Muhimmin sako ga ma’aurata
Yawan mace-macen aure a cikin alummarmu ba bakon abu ba ne, musamman Hausawanmu, hakan kuwa ya samo asali ne daga rashin iya kyakkyawar mu’amala a tsakanin ma’aurata. Don haka duk wata al’umma da ta lalace, to za ka ga yanayin aurenta ya lalace. Akwai hikimar Allah da Ya halicci mace daga namiji; hikimar kuwa ita […]
Yawan mace-macen aure a cikin alummarmu ba bakon abu ba ne, musamman Hausawanmu, hakan kuwa ya samo asali ne daga rashin iya kyakkyawar mu’amala a tsakanin ma’aurata.
Don haka duk wata al’umma da ta lalace, to za ka ga yanayin aurenta ya lalace. Akwai hikimar Allah da Ya halicci mace daga namiji; hikimar kuwa ita ce, da Ya sanya namiji shugaba a kan mace, shi ne zai fita waje, ita kuma ta tsaya a gida, saboda mace ita ta dace da zaman gida, da yanayin gida. Shi ya sa Allah Madaukakin Sarki Ya ce namiji shi ne mai karfi a kan mace, dangane da aure, shi ya sa idan gida ya lalace namiji za a zarga ba mace ba, saboda shi ne shugaba. Don haka dole ne namiji ya koyi duk wata hanya ta shugabancin iyali.
Akwai ruwaya da take cewa, duk magidanci yana bukatuwa ga abubuwa guda uku, na farko; kyakkyawar mu’amala; ya yi kokari ya koye su. Ko da bai iya ba.
Na biyu yalwata wa iyali. Na uku, ya zama mai kishin iyalinsa, kada ya zama soko ko wani talasuru marar kishi. Misali, wanda zai tare wa matarsa dan acaba ta hau, ko idan abokinsa ya zo gidansa, ya shigo da shi cikin gida ko da matar tasa ba ta cikin hijabi, ka ga wannan rashin kishi ne.
Ana bukatar namiji wajen gamsar da matarsa, wanda hakan zai sa ta dace da shi, kuma ta haka ne zai mallake komai nata, ya kasance ka girmama ta, kuma ka koya mata girmama mutane, ba wai ka rika daka mata tsawa ba ko ka rika hantarar ta. Yi kokari ka ga ka mallaki zuciyarta, domin namiji ya kware wajen jan hankalin mata, musamman ta fannin yin ado da kwalliya. Ba daidai ba ne mutum ya je wa matarsa yana warin rana ko hammata.
Ya kasance ka yalwata mata daidai gwargwadon abin da Allah Ya hore maka, kada ka ci nama a waje mai dadi, ita kuma ka kawo mata garau-garau, wannan bai dace ba.
Ita kuwa mace ta yi kokarin kare kanta ta hanyar yi wa kanta adalci da kuma gyaran jiki, domin da haka ne kullum namiji zai rika sha’awarki, bai halarta ba a ce kin yi kwalliya ga wani wanda ba mijinki ba, ki kasance mai kewaye mijinki da so da kauna, domin namiji yana son haka, cikin sauki za ki mallake zuciyarsa. Manzon Allah (SAW) yana cewa, fadin namiji ga matarsa, ina son ki hakan ba ya fita daga zuciyarsa har abada.
Haka nan ana so, duk abin da za ki yi ki yi shi cikin tsarkakkiyar niyya da kyawun zuciya, idan mijinki ya ba ki abu ki kula da shi, idan ya yi mantuwa ko ya jefar da wani abu ki dauka ki adana masa, ba tare da son zuciya ba.
Idan kuwa kin fita unguwa ko sayayya, to ki kame kanki, babu ruwanki da maganganun da za su zubar da mutucinki. Abin da takaici a zamani nan da za ka ga mace ta je sayayya, amma sai ta buge da zantuttuka mara sa amfani.
Hakika kyautatawa tsakanin ma’aurata abu ne mai muhimmanci da ya kara wa aure martaba da daraja, kuma lallai yana da kyau a rika godiya a kan abin da ake yi wa juna na alheri, domin hakan kan sanya kowane bangare ya dada himma a kan abin da yake yi. Kada ka ce ba wajibi ba ne ka yi mata kaza……. Domin kai ma akwai abubuwa da yawa da ba wajibi ba ne a kan ta.
Lallai ma’aurata na da muhimmiyar rawar takawa wajen inganta zamantakewa da tattalin arziki da kwanciyar hankali a kasa, domin zaman lafiyar iyali shi ne zaman lafiyar kasa. Allah ya yi mana agaji.
Ibrahim Hamisu Kabara
08060651676