Mukalar da ta sa aka yi wa jami’in watsa labarai ritayar dole

Wata mukala mai taken: ‘Ngozi Okonjo-Iweala da Sarkakiya a Nada Mukamai’ wadda kwararren dan jarida kuma jami’in watsa labarai a ma’aikatar Gwamnatin Tarayya, Malam Yusha’u A. Shuaib ya rubuta ta tada kura a watannin baya. A sanadiyyarta, aka yi wa marubucinta ritayar dole, a sakamakon zargin cewa Ministar Kudi, Ngozi Okonjo-Iweala ce ta sanya aka […]

Mukalar da ta sa aka yi wa jami’in watsa labarai ritayar dole

Misis Ngozi Okonjo-Iweala

Babban dan jarida, Malam Yusha’u A. Shu’aibWata mukala mai taken: ‘Ngozi Okonjo-Iweala da Sarkakiya a Nada Mukamai’ wadda kwararren dan jarida kuma jami’in watsa labarai a ma’aikatar Gwamnatin Tarayya, Malam Yusha’u A. Shuaib ya rubuta ta tada kura a watannin baya. A sanadiyyarta, aka yi wa marubucinta ritayar dole, a sakamakon zargin cewa Ministar Kudi, Ngozi Okonjo-Iweala ce ta sanya aka yi masa ritayar. A nan, ga mukalar nan, domin mu nazarce ta:
“Har yanzu ina mamakin yadda Ministar Sha’anin Tattalin Arziki, da har ila yau kuma ita ce Ministar Kudi, Dokta Ngozi Okonjo Iweala ke cikin rikici. Amsa sunan mukamai biyu da take yi ba iya yi ba ne, kamar yadda wasu za su yi tunani. Kasancewarta ta farko da ta hau kan irin wannan mukamin a tarihin Najeriya, za a dauki mukamin nata tamkar na Firaminista, wanda hakan ya ba ta hurumin sanya ido kan harkokin dukkan ma’aikatu, sassan gwamnati da hukumomi. Hakan ya hada da duba ware masu kasafin kudinsu da yadda sukan samar da kudin shiga. Ba shakka ita ce mai mukami mafi tasiri a majalisar zartarwa, in ka debe Shugaba Jonathan da mataimakinsa, Namadi Sambo.
A shekaru goma da suka shude, marubucin wannan mukala na daga cikin wadanda ministar ke burge su, don nasarorin da takan samu da zurfin ilimi da kwarewar aiki a matakin duniya da gudunmawar da ta bayar wajen bunkasar tattalin arzikin Najeriya, kasancewarta mace ta farko da ta taba zama ministar kudi, daga bisani kuma ministar harkokin waje; karkashin Gwamnatin Olushegun Obasanjo a 2003 da 2006. Duk da dai ta bar gwamnati ba shiri saboda wasu dalilan kashin kai amma sannan dai ta bar mukamin da ake ganin ta tabuka abin kirki.
Babban abin da wasunmu ke ganin cancantar aikin Dokta Ngozi Iweala shi ne yadda ta yi tafiya tare da idon gari a ’yan Kudu da Arewa lokacin da take kan mukamin Ministar Kudi daga 2003 zuwa 2006. Ba a taba kushe ta da nuna wariya don bambancin kabila a gagarumar kasar da ke da kabilu da addinai daban-daban. Haka nan ma aka yi wa uban gidanta shaida a wancan lokacin da duk da ’yan matsaloli da yake da su amma dai bai nuna kabilanci ba. Shugaba ne da ba ya kabilanci kuma yana da kishin kasa da amanna da wanzuwar Najeriya.
Wadanda take ba da sunayensu don samun mukamai sun fito ne daga dukkan sassan kasar, har ma da wadanda su ke cikin kwamitinta na tattalin arziki kamar Nasir El-rufa’i da Nuhu Ribadu da Bode Augusto da Dokta Mansur Muktar da Chukwuma Soludo da sauransu.
Nasarorinta ma na da ban sha’awa. Za mu iya tunawa a 2005 ta jagoranci Najeriya wajen tattaunawa da Cibiyar Lamuni ta ‘Paris Club’ wacce ta biya wa Najeriya wani sashen bashin da ake bin  ta da ya kai dala biliyan 12, inda wajen biya aka share wa kasar dala biliyan 18.
Ta tabbatar da adalci a rabon kudi ga jihohi, ta hanyar wallafa yadda ake ba kowa kasafinsa duk wata a wasu zababbun jaridu.
Da wadannan nasarorin, bai zama wani abin mamaki ba da ta samu gagarumin goyon baya daga dukkan ’yan Najeriya , lokacin da Shugaba Jonathan ya sake nada ta a matsayin Ministar Kudi da kuma sanya sunanta a 2012 cikin masu neman mukamin Shugabancin Bankin Duniya. Wani dandalin labarai a yanar gizo ma ya ruwaito cewa wasu malamai Musulmi na addu’a a masallatai don samun nasarar Ngozin. A wancan lokacin, duk an dauka ba ta da kabilanci ga kuma kwarewar aiki.
Ministar Kudi, Ngozi Okonjo-IwealaDalilin wannan rubutun shi ne, domin ankarar da ita ga wasu nade-naden mukamai da ke da sarkakiya, ta hanyar yin illa a siyasance da kuma ta fuskar tattalin arziki. Na yi tsammanin za ta ci gaba da halin kwarai a matsayinta na ministar da ta fi tasiri, ga shi kuma gimbiyar Igbo ce daga yankin Neja-Delta; don kasancewarta ’yar Obi na Ogwashi-Uku  a Jihar Delta.
Kwanan nan kungiyar Hadin Kan Yarabawa (Yoruba Unity Forum) ta yi zargin ana tsame hannayen Yarabawa daga mukaman Gwamnatin Tarayya karkashin mulkin Shugaba Jonathan. Bayan taron kungiyar a Ikenne, Jihar Ogun, Bishop ta Majami’ar Katolika ta Akure (mai  ritaya) Rt. Reberend Bolanle Gbonigi, ta yi zargin gwamnati da gangan take tsame hannayen Yarabawa daga mukaman Gwamnatin Tarayya ba ta hanyar adalci ba. Sun yi kira ga gwamnatin da ta daina wannan matakin da gangan don Yarabawa sun fara kulewa da lamarin gwamnatin. Ba a dade ba daga lokacin da Yarabawa suka yi wannan kukan sai kungiyar ’Yan Majalisar Dattawa Na Arewa ta koka ga yadda ba a adalci wajen dauka da karin girma ga sojoji. Dattawan sun nuna damuwa da yadda suka ce ake nuna rashin adalci da ba ’yan kabilar Igbo fifiko a wannan bangaren, wanda ya saba da tsarin rabon mukamai na kasa.
Ya kamata ta san cewa ’yan Najeriya na tuna bayanan da ta yi a littafin mawallafi Chinua Achebe mai taken ‘Teacher of Light’ inda ta nuna bacin rai ga yadda aka nuna wa kabilarta wariya yayin da bayan yakin basasa. Don haka ake rade-radin tun da yanzu ta shigo gwamnati take kokarin gyara wannan tunanin da take yi, na nuna wariya ga al’ummarta. Wasu ma sun dage cewa abin da take yi yanzu shi ne karfafa ajandar bangaranci da kabilanci da ke da illa ga sauran yankunan Najeriya, ta hanyar murdiya wajen nadin mukamai.
A gaskiya ma dai an ambaci sunanta a baya-bayan nan da hada kai da wata mai babban mukami a gwamnati, don sake nada Misis Aruma Oteh a matsayin Shugabar Hukumar Kasuwar Hannayen Jari duk da zargin badakalar da ake yi mata da ma kira da majalisa ke yi na a tsige ta daga mukaminta. Okonjo Nweala dai ta tsaya kai da fata kan matsayinta da ya sa har yau Oteh ke kan mukaminta daram.
Yayin da muhawara kan Oteh ba ta gama sanyi ba, wata gamayyar matasa karkashin jagorancin dan rajin kare hakkin bani Adama, Shehu Sani, ta kalubalanci dalilan nada sabon Shugaban Hukumar Tara Kudaden Shiga Ta kasa, alhali wani dan Arewa, Kabir Mashi na kan mukamin kuma yana bunkasa hanyoyin samun kudin shigar hukumar. A karkashin Mashi, hukumar ta tara haraji musamman a shekarar kudi ta 2012 da suka kai Naira zambar miliyan dubu biyar, inda ciki Naira zambar miliyan dubu daya da miliyan dari takwas (kashi 36.07 cikin dari) suka fito daga kudaden harajin da ba su shafi man fetur ba.
Za mu karkare a makon gobe