Mujallar Tozali ta karrama ’yan fim
Mujallar Tozali da aka kirkiro don ilimantar da mata ta karrama ’yan fim da ’yan siyasa .An gudanar da bikin karramawar ne a dakin taro na International Conference Centre da ke Abuja a kwanakin baya.A cikin ’yan fim din da mujallar ta karrama akwai jarumi Zaharaddeen Sani a matsayin Gwarzon Jarumin mujallar na shekarar 2014 […]
Mujallar Tozali da aka kirkiro don ilimantar da mata ta karrama ’yan fim da ’yan siyasa .
An gudanar da bikin karramawar ne a dakin taro na International Conference Centre da ke Abuja a kwanakin baya.
A cikin ’yan fim din da mujallar ta karrama akwai jarumi Zaharaddeen Sani a matsayin Gwarzon Jarumin mujallar na shekarar 2014 da kuma Fati Washa a matsayin Gwarzuwar Jarumar mujallar ta shekarar 2014.
’Yan fim din da suka halarci bikin sun hada da Yakubu Muhammad da ST Mima da Al-Amin Ciroma da sauransu.
A cikin ’yan siyasar da aka karrama akwai Gwamnan Jihar Gombe a matsayin gwamnan da ya fi aiki tsawon shekara 3 da Gwamnan Jihar Akwa Ibom a matsayin gwamnan da ya fi kwazo tsawon shekara 7.
Gwamnan Jihar Kano Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso shi ne Gwarzon Gwamnonin Najeriya na shekarar 2014.
Mujallar ta karrama matar Mataimakin Shugaban kasa Hajiya Amina Namadi Sambo da tsohuwar Ministar Ilimi Farfesa Rukayya Alkali da ’yan Majalisar Tarayya Dogara Yakubu da Tukur Elsudi da sauransu.
Wannan shi ne karo na uku da Mujallar take karrama ’yan fim da ’yan siyasa da sauran jama’a tsawon shekara 6.
Taken bikin karramawar shi ne: ‘Henna Ball and Award Night’.
Babbar Editar Mujallar Tozali Maimuna Y Abubakar ta ce, ta kirkiro wannan bikin karramawar ne don cusa wa ’yan fim da ’yan siyasa da sauran jama’a karsashin tsayawa kai da fata wajen gudanar da ayyukansu.