Muhimmandin soyayya a rayuwar aure (2)

Bayan kamar wata uku da xaura aurenmu iyalina ta tambayeni wai me ya sa kullum sai kara shiga zudiyarta nake alhali an faxa mata sati biyu ma ya yi yawa za ta fara jin haushina? A maimakon a ga ta rame, ta kanjame, kuma ta yi baki kamar yadda ake yawan gani idan wasu suka […]

Muhimmandin soyayya a rayuwar aure (2)

Bayan kamar wata uku da xaura aurenmu iyalina ta tambayeni wai me ya sa kullum sai kara shiga zudiyarta nake alhali an faxa mata sati biyu ma ya yi yawa za ta fara jin haushina? A maimakon a ga ta rame, ta kanjame, kuma ta yi baki kamar yadda ake yawan gani idan wasu suka yi aure saboda rashin samun natsuwa da kwandiyar hankali, ita kuma Gimbiya Ummul Salmah sai kara kiba take kuma hakan kamar ana kara mata kaimi ne wajen kyautata mini da ba ni girmana a matsayina na maigidanta. Kada in dika mai karatu da surutu ina so ’yan uwana ma’aurata da ma samari da ’yan mata waxanda suka xaura kyakkyawar niyyar aure su fahimdi duk auren da aka gina shi da tubalin hakuri kawai ba tare da an haxa da tubalin soyayya, kyautatawa da nishaxantarwa ba, to tabbas irin wannan aure ba ya xorewa, ko ya xore ma ba a dikin kwandiyar hankali da annashuwa ba. Yana da matukar muhimmandi ma’aurata da masu niyyar aure su zamanto zudiyoyinsu na xauke da kyakkawar niyyar ibadar aure saboda Allah (s.w.t). Namijin da ya yi aure ba don Allah ba shi ne wanda kullum idan zai shigo gidansa sai ya haxe rai kamar kumurdin madiji yana kumburi wai shi namiji ne dole a ba shi girma.

Kasandewar namiji shi ne shugaban iyalinsa wanda hakkin kula da iyalin ke rataye a wuyansa, zan yi amfani da wannan dama wajen isar mana da sakonnin shawarwari waxanda i sha Allah za su taimaka ainun wajen samun zaman lafiya da xorewar zamantakewar aure. Ga su kamar haka;

1. Ka tuna da sadaukarwar da ta yi maka: Xan uwa saurara ka ji. Ba kai kaxai ba ne namiji a duniya, kuma ba kai kaxai ne namijn da yake son aurenta ba. Kuna da yawa watakila ma kun kai dozin kowa da gaske yake. Amma wannan baiwar Allah duk ta share su ta zabeka saboda a wajenta ka fi sauran. Su kuwa sauran watakila daga dikinsu akwai masu jin haushinta  saboda rashin ba su dama. Ya kai xan uwa don Allah idan ka tuna haka shin ba za ka yi tunanin yi mata kyautatawar da za ta rika tunani ta fi kowade made sa a a duniyar nan ba? Idan ba ka yi haka ba za ka sa ta rayu tana da-na-sanin ba ka wannan damar. Ana gane karfin namiji ne wajen kyautatawa ba kuntatawa iyalinsa ba.

2. Xaukar aure a matsayin Ibada: Anas Ibn Malik (Allah Ya kara yarda da shi) ya ruwaito Annabi (s.a.w) ya de duk wanda Allah (s.w.t) ya taimaka masa ya yi aure kuma ya samu made ta-gari tamkar ya dika rabin addininsa ne. Ashe wannan ba zai sa mu mazaje mu rika xaukar aure a matsayin ibada domin samun yardar Allah (s.w.t) ba? Ya kai xan uwa shin kana ganin Allah zai dika maka rabin addininka alhali kana take hakkin iyalinka? Rayuwar auren da babu komai a dikinta sai dutarwa, kuntatawa, bakin diki da rashin kwandiyar hankali tamkar rusa rabin addini ne. Allah Shi ne masani. Ka sake tunani ya kai xan uwa, idan har ka yi aure ne domin bauta wa Allah ta hanyar kyautatawa iyalanka da ba su hakkinsu dadai gwargwadon karfinka to babu shakka ba za ka taba tunanin xaga hannu ka bugi iyalinka ba ko ka take mata hakkinta komai kankantarsa.

3. Ka tuna kana da kanwa: ko da ba diki xaya kuka fito ba ka tuna kai ma kana da ’yar uwa made wadde ba za ka so a dutar da ita ba, kuma idan sun yi aure za ka so a de suna zaman lafiya da kwandiyar hankali. Kar ka yi abin da ba ka so a yi maka ko a yi wa wani naka. Yana da kyau ka rika kallon iyalinka matsayin matarka, kanwarka, kawarka, xalibarka kuma babbar na hannun damarka  wadde za ka iya tuntuba domin neman wasu shawarwari idan bukatar hakan ta taso. Annabi (s.a.w) ma ya kan nemi shawarwari daga wajen iyalinsa musamman Ummul Salmah (Allah Ya kara yarda da ita) ballantana mu!

4. Yana da kyau mu mazaje mu dire girman kai mu rika yaba wa iyalanmu bisa kokarinsu, kuma mu rika jan su a jiki muna nuna musu muhimmandinsu a rayuwarmu, su ma mata su kara zage damtse wajen nuna ladabi da biyayya ga mazajensu domin hakan yana inganta soyayyar rayuwar aure. Maigida ka kasande mai yaba wa girkinta, kwalliyarta da sauran ayyukan gida. Mata suna son hakan domin yin hakan yana kara musu kaimi wajen kokarin kyautata wa mazajensu ta hanyoyi daban-daban..

A karshe ina kira ga ’yan uwana maza da mata da mu tattara dukkan daxaxxun kalamai na soyayya da irin kyautatawar da suka saba yi wa junansu kafin su yi aure zuwa dikin rayuwarmu ta aure. Barin waxannnan sinadaran a waje yana yin illa sosai ga tubalin zamantakewar ma’auratan. Saboda haka al’ummar Hausawa ya kamata mu tashi tsaye wajen ganin mun zama abin misaltuwa idan ana maganar kyan rayuwa da zamantakewar aure. Allah Ya sa mu dade, Amin.

Nasiru Tanimu Annuri, ya rubuto ne daga sansanin  masu yi wa kasa hidima (NYSd) da ke Wamakko, Jihar Sakkwato

08137284277 (sakon tes kawai)  Imel: [email protected]