Muhimmancin kishin kasa ga rayuwar al’umma (4)

Kishin kasa ne ga mutum ya kasance mai kaunar jama’a, ba tare da nuna wariyar kabilanci, bangaranci ko addinanci ba. Kada ka ce za ka yi mu’amala ne kawai da ’yan kabilarka ko kuma ka ce ’yan kabilarka ne kadai mutanen kirki, don haka babu ruwanka da wasu. Idan ka yi haka, babu shakka ba […]

Muhimmancin kishin kasa ga rayuwar al’umma (4)
Muhimmancin kishin kasa ga rayuwar al’umma (4)

Kishin kasa ne ga mutum ya kasance mai kaunar jama’a, ba tare da nuna wariyar kabilanci, bangaranci ko addinanci ba. Kada ka ce za ka yi mu’amala ne kawai da ’yan kabilarka ko kuma ka ce ’yan kabilarka ne kadai mutanen kirki, don haka babu ruwanka da wasu. Idan ka yi haka, babu shakka ba ka nema wa kasarka alheri ba kuma ba ka zama mai kishinta ba. A lokacin da ka dauki ’yan kabilarka kawai a matsayin mutane, ka banzatar da sauran jama’a, kawai domin su ba naka ba ne, to lallai akwai matsala. Na farko dai, kai kanka za ka gamu da matsala, domin kuwa al’ummar kasarka sun kasance kabilu daban-daban, masu yaruka daban-daban, masu al’adu daban-daban, kuma ya zama wajibi su yi rayuwa tare da wasu kabilun, tunda duk ’yan Najeriya ne. Wata rana, dole ne za ka nemi wata bukata, wacce dan kabilarka ba zai biya maka ita ba. Idan haka ta kasance, to yaya za ka yi, tun da ba ka dauke su a bakin komai ba?
Idan mun duba da idon basira, duk wani addinin da ya amsa sunansa, ba ya son al’umma su nuna wariyar kabilanci. Babban burin kowane addinin kwarai shi ne, al’umma su kasance tsintsiya daya, ta yadda za su amfani juna wajen zamantakewa da mu’amala. Hasali ma, Allah (SAW) Ya shaida mana cewa Ya halicci al’umma ne zuwa kabilu da jinsuna daban-daban, ba don komai ba sai domin su fahimci junansu. Wannan yana nuna mana cewa, maimakon mu rika nuna kyama da wariya ga kabilun da ba namu ba, kamata ya yi mu fahimci juna, ta yadda za mu amfani juna kuma mu ci gajiyar juna.
Wannan ne ma ya sanya na tuno da wani kalami da wani jigon al’umma, mai kishin kasa da al’ummarsa ya taba furtawa. Ina maganar Gamji dan kwarai ne, wato marigayi Sardaunan Sakkwato, Alhaji Sa Ahmadu Bello. Kamar yadda aka ruwaito, an ce marigayi Dokta Nnamdi Azikiwe ne ya taba ce masa su mance da bambance-bambancensu… Shi kuwa Gamji sai ya ce masa ba haka za su yi ba, madamar suna son fahimtar juna.
Kamar yadda aka ruwaito, Sardauna ya ce wa Zik su zo su gane bambance-bambancensu sai su fahimci juna, su yi aiki tare alhali suna masu kiyaye hakkokin juna. Ya ce Zik Inyamuri ne, shi kuwa Bahaushe. Zik mutumin Kudu ne, shi kuwa dan Arewa. Zik Kirista ne, shi kuwa Musulmi. Ta haka za su hada hannu su yi wa kasa hidima.
Kuma wannan al’amari, ta kowane janibi muka duba shi, za mu gane tasirinsa, kasancewar kowa na bukatar kowa. A yayin da Allah Ya hore wa wannan kabila wannan baiwa, Ya kuma hore wa waccan wata baiwar ta daban. Sai a hadu tare, kowa ya baza kolin tasa baiwar domin amfanin juna. Wannan shi ne kishin kasa kuma da na al’umma.
Idan muka dauki mummunan halin nan na bangaranci kuwa, shi ma muninsa daya da kabilanci. Madamar muna son mu kasance ’yan kishin kasa, masu son ganin al’umma ta samu ci gaba, dole ne mu rungumi juna, ba tare da la’akari da bangaren da junanmu suka fito ba. Babban abin da a har kullum ya kamata mu rika kallo shi ne, kasa daya ke gare mu, wacce ita ce mallakinmu. Ba mu da wata kasa da za mu iya kira tamu face ita. Ke nan da zarar Kudu ta bunkasa, to Najeriya ce ta bunkasa, haka ma Arewa.
Kamar yadda kowace kabila ke bukatar wata kabila, haka ma bangarorin kasar nan ke bukatar juna. A yau idan muka duba, za mu ga yadda ’yan bangarori daban-daban suka bar yankunansu, suka tafi wani yanki daban, suna rayuwa. A Legas ko Ibadan ko Ekiti, za ka ga Hausawa da Fulani suna gudanar da rayuwarsu, kamar yadda a Katsina da Kano Da Sakkwato za ka ga Yarabawa suna gudanar da nasu al’amuran.
A Borno da Bauchi da Yobe, za ka ga Inyamurai suna sha’aninsu na yau da kullum, kamar yadda za ka ga sauran kabilun Arewa a Fatakwal da Benin da sauran yankunan Kudu. Wanna ya nuna cewa lallai kasa daya muke, kuma duk muna bukatar juna. Ke nan sai mu taru mu aiwatar da abin da ya dace, wanda zai ciyar da kasar gaba, ba tare da wariyar bangaranci ba.
Haka kuma, Allah Ya yi wata hikima, inda Ya warwatsa rahamarSa a dukkan sassan kasar nan, ta yadda ya zama wajibi mu yi zaman tare a matsayinmu na ’yan kasa daya, madamar dai muna son cin gajiyar arzikin juna. A yayin da Allah Ya zuba dukiyar abinci da nama da fadin kasa falala a yankin Arewa, sai kuma Ya malala arzikin makamashin mai da iskar gas a Kudancin kasar nan. A lokacin da ’yan Kudanci ke bukatar abinci da nama da sauran kininsu, mu kuma nan bangaren muna bukatar makamashi. Dalili ke nan ma ya zama wajibi mu hada hannu, mu nuna kishin kasa da kishin juna wajen cudanya da juna cikin fa’ida; ta yadda za mu bunkasa kasarmu. Wannan shi ne kishin kasa.
Za mu ci gaba

Dausayin kauna

Takaddamar Soyayya: Tsakanin Maza Da Mata, Wa Ya Fi Rikon Alkawarin Soyayya? (4)

Har yanzu dai muna cikin maudu’in da ake ragargaza takaddama tsakanin maza da mata, domin gano wadanda suka fi rikon amanar soyayya. A wannan makon ma ga sakonnin da muka samu, sai mu cala:
Za mu bude ne da batun Fatima Abdullahi ’yar Lajawa (08112538490) da take cewa: “Haba ’yan samari, ko kadan ban yi zaton akwai wanda zai furta koda harafi daya daga cikinku, idan ana batun alkawari bare kuma wa ya fi rike alkawari ba. Da yawa daga cikinku kuna fita daga filin daga nan kuna komawa gefe kuna maganar wai daga yarinya ta ga mai kudi sai ta juya baya, wanda kuma hakan shaci-fadi ne da kokarin nade tabarmar kunya. Ba zan ce gaba daya ba, domin a ko’ina akan samu nagari da kuma gurbatattu. Ban jin zan yi kaffara idan na rantse kan cewa kaso 99.5 na maza ba su da rike alkawari. Za ku yarda da ni, idan kuka duba yadda maza suke rige-rige wajen cin amanar matansu. Wannan jarida Aminiya ta isa ta zama hujja da labarukan da take bayarwa na irin cin amanarku a gare mu.”
Shi kuma Mukhtar (07066434519), ya biyo bayan ’yar Lajawa da nasa batun, mai cewa: “Ko shakka babu duk sa’adda aka ambaci amana ko kamun kai, duka dabi’u ne da a cikin maza da mata ana samun masu su da wadanda suka rasa hakan. Sai dai ni a nan na tsaya tsakiya, wato a duk sa’adda aka ce mace wurin juriya da rike alkawari, to da dama sun cancanci a yaba su, domin kamar ra’ayin Mista Tsari, wanda ya fi kawo illolin maza da dama, haka yake. Haka nan ra’ayin Malam Ibrahim Hamisu Kano, shi kuma ya karkata ga bai wa maza shaidar rikon alkawari amma duka dai yau duk yadda ka dau mace kana yi mata hidimomi a matsayin matarka ta aure, koda a ce kana da iko kuma ka biya mata kudin kujera zuwa aikin Hajji, ta je ta sauko farali; to in da matsala da ita a tsakaninku za ta kaure, shi ne batun karo aure? Wato kana cewa ka yi niyyar auro abokiyar zama, to sai sa’a ta tuna alheranka na baya, bayan kuwa shi karin aure ai ibada ce, amma ita sam-sam, ita dai daga kai sai ita.
Ashe cewa wai maza na cin amana, ai da dama su ma tun a cikin neman auren maimakon duba kima da cancantar mai nema, a’a su dai inda za a ja kaya, duk da cewa inda za a ja kayan ba laifi inda hali mai kyau amma sau nawa ne mace ke zuwa gidan da ake kallo komai ya ji a ishe an yi wa rogo hangen kitse. Ai rikon amana da juriya dabi’a ce, a iya samu ga maza haka a iya samu ga mata, duka dai a yi wa juna adalci shi ne ya fi.”
Sai kuma ra’ayin Nabeela Pretty Kazaure (09035685131), tana cewa: “A gaskiya mata sun fi maza rike alkawari. Mace na iya zama da mijinta cikin halin talauci da rashin lafiya komai wuya amma da namiji ne sai ka ga ya kai ta gidan iyayenta, ya ce ta yi jinya a can. Za ka ga budurwa da saurayi na soyayya amma da ya hango wadda ta sha bilicin, ta yi fari sai ka ga ya fara zamewa ya koma wajen waccan. Sau tari ana samun mazan da suke soyayya kawai ta karya, wani sai ka same shi da budurwa ta kai hamsin amma a mata ba za a taba samu ba.”
Shi kuwa Basiru Suru Tudun Jukum Zariya (07067216922), a nasa batun, yana cewa: “A kan rike alkawari saboda in dai ka ga mace ta rike maka alkawari, ba ta guje ka ba, to ba shakka kana da wadata ne ko kuma kana yi mata duk wata hidimar da ta kawo maka. Duk da haka ko kana yi mata, da zarar ta hangi wani wanda ya fi ka hali ya zo, sai ta juya maka baya. Rike alkawari sai maza amma da akwai irinsu Hauwa, wadanda samun su zai yi wahala yanzu.”
Za mu karkare da sakon Abubakar A. Malanjo Gombe (07067758596), wanda ke cewa: “A gaskiya mata sun fi maza rike alkawari saboda idan kana nema da mace har ta ce ‘ina kaunarka’ to da gaske take yi. Sabanin mu maza, namu a baki yake, don namiji fa sai a hankali.”
Masoya, mu hadu a mako na gaba in Allah Ya kai mu! – FDk.