Mukalar da ta sa aka yi wa jami’in watsaa labarai ritayar dole (2)
kungiyar ta nuna kwamitin da ya bincika lamarin Hukumar Tara Kudin Shigar da aka nuna, ba don tabbatar da adalci ne ba, kawai don yana cike ne da dimbin danginta ne ’yan kabilar Igbo. Suka kara da cewa: “Ba mu yi amannar cewa an nuna adalci ba, muna togaciya ga Shugaban kasa da ya guje […]
kungiyar ta nuna kwamitin da ya bincika lamarin Hukumar Tara Kudin Shigar da aka nuna, ba don tabbatar da adalci ne ba, kawai don yana cike ne da dimbin danginta ne ’yan kabilar Igbo. Suka kara da cewa: “Ba mu yi amannar cewa an nuna adalci ba, muna togaciya ga Shugaban kasa da ya guje wa sarayar da hakkin shugabancinsa ga Ministar Kudi.
A zahiri sun zarge ta da nuna kabilanci a yawancin mukaman da ta nada tun dawowar ta kan wannan mukamin. Wasu daga mukaman da suka yi zargin ta nada ’yan uwanta sun hada da Shugaban Hukumar Kula Da Kadarorin Gwamnati, Hukumar Kula Da Kamfanonin Sadarwa (NCC). Kazalika har ma da nada wata mata mai shekaru 40 a matsayin Shugabar Hukumar Fansho Ta kasa.
Mutane na mamakin yadda yakan zamanto ’yan kabilar Igbo ne ke nasara a duk jarabawar daukar aiki mai muhimmanci da ta gudanar, ta hanyar wasu kungiyoyin duniya da ta zaba da kanta don gudanar da jarabawar. Abin da kawai ke nuna adalci a daukar ayyukan shi ne, daukar wasu shugabannin sassa na wucin-gadi da aikinsu na jeka-na-yi-ka ne, ta irin da za su bayar.
Amfani da kalmomin gwada daukar aikin kamar: “Sai mafiya kwakwalwa,” “Sai wadanda suka samu horarwa a ketare,” “Sai kwararru mazauna ketare,” hanya ce da kan hana kwararrun ’yan Najeriya neman irin mukaman da hakan kan gurgunta ci gaban kasa. Nuna cewa wasu mukaman sai kwararru daga wata kabila ne za su iya, ya zama wajibi a gyara wannan tsari.
Da yawa akan samu wadanda suka samu kwarewar a ketare ba su tabuka abin kirki fiye da wadanda suka kware a cikin gida, musamman a lamurra masu tsauri.
Ya zama wajibi Dokta Ngozi ta fahimci cewa daukar kwararru daga kebabbiyar kabila zai jawo wa wadanda aka daukar mummunar kiyayya daga sauran sassa, kamar yadda ya faru a 1960, inda yawancin wadanda aka dauka aiki a matakin Tarayya suka fito daga wata kabila.
Ga irinmu da muka amince da cewa har yanzu ministar na da cancantar aiki, ya zama wajibi ta nesanta kanta daga zargin aiki don cimma burin ’yan Biafara ( masu son raba Najeriya) a wajen nadin mukamai. Mu a zamanin mulkin dimokradiyya ne da bai dace a rika gudanar da lamurra ta hanyar kama-karya na tunanin: “Yanzu ai zamanin mulkinmu ne.”
Don haka nake bukatar ta ta rika tabbatar da cewa ana nada mukaman ne bisa cancantar da za ta gamsar da mizanin al’umma. Na yi amannar cewa sai masu son kasa da alheri ne kawai za su iya fitowa su fadi gaskiya yadda mutane ke dubar yadda lamurra ke gudana a kasar nan.
A wannan makon, ga sababbin Gizagawan da suka samu rijista:
1-Abubakar Muhammad Kwadon Gombe, 08024263082 (GZG632GMB). 2-Ibrahim Kawuji Ahmed Gombe, 08034455567 (GZG633GMB). 3-Sunusi Abdullahi Fagge Kano, 08099526261 (GZG634KNO). 4-Almustapha Kamal bagwai Kano, 08066166966 (GZG635KNO).