Mujallar Sahihiya: Da fa sauran rina a kaba

‘Sahihiya’ mujallar Hausa ce da ta fara leko duniya a wajajen 2008. Ta ci gaba da haskawa kafin daga baya ta shiga duhu, aka daina jin amonta.Haka al’amarin ya kasance ga wasu mujallun Hausa masu yawa da suka yi rayuwa a cikin tarihin adabi. Wasu mujallaun da suka yi doguwar suma kamar ‘Zuma,’ ‘Gagarau,’ ‘Tamola,’ […]

Mujallar Sahihiya: Da fa sauran rina a kaba

‘Sahihiya’ mujallar Hausa ce da ta fara leko duniya a wajajen 2008. Ta ci gaba da haskawa kafin daga baya ta shiga duhu, aka daina jin amonta.
Haka al’amarin ya kasance ga wasu mujallun Hausa masu yawa da suka yi rayuwa a cikin tarihin adabi. Wasu mujallaun da suka yi doguwar suma kamar ‘Zuma,’ ‘Gagarau,’ ‘Tamola,’ ‘Garkuwa,’ ‘Taskar kwallo’ da sauransu, abu kamar wasa sai ba a kuma jin su ba kuma ga alamu ba tunanin dawowar su. Wannan yanayi ya sa an sami gibi a wannan bangare na rubuce-rubucen Hausa da kuma hasarar wasu labarai da muhimman filaye na wadannan mujallu.
Babban abin farin ciki ne ganin dawowar mujallar ‘Sahihiya’ a fagen dab’i, domin ci gaba da kawo wa al’umma labarai da kuma cike wani gibi da aka taba samu dalilin rashin ta. Hakika wannan abin murna ne da kuma farin ciki.

Abubuwan da mujallar ya kamata ta kula das u:
Ta wata fuska kuma, akwai bukatar mujallar ta kula da wasu muhimman abubuwa da ke bukatar a kiyaye da su. Su wadannan abubuwa sun kasance muhimman matakai na kyautata lamarin ci gaba da fitowar mujallar da kuma biyan bukatar masu karantawa. Kiyaye wadannan abubuwa zai taimaka ainun ga rufe wata kafa da za ta sa mujallar ta yi hasarar masu karatu, wanda haka zai iya jan ragamar mai da ita gidan jiya; abin da ba a fata.
Abu na farko shi ne ka’idojin rubutu. Su ka’idojin rubutu su ne hukunce-hukuncen rubutun Hausa wadanda malamai suka shata domin kyautata rubutun Hausa. Shi rubutun Hausa yana tafiya ne bisa wasu ka’idojin da suke daidaita shi, su sa sakon marubuci ya isa ga mai karatu cikin sauki. Duk rubutun Hausa da aka yi ba bisa ka’idojin da masana suka shata ba, zai kasance ba tsari kuma sakon cikinsa ba zai isa ga mai karatu cikin sauki ba. Daga cikin ka’idojin akwai hade kalma da raba ta inda ya dace. Akwai sanya alamomin rubutu inda suka dace. Akwai sanya kugiya ga bakake masu kugiya kamar /k/ /b/ /’y/ /d/ da sauransu. Akwai kula da amfani da babban baki da karami da sauransu. Dukkan wadannan ka’idojin rubutu matsayinsu a rubutun Hausa daya yake da matsayin gishiri cikin miya.
Idan aka dubi sabbin fitowar wannan mujalla za a ga cewa, akwai matsalolin ka’idojin rubutu masu yawa a cikinsu. Dubi fitowar baya-bayan nan, wato fitowa ta hudu. dauki labari mai take ‘Rahoto na musamman wa ya saki Mejo Hamza Al’mustapha?’ da ke shafi na 24. Irin wannan matsala ta sa karanta shi yake da wahala. Ga sakin layi na farko kawai.
Yadda aka kawo Shi:
“Hausawa kance kome nisan jifa kasa tayi. wannan haka yake, domin har n ya tunatar dani da yawan shekaru sha biyar da tsohon dogarin marigayi Janar Sani Abacha, ya kwashe tsare, bisa ga zarginsa da hannu akan kisan Kuduratu MKO Abewala, wato Mejo Hamza Al,Mustapha, wanda aka dauki matakai iri-iri, domin ganin an halakashi,amma a cikin iyawar Allah ya tsar da shi.”
Yadda ya dace:
“Hausawa kan ce, ‘Komai nisan jifa kasa ta yi.’ Wannan haka yake domin har ya tunatar da ni da yawan shekaru sha biyar da tsohon dogarin marigayi Janar Sani Abacha ya kwashe tsare bisa ga zargin sa da hannu
a kan kisan Kuduratu MKO Abiyola, wato Mejo Hamza AlMustapha wanda aka dauki matakai iri-iri domin ganin an halaka shi, amma a cikin iyawar Allah ya tserar da shi.”

A kula da zaben kalmomi:
Abu na biyu shi ne, zaben kalmomin jan hankalin mai karatu. Sanin kowane Bahaushe ne cewa, harshen Hausa harshe ne da Allah Ya yi wa albarkar dimbin kalmomin isar da sako. Ire-iren wadannan kalmomi na
bukatar zabe wajen amfani da su don isar da sako ko a magance ko kuma a rubuce. Idan aka yi rashin sa’a a wajen zaben kalmomi, sai manufa ta canza daga abin da ake nufi zuwa wani abu daban.
Ga misali: ‘Ubanka-mahaifinka. Uwarka-mahaifiyarka.’ Ba shakka, kalmar ubanka da uwarka sun fi kusa ga zagi. Mahaifinka da mahaifiyarka sun fi kusa ga girmamawa. Idan aka duba za a ga kalmomin ai suna da ma’ana makusanciya ko iri daya amma manufarsu ta bambanta. Wannan ya nuna sai an kula, an yi zabe a wajen isar da manufa ga mai saurare ko rubutu.
A wannan fitowar mujallar Sahihiya ta hudu, akwai irin wannan matsala ta rashin kula da zaben kalmomi don isar da manufa. Dubi shafi na 12 a labarin ‘Babban Labari Wa Ke Tsoron A Raba Najeriya?’ A tsakiyar shafin an sa hoton wani mutum. Daga kasan fuskar mutumin aka rubuta ‘Mujahid Dokubo Asari.’ Maganganun da wannan mujallar ta nuna mutumin ya yi a tsakanin shafinta na 12-13 maganganu ne na Allah wadai kuma masu alaka da ta’addanci don sun fi kusa da rusa tsarin dimokuradiyya da wargaza zaman lafiyar al’umma. Idan haka ne ina dalilin Kalmar ‘Mujahid?’ Mujahid zai yi ire-iren wadannan maganganu? Anya kuwa maganganun sun dace da kalmar idan aka dubi ma’anarta da manufarta da matsayinta a tunanin Bahaushen yau?
Wani abu kuma shi ne rashin tsarin aje labari da hotuna cikin shafukan mujalla. Tsarin labari da hotuna na daya daga cikin muhimman abubuwan da ke kara wa mujalla kwarjini da farin jini ga masu karatu. Wasu masu karantun labari tun karon farko sukan dubi yadda aka tsara komai na cikin mujalla kafin shiga cikin ainihin labaranta. Akwai masu karatun da abu na farko da suke yi shi ne duba shafin kumshiya ko abubuwan da ke cikin mujalla. Tun a wannan shafi za su ga labarin da suke sha’awar karantawa. Wani lokaci, suna ko taken da aka ba labari da hoton da ke tare da taken suke jan hankalin wani. Idan aka rasa dacewar tsarin sai a wayi gari ba a sha’awar karanta mujallar.
A cikin wannan fitowa ta 4, tun a shafin farko (Abubuwan Dake Ciki) aka yamutsa daidaitacce kuma sanannen tsarin kidar lambobin Bahaushe. An fara da 12, 23, 22, 18, 27, 3, 6, 17, 20, 29. Mene ne abin wahalar da mai karatu? A yi amfani da sanannen tsari mana; daga karamar lamba zuwa babba mana! 3, 6, 12, 17, 18,  20, 22, 23, 27, 29.

Wasu kura-kuren mujallar:
Ta fuskar yadda aka aje hotunan fitowar ma akwai matsala. Hoton Sardauna da aka sa a lamba ta 27 a tsarin ‘Abubuwan Dake Ciki’ bai dace da wurin ba. Idan aka duba shafin (a can cikin mujallar) za a ga ba
wani dalili na sa hoton. Mai hoton (Sardauna) ba inda aka shigo da shi cikin ainihin labarin. Mai dunkin telan da aka rubuta sunan mai hoton kasansa, mai karatu bai san ko shi ne Sardauna ba domin ba a ce komai game da shi ba. Inda aka yi amfani da hoton Sir Ahmadu Bello Sardauna, ya kuma dace shi ne shafi na 16 da kuma shafi na 21 amma kuma ba a nuna haka ba a shafin abubuwan da ke ciki.
Yawaitar tallace-tallace na cikin matsalolin da suka kamata mujallar Sahihiya ta kula da su. Ba shakka talla ita ce kashin bayan ci gaban rayuwar yawancin mujallu. Talla daya a mujalla sau da yawa takan cike gibin hasarar da ake yi na rashin sai da kwafenta masu yawa. Duk da wannan garabasa, idan talla ta yi yawa a fitowar mujalla takan dakushe haskenta. Yawaitar talla ke tare filayen wasu labarai masu muhimmanci wadanda mutane ke son karantawa.
Dubi wannan fitowa ta hudu, tallace-tallace da ke cikinta sun yi yawa. Shafukan fitowar 34 kacal idan aka cire bangayenta. 10 daga cikinsu duk talla ce. Ke nan shafuka 24 ne kawai suke kunshe da labarai wadanda su ne jijiyoyin mujalla irin Sahihiya wadda take ta zamantakewa da walwala. Wannan yawaitar talla ya sa babu labarai na kiwon lafiya, ilimi, addini, wasanni da sauransu wadanda suke da muhimmanci kwarai ga al’umma.
Idan aka yi la’akari da bayanan da aka gabatar, za a ga cewa, abubuwan da aka gabatar ba su ne iyakar abubuwan da ke bukatar kulawa ba. Haka kuma ba an kawo wadannan bayanai ne don tsokana ko rainawa ba. Ana sane ba wani mutum da ya isa ya yi rubutu har kuma ya tsira daga kowane kure domin kowane mutum dan tara ne, bai cika dan goma ba.

Dalilin sharhin nan:
An yi haka ne don ba da gudummuwa ga ci gaba da dorewar Mujallar Sahihiya. Yin haka kuwa yana da muhimmanci don sanin kowa ne, aikin buga mujalla aiki ne ja kuma babba da ke bukatar sa hannun  mutane.
Kashin baki sai taro! Hannu daya ba ya daukar jinka! Haka wannan yana nuna ana karanta mujallar kuma ana biye da ita don sha’awa da kauna.
Ina fatar wannan rubutu ya kasance makamin ci gaban mujallar Sahihiya da ma sauran mujallun Hausa, domin mu gudu tare, mu tsira tare!
Malam Bunza, malami ne a Sashen Koyar Da Harsunan Najeriya, Jami’ar Usmanu danfodiyo, Sakkwato, 07063532532, [email protected]