Muhimmancin kula da masu lalurar kwakwalwa
An yi kiyasin cewa, a duk cikin mutane hudu a A Najeriya, ana iya samun daya da yake da matsalar lalurar kwakwalwa
Ba da jimawa ba ne aka gudanar da bikin Ranar Kula da Masu Lalurar Kwakwalwa ta Duniya, wanda ya mayar da hankali wajen tattauna muhimmancin bai wa lafiyar kwakwalwa fifiko a bangaren kiwon lafiya, saboda tasirin hakan ga cigaban rayuwa baki daya.
Majalisar Dinkin Duniya ce ta ware wannan ranar a shekarar 1992 domin fadakar da al’ummar duniya, da karkatar da tunaninsu ga muhimmancin kula da inganta lafiyar kwakwalwa da fadakar da jama’a illar nuna wa masu fama da lalurar kwakwalwa kyama ko wariya.
Har wa yau tsayar da ranar na da muhimmanci duba da irin yadda ake samun karuwar jama’a masu samun lalurar kwakwalwa a duniya, sakamakon canje-canje da tsadar rayuwa da ake fuskanta.
Wata kididdiga ta baya-bayan nan ta bayyana cewa, akwai mutane miliyan dari tara da saba’in a duniya da aka tabbatar suna fama da lalurar kwakwalwa, ban da dubban wasu da ba a san halin da suke ciki ba, kuma suke rayuwa cikin kunci da tsangwama, a tsakanin ’yan uwa da iyaye, ko kuma suna yawon bin bola a tituna.
A nahiyar Afirka an gano akwai akalla mutane miliyan 116 da suka samu tabin hankali, yayin da a Najeriya aka yi kiyasin cewa, a duk cikin mutane hudu ana iya samun daya da yake da matsalar lalurar kwakwalwa, ko da ya sani ko bai sani ba.
Alamomin lalurar kwakwalwa
Daga cikin alamomin da ake iya kula a gane mutum na dauke da wannan damuwa, ko kuma a ce hankalin sa ya fara tabuwa, a cewar wani kwararren likitan kwakwalwa, Dokta Maigari Yusuf Taru, idan aka ga halayyar mutum na canzawa daga wani yanayi da aka saba da shi zuwa wasu halaye da ba san shi da su ba.
Misali shi ne, idan an ga mutum mai tsafta ya fara zama kazami, ko mutum mai shiru shiru, a ga ya koma magana barkatai, ko idan yana da son shiga jama’a sai a ga lokaci guda ya koma kebe kansa yana gudun jama’a.
Ko kuma a ji mutum na yawan zargin wasu na shirya masa mugunta ko neman ganin bayansa.
Me ke kawo lalurar kwakwalwa a Najeriya?
- Matsin rayuwa
Shugaban kungiyar kwararrun masana ilimin dabi’ar kwakwalwar dan Adam ta Najeriya, Farfesa Taiwo Obindo, ya bayyana damuwa kan yadda ake samun yawaitar masu fama da lalurar kwakwalwa a Najeriya, inda ya bayyana cewa kawo yanzu akwai ’yan Najeriya kimanin miliyan 60 da ke fama da wannan matsala, kuma yawancinsu suna rayuwa ne cikin jama’a, wanda aka danganta da halin tabarbarewar tattalin arziki da kuncin rayuwa da ake fuskanta.
- Shan magunguna
Masana harkar lafiya na ganin matsaloli na rayuwa, shaye-shayen magunguna barkatai, kwayoyin halitta na gado da shan sinadarai masu karfi ko karayar zuciya, a dalilin bacin rai na daga cikin dalilan da suke kawo tabuwar kwakwalwa.
- Kafin haihuwa
Kuma a cewar kwararru, ana iya samun lalurar kwakwalwa tun daga ciki kafin a haifi mutum, sakamakon wasu dalilai na ganganci ko kuskure ko wasu magunguna da mai ciki take sha wanda zai iya rikita kwakwalwar jaririn da ke cikinta.
- Shekaru
Mutane na iya kamuwa da lalurar kwakwalwa saboda shekaru ko yawan mu’amala da zaurukan sada zumunta yana iya shafar tunanin mutum da yanayin rayuwarsa, saboda yana ganin wasu ba sa kaunar sa ko ba a nuna masa kauna, ba a yi masa sharhi ko tsokaci a abubuwan da yake dorawa a giza gizan sadarwa da yake amfani da su.
- Shafukan sada zumunta
Bincike ya nuna cewa, yawan mu’amala da shafukan sadarwa yana haifar da matsalolin damuwa, fargaba, tsoro, da karayar zuciya, a sakamakon yadda mutum ke ganin yadda shafinsa na sadarwa ke jan hankalin jama’a ko akasin haka.
- Alfahari
Har wa yau kuma yadda wasu ke nuna irin jin dadin da suke yi da matsayinsu a idon duniya, yana sa wasu su ji kaskanci a ransu, har abin ya fara sa suna jin haushin kansu ko kunyar bayyana kansu, don kada a yi musu tunanin kimar su ba ta kai ba.
- Shaye-shaye
Yawan shaye shaye a tsakanin matasa maza da mata.
Misalin Shisha da ake ganin ba komai ba ce, bincike ya gano tana dauke da sinadaren da ke taba lafiyar kwakwalwa, tana kuma zama kalubale ga cigaban rayuwar matasa da makomarsu, a matsayinsu na manyan gobe.
Abin da ya kamata a yi
Wani tsohon shugaban kungiyar likitoci ta Nijeriya ya taba bayyana bukatar Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sa a rika yi wa ’yan siyasa masu fitowa takarar mukamai daban-daban gwajin lafiyar kwakwalwa, saboda tabbatar da ingancin lafiyarsu, lura da irin yadda wasu ’yan siyasa ke wawurar dukiyar kasa da almubazzaranci, wanda ya saba da aiki da hankali.
- Ba da muhimmanci ga lamarin
An yi kira ga hukumomin da abin ya shafa su rika ba da muhimmanci ga al’amarin kula da lafiyar kwakwalwa, samar da tallafin magunguna da inshorar lafiya, bude rassan kula da masu fama da lalurar kwakwalwa a kananan asibitoci na kauyuka da karkara, domin kara kusanto da harkar kula da lafiyar kwakwalwa ga jama’ar da ke kauyuka da karkara.
- Saurin daukar mataki
Sannan ana bukatar iyaye da yan uwa su rika gaggawar daukar matakin neman magani da shawarwarin likita yayin da suka lura da canji a rayuwar wani makusancinsu tun kafin abin ya fita daga matakin da za a iya gyarawa ko dawo da shi daidai.
- Daina kyamar su
A guji nuna kyama ko tsangwama ga wadanda ke cikin wannan hali, a nuna musu kauna da kulawa, don haka ne zai sa musu natsuwa da yarda a zukatansu, har su amince su iya ba da hadin kai a samar musu da magani da kulawar da ta kamata.