatar aikin bai cutar da rayuwar mutanen yankunan da bututan za su bi ba.