Muhimmancin kishin kasa ga rayuwar al’umma (5)

Babu yadda za mu ce mu samu ci gaba, madamar muna kyarar juna, muna yakar juna. Idan har za mu waiwayi tarihi, ai iyayenmu sun taba jaraba yakin juna, inda aka fafata Yakin Basasa. Babu wani bangare da ya ci ribar wannan yaki, alhali kasar gaba daya ta yi asara. A wannan yaki, an yi […]

Muhimmancin kishin kasa ga rayuwar al’umma (5)
Muhimmancin kishin kasa ga rayuwar al’umma (5)

Babu yadda za mu ce mu samu ci gaba, madamar muna kyarar juna, muna yakar juna. Idan har za mu waiwayi tarihi, ai iyayenmu sun taba jaraba yakin juna, inda aka fafata Yakin Basasa. Babu wani bangare da ya ci ribar wannan yaki, alhali kasar gaba daya ta yi asara. A wannan yaki, an yi asarar rayuka da dukiya mai yawa. Akan dole kuma aka dawo aka zauna a matsayin kasa daya. Ke nan, babu abin da ya dace da mu illa mu fitar da bangaranci daga zukatanmu, mu fuskanci kasa gaba daya, ta yadda za mu samu ci gaban da ya dace da mu.
Wata mummunar dabi’a da ke yi wa kishin kasa karan tsaye kuma take janyo wa kasa koma baya, ita ce dabi’ar nuna wariyar addini. Babu shakka wannan dabi’a tana taka rawa wajen haddasa hairani da rashin hadin kai a Najeriya. Lallai ne ’yan kasa su tashi tsaye wajen cijewa da daurewa wajen zama da juna tare da daratta addinan juna, ba tare da nuna yatsa ga wadanda ba addinanmu daya da su ba.
Kamar yadda za mu lura, Allah cikin ikonSa da hikimarSa, Ya halitta kuma Ya kadarta mutane masu mabambantan akida da addini su rayu a cikin kasa daya. Idan kowane mai addini ya cije wuri guda ya ce dole sai ra’ayin addinisa za a bi domin a tafi tare, lallai kam haka faufau ba za ta yiwu ba. Idan haka ne, kuma haka din ne ma, to ina dubara, ina mafita? Akwai ta, kuma guda daya ce. Abin yi shi ne, a matsayinmu na ’yan kasa daya, kowa ya rike martabar addininsa, ya bi darussan da ke shimfide cikin addininsa sau da kafa, ba tare da ya kawo wa dan uwansa mabiyin wani addini cikas ba. Idan aka yi haka, shi ke nan, an huta da kace-nace. Kai mabiyin addinin Kirista, sai ka ci gaba da bin kiristancinka, kai ma mabiyin Musulunci, sai ka ci gaba da bin musuluncinka. Hatta ma wadanda ke bin addinin gargajiya, tun da dai su ma ’yan kasa ne, sai su ci gaba da bin nasu addinin. Shi ke nan, husuma ta kare, babu hairani.
A matasyinka ba Musulmi, idan kana son mutane su shiga addininka, sai ka bi hanyar da Allah Ya huwace maka, ta nuna kyakkyawan misali, wato ka rika mu’amala mai kyau da nuna halayya tagari ga al’umma, kamar yadda addininka ya koya maka. Za ka rika yin rayuwa ta tawali’u, kana aiwatar da komai cikin gaskiya, adalci da amana da son al’umma. Wadannan kyawawan halaye, za su zama abin koyi kuma abin sha’awa ga sauran al’umma. Ta haka sai ka ga wadanda ba mabiyan addininka ba suna sha’awarka, suna sha’awar rayuwarka. Babu mamaki idan ka yi masu tayi, su shigo su ma su zama Musulmi.
Haka shi ma mabiyin Kiristanci, idan har yana son wani ya shiga addininsa, abin da zai yi ke nan. Wato ya bibiyi rayuwarsa cikin aminci da gaskiya da adalci. Idan aka yi haka, shi ke nan an huta da husuma.
Wani abin da ya kamata mu fahimta shi ne, duk wani addini, madamar na kirki ne, to manufarsa ita ce samar da tsira da ci gaban dan Adam. Babu wani addini da ya amsa sunansa da ya amince da ka uzura wa wani ko ka yi wa wani ta’addanci. Duk wani addini na mutunci, burinsa shi ne ya jagoranci dan Adam zuwa ga aikata kyawawan ayyuka kuma ya hana shi aikata munana. Don haka, kishin kasa ne ga dan kasa ya jure wa zaman tare tsakaninsa da abokin zamansa, koda kuwa addininsu ya bambanta.
Yana kuma daga kishin kasa ga mutum ya kasance mai tafiyar da al’amuransa cikin gaskiya da amana, wato ya guje wa ha’inci. A yayin da rikon amana da gaskiya suka kasance jigogin kishin kasa, shi kuwa ha’inci ya kasance makamin ruguza kasa. Sai mu kama dabi’un kirki, mu watsar da na banza, madamar dai muna son mu ga muna samun ci gaba da bunkasa.
Yaudara, halayya ce mai saukin aikatawa, amma illar da ke tattare da ita tana da yawa. Ba kishin kasa ba ne ga dan kasa ya kasance cikin halayyar yaudara, domin kuwa babu abin da take haifarwa sai koma-baya ga al’umma da kasa baki daya. Ke nan, ya zama wajibi mu guji yaudara, tun da dai na tabbata babu mai son ya ga cewa wani ya yaudare shi. To, dan uwa, abin da ka san cewa ba ka son a yi maka, yaushe kuma kai za ka yi wa wani? Babu hikima cikin wannan ko kadan.
Wadannan dabi’u: Shashanci, tambele, hassada, gaba, gilli da ayarinsu, dabi’u ne da tuni suka kauce wa hanyar kwarai kuma duk wanda ya siffatu da aikata su, bai kasance dan kishin kasa ba. Lallai ne mu kaurace musu, domin mu kasance ’yan kasa nagari masu kishin kasa da kishin al’umma.
Wajibi ne a gare mu mu kasance masu bin dokokin kasa, kamar yadda aka shimfida su. Ta hanyar bin dokokin ne za mu samu tafiyar da al’amuranmu cikin tsari da inganci. Idan kuwa muka kasance muna zama cikin karya doka, muka zauna zaman-kara-zube, babu babba babu yaro, to rayuwarmu ba za ta sha bamban da ta dabbobi ba. Idan haka ta faru, shi ke nan mutuwar kasa ta zo, wanda kuma ba haka aka so ba, wai kanen miji ya fi miji kyau.
A yayin da muke rufe wannan maudu’i, zan yi kira ga al’umma, manyanmu da kanananmu, mazanmu da matanmu da cewa lallai ne mu tashi tsaye mu ceto kasarmu, mu kasance masu kishinta nakwarai, masu son ta da kishin ci gabanta. Kada mu bari ta fadi ko ta ruguje, domin kuwa ba mu da wata kasa kamar ta.
Wassalam. Sai kuma mun hadu a mako na gaba.

Dausayin kauna

Takaddamar Soyayya: Tsakanin Maza Da Mata, Wa Ya Fi Rikon Alkawarin Soyayya? (5)

Masoya, mun shiga mako na biyar cikin wannan baban maudu’i na takaddama tsakanin maza da mata. Yau ma da ikon Allah za mu dora.
Gimbiya Bilkisu Abdulrazak Rimi, ’yar mutan Funtuwa (07033588837) ce ta bude mana filin da cewa: “Dankari makari! Ai ko a sikeli aka gwada an san mun fi maza rike alkawarin soyayya. Magana ta gaskiya mun fi maza kokarin ganin mun rike alkawari, musamman ma a fannin soyayya. Ku duba ku gani, sau nawa namiji zai zo wurin mace da maganar aure, sai mun gama amincewa da shi mun saki jiki, sai sun gama daukar alkawari tsakaninsu da zarar an yi maganar aure sai ka nemi kafarsa ka rasa, wanda in da ita ce ba za ta taba guje masa ba, koda kuwa bai shirya aure ba; za ta iya zaman jiransa har sai ya shirya, saboda alkawarin da ke tsakaninsu. Ku duba ku ga mata tana zaune da mijinta lafiya amma da zarar lalura ta same ta, idan ya gaji da magani sai ya tattara ta ya maida ita gida, sai dai ta ji ya yi aure. Wa’iyazu billahi! Wanda idan da ita ce, za ta iya zama da shi har sai in mai rabawa ce ta raba. Da wannan nake kafa hujja tare da kara cewa mata sun fi maza alkawari. Maza ba ku da alkawari – namiji, namiji!”
Shi kuwa Salisu Haladu, wanda aka fi sani da Hapijo (08065994746), a nasa batun ya ce: “So dai kowa yana sane da cewa ba ya da magani, sai dai ko a mallaki abun da ake son ko kuma dole a hakura! Babu makawa maza ne suka fi rikon alkawarin soyayya, tun da ai mata ake nema ba maza ba. Namiji dai ba ya zuwa wajen mace sai idan ta yi mashi kuma ya nace a kanta har sai ya aure ta. Ita kuwa mace, zo mata ake yi kamar Gimbiyar Zuma, kuma dukansu sai ta saurare su ko da so ko kuma babu. Namiji mai alkawari ne ke daurewa har ya dace da kai amaryarsa gida. Kuma idan macen na gidan, shi zai yi ta lallashi da shagwaba ta har su haihu kuma har mai rabawa ta raba su.”
Sai kuma sakon Aminu Fifa Jega (07063065355) da ke cewa: “Managar gaskiya maza sun fi mata rike alkawari, domin sau da yawa namiji zai yi alkawarin auren yarinya tun tana makaranta JS1, har ta kai ga kammala SS3 yana nan rike da alkawarin, ba zai canza ba saboda sanin darajar alkawari da tausayi irin namu na maza. Amma mace koda alkawarin aure kuka yi kai da ita, ko ka share shekara goma kana mata bauta; ranar da ta samu wanda ya fi ka abin duniya sai ka ji ta ce ba ta son ka, ba ta ra’ayinka  saboda rashin sanin daraja alkawari.”
Ita kuwa Dinatu Sule Hamman daga Jihar Taraba (08160717308), sakonta yana cike da ban tausayi. Ga abin da take cewa: “Gaskiya tsakani da Allah maza su ne masu yaudarar mata. A wasu shekaru da suka wuce, lokacin ina da shekara 14, ina karatu a sakandare; mutum biyu, akwai wani malaminmu wanda ya nace sai ya yi fasikanci da ni, na ki. Ya sa aka yi mani bulala 12. Daga nan na yi ciwon tabuwar hankali, har na kurmance ba tare da an hukunta shi ba kuma har wayau ina fama da wannan rashin zaman lafiya wajen maza.
“A rayuwata, bayan na kai shekara 17, wani saurayi ya fito yana so na, yana dai yi min wadansu dawainiya da kuma kyaututtuk. Saboda halin da nake ciki, mahaifina kuma Allah Ya yi masa rasuwa. Muna tafiya dai da mutunci. Ni yarinya ce mai kamun kai. Wata rana da kawata Abu ta ziyarce ni, a kauyensu tana da wa, marigayi Sani, abokin saurayina Felid suka gama baki ya yi min fyade. Bayan wata biyu na fara kukan ciwon ciki. Shi saurayin nawa likita ne, ya san juna biyu ne da ni amma ina karama ban san haka ba. Ya dauko wata katuwar allura ya dora mani a cinya. Allah dai ya sa kwanana yana gaba.
“Abin ya yi karfi har ya kai ga iyaye, aka kai ni asibitin Federal Medical Center na Jalingo. Likitoci suka gane abin da yake tafiya, aka kai ga ’yan sanda. Da an je a dauko shi sai ya sulale ya gudu. Ina rai ga Allah, aka tukumi iyayensa su dawo da shi suka ki. An yi mani aikin tiyata, kamar na mutu. Bai dawo wurina neman gafara ba har wayau, ni kuma ina son shi matuka. Na matsa wa yayansa Sunday da ya dawo min da shi amma bai yarda ba, yana cewa dan uwansa ba zai auri kurma ba.
“Ni dai har na mutu ba zan taba mantawa da yaudarar maza ba. Yadda maza suke so na na ki su, ina son shi. Lallai so cuta ne. har yanzu yana raina, ba na kaunar kowane namiji a duniya sai dai Felid. Ina nan zama na kuma Allah Ya sa ya gane kuskurensa, ya tuba.”