Mukabala: Yau za a yi ta ta kare tsakanin Sheik Abduljabbar da malaman Kano
Za a gudanar da mukabalar ne a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano.
Masu iya magana kan ce rana ba ta karya, daga karshe dai ranar da gwamnatin Jihar Kano ta saka domin gudanar da mukabala tsakanin Sheik Abduljabbar Nasiru Kabara da malaman Kano ta zo.
An shirya gudanar da mukabalar ne ranar Asabar, 10 ga watan Yulin 2021 a harabar Ma’aikatar Shari’a ta Jihar da misalin karfe 8:30 na safe.
- A fara duban watan Zul-Hijja daga ranar Asabar – Fadar Sarkin Musulmi
- Bayan shafe mako 4 a tsare, ’yan bindiga sun sako daliban Kwalejin Zariya
A baya dai an shirya gudanar da ita ne a Fadar Sarkin Kano kuma za a watsa ta kai tsaye ta kafafen watsa labarai da sauran kafofin sadarwa na zamani, kafin daga bisani wani hukuncin kotu ya dakatar da ita, kasa da sa’o’i 24 kafin lokacin da aka tsara yi.
‘Ba za a watsa kai tsaye ta kafafen watsa labarai ba’
To sai dai yayin tattaunawarsa da wakilin Aminiya, Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Kano wanda kuma ma’aikatarsa ce ke da alhakin tantance ’yan jaridar da za su dauki rahoto a wurin, Malam Muhammad Garba ya ce sabanin a baya, wannan karon sun yanke shawarar ba za a watsa mukabalar kai tsaye ba.
Bugu da kari, Aminiya ta kuma gano cewa wadanda aka ba shaidar gaiyata ne kawai za a bari su shiga wajen saboda takaita yawan jama’a.
Hatta ’yan jaridar da aka tantance za su shiga wurin ma Aminiya ta gano ba su da yawa.
Tuni dai Sheik Abduljabbar ya ce ya shirya tsaf domin halartar mukabalar tare da bajekolin hujjojinsa a wurin.
Ita kuwa a nata bangaren, Gwamnatin Jihar Kano ta bakin Kwamishinan Al’amuran Addinai na Jihar, Dokta Muhammad Tahar Adam (Baba Impossible) ta ce ta shirya tsaf domin tabbatar da cewa mukabalar ta gudana kamar yadda aka tsara ba tare da kowacce irin tangarda ba.
Baba Impossible ya ce tuni suka aikewa malamin da ma dukkan sauran malaman da za su fafata da kuma wadanda za su yi alkalanci a wurin goron gayyata.
Tun a ranar 4 ga watan Fabrairun 2021 gwamnatin Jihar Kano ta rufe masallacin Sheikh Abduljabbar tare da hana shi yin wa’azi bisa zargin yin batanci ga Sahabban Manzon Allah (S.A.W) a karatunsa.
Malamai da dama daga Kano da kewaye sun yi raddi a kan salon koyarwar malamin, inda suke ce ya saba da tsarin yadda ake koyarwa.
Sheikh Abduljabbar, wanda dan Darikar Kadiriyya ne, na sukar wasu Sahabbai da zarginsu da kirkirar Hadisai na karya suna dangantawa ga Manzon Allah (SAW); yana kiran mabiyansa da su yi watsi da Hadisan.
Mukabalar dai na jan hankalin mutane da dama a ciki da wajen Jihar.