Mukamin Minista: Ko ya dace a tantance Buhari a Majalisar Tarayya?

An samu tabbacin cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari shi ne zai kasance Ministan Mai a Najeriya. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace shi ma shugaban ya hallara gaban Majalisar Tarayya kamar sauran ministoci domin a tantance shi? Wakilanmu sun jiwo ta bakin wadansu mutane, kamar haka: Bai dace ya je a […]

Mukamin Minista: Ko ya dace a tantance Buhari a Majalisar Tarayya?
Mukamin Minista: Ko ya dace a tantance Buhari a Majalisar Tarayya?

An samu tabbacin cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari shi ne zai kasance Ministan Mai a Najeriya. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace shi ma shugaban ya hallara gaban Majalisar Tarayya kamar sauran ministoci domin a tantance shi? Wakilanmu sun jiwo ta bakin wadansu mutane, kamar haka:

Bai dace ya je a tantance shi ba – Jafar Madobi

Muhammad Yaba, a Kaduna

Malam Jafaru Madobi: “Gaskiya Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cancanci rike mukamin Ministan Mai saboda haka bai dace a ce wai sai ya je an tantance shi ba, domin shi mutum ne mai adalci da mutane suka yarda da shi. Muna kuma fatan idan har ya samu ministoci na kwarai sai Najeriya ta zama kasa kamar Saudiya a ci gaba.”

Bai kamata a tantance Buhari ba – Hajiya Zinaru

Abbas Ibrahim dalibi, a Legas

Hajiya Zinaru Ibrahim Agege: “A gaskiya bai kamata Shugaba Buhari ya gurfana a majalisa a tantance shi ba, domin ai shi tuni ’yan Najeriya suka tantance shi kuma duniya ta shaida haka kuma mu mun san ba mu yi zaben tumun dare ba. Domin ya yi a da an gani kuma a yanzu ma yana kan yi. Don haka kalubale ne ga masu son ya gurfana a gabansu da su yi koyi da shi, su bayyana wa duniya abin da suka mallaka, har in ya zama lallai ya gurfana sai ya yi domin durkusa wa wada ba gajiyawa ba ne.”

kaskanci ne Buhari ya je majalisa don a tantance shi – Alhaji Hamza Darda’u

Ahmed Garba Mohammed, a Kaduna

Alhaji Hamza Darda’u: “Lallai a kan wannan batu na neman majalisa ta tantance Shugaban kasa Muhammadu Buhari a neman ya zama Ministan man fetur, to hakan sam bai dace ba.  Hasali ma kaskanci ne a ce Buhari wai ya tafi Majalisar Dattawa don ta tantance shi kafin ya rike mukamin Ministan man fetur kamar yadda aka yi wa sauran ministoci. Tun da an sha yin irin haka, Obasanjo da shi kansa Jonathan sun rike Ministoci daban-daban amma ba su je majalisa don a tantance su ba kafin su rike mukaman.  Don haka ban ga dalilin da zai sa a ce sai Buhari ya tafi majalisa an tantance shi kamar sauran ministocin da ya gabatarwa majalisa don a tantance su kafin ya zama Ministan fetur ba.”

Bai kamata ya je ba – Ahmad Tijjani

Muhammad Yaba, a Kaduna

Ahmad Tijjani Suleiman: “Shugaban kasa Muhammad Buhari ya fi karfin ya je majalisa domin a tantance shi saboda ya ce zai rike matsayin Ministan man fetur. Domin dokar tsarin mulkin kasar nan ta ba shi kariya shi da mataimakinsa, cewa a matsayinsa na Shugaban kasa doka ta amince masa ya rike ma’aikatu uku ma ba daya ba. Saboda haka ’yan majalisa su je su nemi tsarin dokar kasa domin haka muka ji ta ce.”

Bai dace Buhari ya je majalisa don a tantance shi ba      – Abdullahi Muhammad

Ahmed Garba Mohammed, a Kaduna

Abdullahi Muhammad: “Watau ita dokar kasarmu Najeriya ce ta tsara hanyoyin da suka kamata a bi wajen zaben ministoci kuma babu inda aka nuna cewa idan Shugaban kasa yana da sha’awar rike kowace irin ma’aikata sai ya gurfana a gaban majalisar kasa ta tantance shi.  Ai shi ba mukamin minista yake rike da shi ba, shi Shugaban kasa ne kuma yana da damar ya rike kowace irin maa’ikata da ke karkashinsa idan yana da bukatar yin haka. Don haka maganar ko ya dace ya gurfana a gaban Majalisar Dattijai don su wanke shi ai ba ta ma taso ba.  Don haka ra’ayina shi ne, babu dalilin da zai sa Shugaba Muhammadu Buhari ya gurfana a gaban majalisa don a tantance shi kafin ya zama ministan da zai kula da harkokin fetur. Alal misali an taba samun irin haka a zamanin shugabancin Olusegun Obasanjo da kuma marigayi Umaru Musa ’Yar’aduwa kuma ba su je majalisa don a tantance su ba.”

Bai dace a tantance Buhari ba  – Mukhtar Gambo

Abbas Ibrahim dalibi, a Abekuta

Alhaji Munkhtar Gambo Ali K/Mata: “Bai dace ba dari-bisa-dari Shugaba Buhari ya gurfana a gaban majalisa domin a tantance shi ba. Domin abin da dai ake bukata shi ne cancanta. To ai shi daman can ya cancanta saboda ba a Najeriya kadai ba har ma a duniya an yarda da shi ya kuma sami kyakyawar shaida, ya kuma zama shugaban da a duniya ma ya kamata a yi koyi da shi saboda gaskiyarsa da rikon amanarsa. Ga shi uwa uba ma ya bayyana wa duniya kadarorinsa, to me ake bukatar a sani?”