Muhimmancin taimakon juna

Assalamu alaikum Edita. Kowa ya taimaki wani shi ma Allah zai taimake shi, albarkacin wannan rana nake son ku ba ni dama in yi kira ga al’umma musammam makwabta mazauna unguwa daya da kuma masu hannu da shuni, cewa ya kamata mu rika taimakon juna. Musamman fannin sha’anin rayuwar yau da kullum ga talakawan cikinmu […]

Muhimmancin taimakon juna
Muhimmancin taimakon juna

Assalamu alaikum Edita. Kowa ya taimaki wani shi ma Allah zai taimake shi, albarkacin wannan rana nake son ku ba ni dama in yi kira ga al’umma musammam makwabta mazauna unguwa daya da kuma masu hannu da shuni, cewa ya kamata mu rika taimakon juna. Musamman fannin sha’anin rayuwar yau da kullum ga talakawan cikinmu masu karamin karfi, wadanda abincin da za su ci ma yana neman ya fi karfinsu. Ya kamata mu himmatu wajen tallafa musu tare da iyalansu, domin mu gudu tare mu tsira tare.

Haka zalika akwai wadanda su kuma nasu taimakon na daban ne, saboda halin da suke ciki na tausayawa wato marayu wadanda ba su da uwa ba uba. Ya kamata duk wanda yake da halin taimakawa to hankalinsa ya karkata zuwa can. Domin a ba su taimako gwargwadon hali, ba don komai ba sai don irin tarin ladar da ke tattare da irin wannan taimako matukar an yi shi don Allah ba don duniya su yaba ba. Allah Ya ba mu ikon taimakawa, amin.

Sannan hakika ya dace in saka gwamnati cikin wannan rubutu nawa dalili kuwa shi ne ita ya dace ta fi kowa taimaka wa al’ummar kasarta. Domin haka ake yin gwamnati, amma sai dai ita gwamnati ba mutum ba ce, mutane ne ke tafiyar da ita. In kuwa haka ne me zai hana mutanen da ke tafiyar da ita su rika tunawa da halin da al’umma ke ciki don share musu hawaye maimakon ba da fifiko da mafi yawancin masu ruwa-da-tsaki a gwamnati ke yi ga bukatun kansu fiye da na talakawa? Saboda haka nake kira ga daukacin mutanen da Allah Ya ba su dama na zama shugabannin cewa su yi gaskiya da adalci wajen taimakon al’ummar da suke shugabanta ta hanyar ba da fiffiko ga yin ayyukan da za su inganta rayuwar jama’a. Allah Ya sa mu dace Ya sa kirana ya amfane mu baki daya, amin summa amin

Hussaini Abba Dambam, Dambam, Jihar Bauchi 08020814173