Mujallar Magama tana karfafa dangantaka tsakanin Najeriya da Amurka

Sunan Mujalla:     Magama Mawallafa:     Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya Shekarar Wallafa:  Disamba/Janairu, 2018 Yawan Shafi:     18 Farashi:     Kyauta Mai sharhi: Kamal Abdulrahman Dodo Mujallar Magama wacce Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ke wallafawa, mujalla ce mai ban sha’awa musamman yadda ake buga ta cikin harshen Hausa kuma […]

Mujallar Magama tana karfafa dangantaka tsakanin Najeriya da Amurka

Sunan Mujalla:    Magama

Mawallafa:    Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya

Shekarar Wallafa:  Disamba/Janairu, 2018

Yawan Shafi:    18

Farashi:    Kyauta

Mai sharhi: Kamal Abdulrahman Dodo

Mujallar Magama wacce Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ke wallafawa, mujalla ce mai ban sha’awa musamman yadda ake buga ta cikin harshen Hausa kuma ake kokarin kutsawa da ita cikin kowane lungu da sako na Arewacin kasar nan.

Hakan na iya taimakawa wajen wayar wa mutane kai ta fuskoki da dama da suka hada da gane irin hakikanin dangantakar da ke tsakanin Najeriya da kasar Amurka da kuma irin tallafin da Najeriya ke samu ta fuskar habaka ilimin kimiya da kere-kere, kamar yadda hakan ya bayyana a cikin mujallar ta watan Disambar 2017/Janairun 2018 shafi na 4.

Sai dai kuma za mu iya fahimtar cewa irin wadannan shirye- shirye na habaka ilimin kimiyya da kere-keren sun fi mayar da hankali ne a sashin Kudancin kasar nan, kamar yadda mujallar ta ruwaito mana cewa Daraktan Cibiyar Sarrafa Mutum-Mutumi ta Arewacin Amurka (RoboRAbE) Brian Montoya yana ganawa da daliban makaranta lokacin gasar sarrafa mutum-mutumi mai motsi, duk wadannan dalibai sun fito ne a tsakanin Jihar Legas da kuma Ogun, maimakon a ce an samu dalibai daga jihohi 36 na kasar nan.

Haka kuma mujallar a shafinta na 15, mun ga irin gudunmawar da kasar Amurka ke bai wa Najeriya ta fuskar habaka sana’ar fina-finai, kamar yadda ta ruwaito mana cewa Sashen Hulda da Jama’a na Ofishin Jakadancin Amurika (PAS) da ke Abuja ya dauki nauyin karrama Ba’amurke mai sarrafa fina-finai, marubuci kuma Darakta Doug Blush a ziyarar mako guda da ya kawo Najeriya.

To, hakan ya yi, amma an hasko mana wannan masani a Jihar Legas shi da kwararrun masu shirin fina-finai. Amma ba mu ji labarin ya je ko zai je Kano ba, inda kwararrun masu shirin fina-finan Hausa suke da sansani.

Mujallar Magama mai matukar ban sha’awa ce in muka yi la’akari da irin gudunmawar da take bayarwa ta bangaren ilimantarwa da nishadi da kuma ba jama’a damar sanin abubuwan da suke faruwa a siyasance da zamantakewa. Misali, idan muka dauki shafin mujallar na 16 za mu ga Shirin Asusun Raya Ilimi Don Inganta Rayuwa da Asusun Bayar Da Tallafin Ilimi na Amurka (The Education USA Opportunity Funds Program) suna taimaka wa masu basira da kwazo, masu jajircewa, sai dai daliban da suka fito daga gidaje masu karamin karfi, kuma sun cancanci tallafin daukar dawainiyar karatu daga kwalejoji da jami’o’in Amurka, sannan ba su da karfin biyan kudin samun makaranta.

Wannan batu na mujallar na kokarin bayyana mana yadda kasar Amurka ke taimaka wa ’ya’yan talakawa masu basira da hazaka wajen daukar nauyinsu daga Najeriya zuwa Amurka ko wasu kasashe na daban, don ganin sun ci gaba da karatunsu.

Kuma mujallar ta ruwaito cewa za a sake bude kafar neman wannan damar nan da 1 ga Afrilun bana, inda za a rufe ranar 30 ga Yuni na bana. Bayan haka, ta ci gaba da cewa: “Ana maraba da masu neman guraben karatu daga daukacin jihohin Najeriya.” To, Allah Ya tabbatar da alheri, Ya kuma kara dankon zumunci tsakanin kasar Amurka da Najeriya.

Sai dai mu fatanmu a nan shi ne mu ga Mujallar Magama ta ruwaito cewa an ba Musa da Isa da Yusuf wannan dama, kamar yadda muka ga ta wallafa sunayen su Bukola Adeoye, Ifunanya Nwolah da kuma Egbunu Mudi a matsayin wadanda suka samu nasarar shiga cikin wannan dama. Yin hakan zai kara wa mujallar kwarjini a idon mutanen Arewa.

Tunda Mujallar Magama ta ruwaito mana cewa taron hadin gwiwar BNC (Hukumar Hadin Gwiwar Amurka Da Najeriya), wanda aka gudanar a Abuja ranar 20 ga Nuwamban 2017, ya mayar da hankali ne a kan abubuwa uku, wadanda suka hada da hadin gwiwa kan harkokin tsaro, bunkasar tattalin arziki da raya kasa da kuma shugabanci da dimokuradiyya. To idan muka dauki bunkasar tattalin arziki da raya kasa, za mu iya sa ran cewa mujallar a karo na gaba za ta kawo mana irin shirye- shiryen da wannan hukuma ke yi don ganin an kawo karshen tsabar talauci da rashin aikin yi a tsakanin matasa da kuma rugurgujewar masana’antun kasar nan, don su ma suna taimakawa kwarai matuka wajen habakar tattalin arziki. 

A nan ne zan yi amfani da wannan dama in jawo hankalin mujallar cewa, ya kamata ta samar da wani shafi a cikinta wanda zai mayar da hankali a kan noma da kiwo na zamani ta kuma rika samo mana rahotannin irin taimakon da kasar Amurka ke yi wa Najeriya ta wannan fanni don hakan yana daga cikin hanyoyin da ya kamata a bi don habaka tattalin arzikin kasar nan.

A siyasance kuma ya kamata ta samar da wani shafi wanda zai mayar da hankali a kan siyasar Najeriya kai-tsaye. Sannnan a rika ba masu ruwa-da-tsaki da kwararru da kuma talakawa dama don tofa albarkacin bakinsu. Yin hakan zai taimaka wajen habaka siyasar kasar nan.

Kamal Abdulrahman Dodo Malumfashi, ya aiko da wannan sharhi ne daga I-mel:  [email protected]