Muhimmancin watannin aikin hajji
A Musulunci, da zarar watan Shawwal na karamar sallah ya kama, to watannin aikin hajji ma sun kama. Watan Shawwal da Zul-ki’da da kwanaki 10 na farkon Zul-hijja su ne watannin da aka yarda maniyyaci ya yi harama ya kama hanyar tafiya Makka domin sauke farali. Hajji dai ibada ce da aka wajabta wa Musulmin […]
A Musulunci, da zarar watan Shawwal na karamar sallah ya kama, to watannin aikin hajji ma sun kama. Watan Shawwal da Zul-ki’da da kwanaki 10 na farkon Zul-hijja su ne watannin da aka yarda maniyyaci ya yi harama ya kama hanyar tafiya Makka domin sauke farali. Hajji dai ibada ce da aka wajabta wa Musulmin da ke da iko sau daya tak a rayuwar shi. Ibada ce da Allah Ta’ala Ke son Musulmi su kawar da duk wani bambanci a tsakaninsu su fito masu bautawa Mahaliccinsu ba tare da wasa ko son zuciya ba. Hakan ne ma ya sa Allah ya sanya lokacin wannan ibada a wasu watanni da ake kira “Ashhurul hurum” wato watanni da aka haramta duk wani aiki na sabo ko zalunci ko yaki ko tashin hankali. Kamata ya yi Musulmi da maniyyatan da wasunsu, su kwaikwayi salon rayuwar Mala’iku wajen ibada ba tare da saba wa Allah ko zaluntar junansu ba. Samun damar zuwa wannan waje na ibada babban alheri ne ga bawa, mutunta wajen kuwa na daga cikin mutunta iyakokin Allah Ta’ala. Yadda ake ribanya lada ga wanda ya yi ibada a wannan waje, haka kuma Allah Ke ninka alhaki a kan wanda ya yi zunubi a wajen.
Mahimmanci kiyaye dokokin Allah a Makka ya kai a ko a zuci ka raya aikata saon Allah a Makka, to Allah Ya yi alkawarin sai ya azabtar da kai; ballantana kuma ka aikata sabon. Maniyyatan da ke zuwa su bige da sabawa Allah a wajen lallai su shiga hankalinsu. Ko bawa kamarka ba a yarda ka masa isgilanci a Makka ba, ballantana Mahaliccinmu baki daya. Sahabban Manzon Allah (SAW) duk da takawarsu da tsantseninsu, amma da zarar sun zo Makka sun gama ibadar da ta kawosu, cikin hanzari su ke fita su koma Madina, saboda tsoron kar su yi wani abu da zai ia zama zunubi ya zamo sun fada cikin wadanda za su fada cikin fushin Allah.
Wasu maniyyatan na zamani kuwa har da gayya ma suke tafiya domin tafka ta’asa a wannan gari mai tsarki. Ina kira ga duk wanda ya karanta wannan bayani ya yawaita addu’a Allah Ya tsaftace wannan gari mai tsarki daga barin duk wani iblishin mutumin da ke zuwa domin ya saba wa Allah a cikin shi. Maniyyatanmu kuma Allah Ya sa su yi aiki karbabbe su kuma dawo gida lafia. AMIN YA RABBI. [email protected] 07061587787.