Muhimmancin gane kayan kwalliya
Mata da dama sukan so su ga sun yi kwalliyar da za ta janyo hankalin jama’a kuma suna son su ga sun fi kowa kyau a cikin taro. To, ta yaya hakan zai faru? Hakan zai iya faruwa ne idan an san abubuwa 4 game da kwalliyar zamani wadanda idan aka yi amfani da su, […]
Mata da dama sukan so su ga sun yi kwalliyar da za ta janyo hankalin jama’a kuma suna son su ga sun fi kowa kyau a cikin taro. To, ta yaya hakan zai faru? Hakan zai iya faruwa ne idan an san abubuwa 4 game da kwalliyar zamani wadanda idan aka yi amfani da su, za a ga kyau ya karu.
Sanin launin da ya dace da ido da baki
Babban kuskuren da ake yi idan aka zo shafa kayan kwalliya shi ne, ana shafa launi iri daya a baki da fatar ido. Idan aka yi haka, sai a ga kwalliyar ta yi kama da ta kauyawa. Yadda ya fi dacewa shi ne, a shafa launi daban-daban a fatar ido (eye shadow) sannan a shafa wani launi daban a baki. Misali, idan kayan da aka sanya kore ne, sai a shafa kore a fatar ido sannan a shafa ja a baki. Idan kore ya kasance shi ne a kan ido da baki kwalliyar ba za ta yi armashi ba.
Boye tabo da sanin launin fatarki
Sanin launin da ya dace da fatarki ya fi muhimmanci fiye da komai a kayan kwalliya. Sirrin shi ne, bayan an gama kwalliya za a yi kokarin boye kwalliyar kamar ba a shafa komai a fuskar ba. Idan ana da fuska mai tabo, sai a shafa ‘fondishan’ kafin shafa hoda kuma a tabbata cewa launin hodar fandesho ta yi daidai da launin fata.
Abubuwan da bai kamata a manta ba kafin daukar hoto
A tabbatar cewa an sanya jambaki da hoda domin boye maikon fuska. Kamar kan hanci da goshi da kumatu kafin a dauki hoto. Idan aka yi haka, lallai za a ga an fito daban a hoton.
Abubuwan da za a sanya a jakar kwalliya
Kada a kuskura a bar gida ba tare da an sanya abin goge gumi da jambaki da hoda da turaren jiki da na baki a cikin jaka ba. Kuma kada a manta idan an shiga wajen taro a zama cikin fara’a kada a rika yamutse fuska. Domin murmushi na kara fitar da kyan mace.