Muhimmancin kishin kasa ga rayuwar al’umma (2)

Gare ku masu bibiyar filin Sinada-rin Rayuwa, Assalamu alaikum. Bayan haka, kamar yadda muka faro wannan sabon maudu’in a makon jiya, yau kuma za mu ci gaba daga inda muka tsaya; wato inda muke yin bayani game da illar da ke tattare da kabilanci.Idan mun duba da idon basira, duk wani addinin da ya amsa […]

Muhimmancin kishin kasa ga rayuwar al’umma (2)
Muhimmancin kishin kasa ga rayuwar al’umma (2)

Gare ku masu bibiyar filin Sinada-rin Rayuwa, Assalamu alaikum. Bayan haka, kamar yadda muka faro wannan sabon maudu’in a makon jiya, yau kuma za mu ci gaba daga inda muka tsaya; wato inda muke yin bayani game da illar da ke tattare da kabilanci.
Idan mun duba da idon basira, duk wani addinin da ya amsa sunansa, ba ya son al’umma su nuna wariyar kabilanci. Babban burin kowane addinin kwarai shi ne, al’umma su kasance tsintsiya daya, ta yadda za su amfani juna wajen zamantakewa da mu’amala. Hasali ma, Allah (SAW) Ya shaida mana cewa Ya halicci al’umma ne zuwa kabilu da jinsuna daban-daban, ba don komai ba sai domin su fahimci junansu. Wannan yana nuna mana cewa, maimakon mu rika nuna kyama da wariya ga kabilun da ba namu ba, kamata ya yi mu fahimci juna, ta yadda za mu amfani juna kuma mu ci gajiyar juna.
Wannan ne ma ya sanya na tuno da wani kalami da wani jigon al’umma, mai kishin kasa da al’ummarsa ya taba furtawa. Ina maganar Gamji dan kwarai ne, wato marigayi Sardaunan Sakkwato, Alhaji Sa Ahmadu Bello. Kamar yadda aka ruwaito, an ce marigayi Dokta Nnamdi Azikiwe ne ya taba ce masa su mance da bambance-bambancensu… Shi kuwa Gamji sai ya ce masa ba haka za su yi ba, madamar suna son fahimtar juna.
Kamar yadda aka ruwaito, Sardauna ya ce wa Zik su zo su gane bambance-bambancensu sai su fahimci juna, su yi aiki tare alhali suna masu kiyaye hakkokin juna. Ya ce Zik Inyamuri ne, shi kuwa Bahaushe. Zik mutumin Kudu ne, shi kuwa dan Arewa. Zik Kirista ne, shi kuwa Musulmi. Ta haka za su hada hannu su yi wa kasa hidima.
Kuma wannan al’amari, ta kowane janibi muka duba shi, za mu gane tasirinsa, kasancewar kowa na bukatar kowa. A yayin da Allah Ya hore wa wannan kabila wannan baiwa, Ya kuma hore wa waccan wata baiwar ta daban. Sai a hadu tare, kowa ya baza kolin tasa baiwar domin amfanin juna. Wannan shi ne kishin kasa kuma da na al’umma.
Idan muka dauki mummunan halin nan na bangaranci kuwa, shi ma muninsa daya da kabilanci. Madamar muna son mu kasance ’yan kishin kasa, masu son ganin al’umma ta samu ci gaba, dole ne mu rungumi juna, ba tare da la’akari da bangaren da junanmu suka fito ba. Babban abin da a har kullum ya kamata mu rika kallo shi ne, kasa daya ke gare mu, wacce ita ce mallakinmu. Ba mu da wata kasa da za mu iya kira tamu face ita. Ke nan da zarar Kudu ta bunkasa, to Najeriya ce ta bunkasa, haka ma Arewa.
Kamar yadda kowace kabila ke buka-tar wata kabila, haka ma bangarorin kasar nan ke bukatar juna. A yau idan muka duba, za mu ga yadda ’yan bangarori daban-daban suka bar yankunansu, suka tafi wani yanki daban, suna rayu-wa. A Legas ko Ibadan ko Ekiti, za ka ga Hausawa da Fulani suna gudanar da rayuwarsu, kamar yadda a Katsina da Kano Da Sakkwato za ka ga Yarabawa suna gudanar da nasu al’amuran.
A Borno da Bauchi da Yobe, za ka ga Inyamurai suna sha’aninsu na yau da kullum, kamar yadda za ka ga sauran kabilun Arewa a Fatakwal da Benin da sauran yankunan Kudu. Wanna ya nuna cewa lallai kasa daya muke, kuma duk muna bukatar juna. Ke nan sai mu taru mu aiwatar da abin da ya dace, wanda zai ciyar da kasar gaba, ba tare da wariyar bangaranci ba.
Haka kuma, Allah Ya yi wata hikima, inda Ya warwatsa rahamarSa a dukkan sassan kasar nan, ta yadda ya zama wajibi mu yi zaman tare a matsayinmu na ’yan kasa daya, madamar dai muna son cin gajiyar arzikin juna. A yayin da Allah Ya zuba  dukiyar abinci da nama da fadin kasa falala a yankin Arewa, sai kuma Ya malala arzikin makamashin mai da iskar gas a Kudancin kasar nan. A lokacin da ’yan Kudanci ke bukatar abinci da nama da sauran kininsu, mu kuma nan bangaren muna bukatar makamashi. Dalili ke nan ma ya zama wajibi mu hada hannu, mu nuna kishin kasa da kishin juna wajen cudanya da juna cikin fa’ida; ta yadda za mu bunkasa kasarmu. Wannan shi ne kishin kasa.
Babu yadda za mu ce mu samu ci gaba, madamar muna kyarar juna, muna yakar juna. Idan har za mu waiwayi tarihi, ai iyayenmu sun taba jaraba yakin juna, inda aka fafata Yakin Basasa. Babu wani bangare da ya ci ribar wannan yaki, alhali kasar gaba daya ta yi asara. A wannan yaki, an yi asarar rayuka da dukiya mai yawa. Akan dole kuma aka dawo aka zauna a matsayin kasa daya. Ke nan, babu abin da ya dace da mu illa mu fitar da bangaranci daga zukatanmu, mu fuskanci kasa gaba daya, ta yadda za mu samu ci gaban da ya dace da mu.
Za mu ci gaba

Dausayin kauna

Tsakanin masoya: Dalilan da suke kara mana kaunar juna (3)

Yau dai mun shiga mako na uku a cikin wannan maudu’i, kuma za mu fara da sako Aminu Fifa Jega 08185895200: “FDk, ka mika min gaisuwata da jinjinar girma ga malamata, abin alfaharina Hajiya Maryam. Ita ce mace daya tankar dubu. Hakikanin gaskiya da matan yanzu za su yi koyi da hali irin na Maryam da za su ji dadin zama da masoyansu; domin Allah Ya hore mata wasu kyawawan haleyan da kowane namiji ke marmarin Allah Ya ba shi mace irinta. Kadan daga cikin halayenta su ne: Mace ce mai son addini, mai son tsafta kuma mai son faran ta wa masoyinta.”
Fifa, Allah sa masoyiyar taka tana jin ka, Allah Ya ida nufi, amin. – FDk.
Shi kuma mai lamba 08031952823, yana cewa: “Ni dai wallahi na yi sa’a, domin budurwata tana so na sosai, ba ta kula kowa, ba ta saurarar kowa in ba ni ba. Ni dai gaskiya na yi sa’ar matar da zan aura. Ina rokon ’yan uwana samari su taya ni da addu’a, Allah Ya ba ni ita. Ni ma ina yi wa ’yan uwana samari addu’a; Allah Ya ba su mai son su, kamar yadda tawa take so na tsakaninta da Allah.”
To, Malam, da kai da sauran masu aiko da sakonni, daga yau a rika sanya suna da lamba a cikin sakon. – FDk.
Sako daga Bintu Madu Nguru 08061568460, yana cewa: “Assalamu alaikum. Da farko dai zan fara da gaisuwa ga FDk da kuma lale da dawowar Dausayin kauna. Ni dai ina kaunar saurayina saboda abubuwa kamar haka: Kamili ne, yana girmama iyayena, yana da ilimin boko da na Islama. Kadan daga cikin abubuwan da suka sa nake son saurayina ke nan kuma mijina in sha Allah.”
Mannir M. Yabo Sakkwato, 08034457383, ya ce: “Salam, FDK, Barka da warhaka. Ina so da kaunar masoyiyata Bilkisu saboda iliminta, hankali, girmama na gaba, hangen nesa; ga iya kalaman kauna. Allah Ya nuna muna ranar aurenmu.”
Ita kuwa Rukayya Ibrahim (Maman Hajiya), ta ce: “Ina kaunar maigidana saboda kyawawan dabi’unsa, ga shi da rikon addini, ga iya kula da iyali. Duk wanda ya yi mu’amula da shi sai ya yaba kyawun halinsa.”
Sai kuma sakon dahiru Dauda (KGY) Bindawa, 08055552897, mai cewa: “Sallama a gare ka FDk, bayan kewarka ta tsawon lokaci. Muna yi maka barka da dawowa tare da fatan alheri. Babu shakka a kullum so da kaunar Maman Khadija karuwa suke a cikin zuciyata, a sabili da fahimtar irin so da kaunar da take nuna mini ba tare da gajiyawa ba. Bugu da kari, tana matukar tausaya mini a kan duk abin da ya bijiro min, musamman idan ta fahimci ina da damuwa a kansa.”
Daga Shehu Ibrahim Gusau 08051526272: “Salam FDk, ina matukar kaunar Nana Asiya saboda tana da ilimin addini ga hakuri ga sanin ya kamata.”
Daga Isah Muhammad Rabah 07034218311: “Salam, FDk, dalilin da ya sa nake son matata shi ne, saboda tana da hakuri da kauna da kuma iya soyayya.”
Shi kuma Babawo Chelsea Kofaran, Bauchi 08053955043, ya ce: “Assalamu alaikum FDk, abubuwan da suka sa nake kaunar budurwata su ne: Gidansu akwai dattaku kuma ita tana da ilimin addini da na zamani.”
Inji Lawal A. Khalid Gwagwalada-Abuja 08163274360, yana cewa: “Ina kaunar masoyiyata A’isha Khalid saboda halayenta kamar haka: A’isha mace ce mai alkunya da girmama na gaba da sanin matsayin kowa a wajenta. Ba ta da girman kai ko rashin da’a ko kuma nuna rashin kunya ga kowa. Tana matukar son jin tarihin magabata, wadanda suka yi wa mazansu da’a.”
dan mutanen Akwanga Jihar Nasarawa, S.M.I akwanga, 07039397069, shi kuma yana cewa: “Ina kaunar budurwata saboda hankalinta, natsuwarta, addininta da kuma sanin ya kamata. (Kash, sai dai Hausawa sun ce kaddara ta riga fata, na kasa gaya mata). Yaya zan yi ’yan uwana na Dausayin kauna?”
Lallai wannan shi ake kira harara a duhu. To kai dan Akwanga, idan ba ka shaida mata soyayyarka ba, yaushe za ta sani? Yi maza ka isar da sakonka ko kai tsaye ko kuma ta hanyar abokanka, ko kuwa a bar ka a baya! – FDk.
Ita kuwa Rabi’atu (Rabpretty), Jihar Nasarawa 08065398843, cewa take: “Salam FDk, ina muku maraba da dawowa amma mun ji dadi sosai da dawowarku; Allah bar mu tare. Ina kuma gaishe da masoyan FDk maza da mata.”
Shi kuwa mai lambar nan, 07019540766 saba wa maudu’inmu ya yi, inda ya bijiro da wannan kalubalen: “Assalam FDk, shin ya kamata mummunan hasashe ya shigo dausayin soyayya? Dalilina na wannan tambayar shi ne, ina buri in yi auren dangi amma hasashen cewa idan sabani ya shigo, zumunci na iya rushewa ya yi tasiri a zuciyata! Ya zanyi ne ’yan uwa?”
Ita kuwa Fatima Ashiru 08095482722 cewa ta yi: “Barka da dawowa FDk. Muna matukar farin ciki.”
A yayin da wasu ke yabawa da masoyansu, shi kuwa Suleiman Muhammed Adam Falgoren Daji, Jihar Kano, 08093437476, kokawa ya yi da tasa masoyiyar. Ga abin da yake cewa: “Ni kam na yanke shawarar rabuwa da wacce nake kauna sakamakon ko in kula da take nuna min. Hausawa sun ce son maso wani asara. Ni kam tsakanina da Allah nake kaunarta amma ita ko damuwa da ni ma ba ta yi ba. Don Allah mece ce shawararku ’yan uwana?”
Shi kuma Sanusi Nalandon Gusau, 08067791410, cewa yake: “Dalilin da ya sa nake matukar kaunar matata Fatima Bala, saboda mai ilmi ce, mai da’a da ladabi da biyayya, ga natsuwa.”
Madallah da masoyan FDk, maza da mata, sai kuma makon gobe idan Allah Ya kai mu. Ga duk mai son aiko da sako, a tabbatar an sanya suna, sunan gari, jiha da kuma lambar waya, amma matan aure su nuna, idan ba su son a sanya lambar wayarsu. Wassalam. FDk!