Muhimmancin kishin kasa ga rayuwar al’umma (3)

Ya ku masu bibiyar Sinadarin Rayuwa, yau ma dai ga sallamar nan dai da muka saba, Assalamu alaikum.Kamar yadda muka faro tambihi a makonni biyu da suka gabata game da wannan maudu’i na kishin kasa, yau ma za mu dora daga inda muka tsaya a makon jiya.Wata mummunar dabi’a da ke yi wa kishin kasa […]

Muhimmancin kishin kasa ga rayuwar al’umma (3)
Muhimmancin kishin kasa ga rayuwar al’umma (3)

Ya ku masu bibiyar Sinadarin Rayuwa, yau ma dai ga sallamar nan dai da muka saba, Assalamu alaikum.
Kamar yadda muka faro tambihi a makonni biyu da suka gabata game da wannan maudu’i na kishin kasa, yau ma za mu dora daga inda muka tsaya a makon jiya.
Wata mummunar dabi’a da ke yi wa kishin kasa karan tsaye kuma take janyo wa kasa koma baya, ita ce dabi’ar nuna wariyar addini. Babu shakka wannan dabi’a tana taka rawa wajen haddasa hairani da rashin hadin kai a Najeriya. Lallai ne ’yan kasa su tashi tsaye wajen cijewa da daurewa wajen zama da juna tare da daratta addinan juna, ba tare da nuna yatsa ga wadanda ba addinanmu daya da su ba.
Kamar yadda za mu lura, Allah cikin ikonSa da hikimarSa, Ya halitta kuma Ya kadarta mutane masu mabambantan akida da addini su rayu a cikin kasa daya. Idan kowane mai addini ya cije wuri guda ya ce dole sai ra’ayin addinisa za a bi domin a tafi tare, lallai kam haka faufau ba za ta yiwu ba. Idan haka ne, kuma haka din ne ma, to ina dubara, ina mafita? Akwai ta, kuma guda daya ce. Abin yi shi ne, a matsayinmu na ’yan kasa daya, kowa ya rike martabar addininsa, ya bi darussan da ke shimfide cikin addininsa sau da kafa, ba tare da ya kawo wa dan uwansa mabiyin wani addini cikas ba. Idan aka yi haka, shi ke nan, an huta da kace-nace. Kai mabiyin addinin Kirista, sai ka ci gaba da bin kiristancinka, kai ma mabiyin Musulunci, sai ka ci gaba da bin musuluncinka. Hatta ma wadanda ke bin addinin gargajiya, tun da dai su ma ’yan kasa ne, sai su ci gaba da bin nasu addinin. Shi ke nan, husuma ta kare, babu hairani.
Wani abin da ya kamata mu fahimta shi ne, duk wani addini, madamar na kirki ne, to manufarsa ita ce samar da tsira da ci gaban dan Adam. Babu wani addini da ya amsa sunansa da ya amince da ka uzura wa wani ko ka yi wa wani ta’addanci. Duk wani addini na mutunci, burinsa shi ne ya jagoranci dan Adam zuwa ga aikata kyawawan ayyuka kuma ya hana shi aikata munana. Don haka, kishin kasa ne ga dan kasa ya jure wa zaman tare tsakaninsa da abokin zamansa, koda kuwa addininsu ya bambanta.
Yana kuma daga kishin kasa ga mutum ya kasance mai tafiyar da al’amuransa cikin gaskiya da amana, wato ya guje wa ha’inci. A yayin da rikon amana da gaskiya suka kasance jigogin kishin kasa, shi kuwa ha’inci ya kasance makamin ruguza kasa. Sai mu kama dabi’un kirki, mu watsar da na banza, madamar dai muna son mu ga muna samun ci gaba da bunkasa.
Yaudara, halayya ce mai saukin aikatawa, amma illar da ke tattare da ita tana da yawa. Ba kishin kasa ba ne ga dan kasa ya kasance cikin halayyar yaudara, domin kuwa babu abin da take haifarwa sai koma-baya ga al’umma da kasa baki daya. Ke nan, ya zama wajibi mu guji yaudara, tun da dai na tabbata babu mai son ya ga cewa wani ya yaudare shi. To, dan uwa, abin da ka san cewa ba ka son a yi maka, yaushe kuma kai za ka yi wa wani? Babu hikima cikin wannan ko kadan.
Wadannan dabi’u: Shashanci, tambele, hassada, gaba, gilli da ayarinsu, dabi’u ne da tuni suka kauce wa hanyar kwarai kuma duk wanda ya siffatu da aikata su, bai kasance dan kishin kasa ba. Lallai ne mu kaurace musu, domin mu kasance ’yan kasa nagari masu kishin kasa da kishin al’umma.
Wajibi ne a gare mu mu kasance masu bin dokokin kasa, kamar yadda aka shimfida su. Ta hanyar bin dokokin ne za mu samu tafiyar da al’amuranmu cikin tsari da inganci. Idan kuwa muka kasance muna zama cikin karya doka, muka zauna zaman-kara-zube, babu babba babu yaro, to rayuwarmu ba za ta sha bamban da ta dabbobi ba. Idan haka ta faru, shi ke nan mutuwar kasa ta zo, wanda kuma ba haka aka so ba, wai kanen miji ya fi miji kyau.
A yayin da muke rufe wannan maudu’i, zan yi kira ga al’umma, manyanmu da kanananmu, mazanmu da matanmu da cewa lallai ne mu tashi tsaye mu ceto kasarmu, mu kasance masu kishinta nakwarai, masu son ta da kishin ci gabanta. Kada mu bari ta fadi ko ta ruguje, domin kuwa ba mu da wata kasa kamar ta.
Wassalam. Sai kuma mun hadu a mako na gaba.