Mulkin Buhari zai kawo wa Najeriya gagarumar ci gaba – Jabbi Shagari

Shugaban karamar Hukumar Shagari kuma shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomin Jihar Sakkwato Alhaji Muhammad Jabbi Shagari ya ce mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kawo wa kasar nan gagarumin ci gaba da kuma hadin kai mai dorewa.Alhaji Jabbi Shagari ya bayyanan haka ne lokacin da yake ganawa da wakilinmu a Sakkwato, inda ya ce za […]

Mulkin Buhari zai kawo wa Najeriya gagarumar ci gaba – Jabbi Shagari
Mulkin Buhari zai kawo wa Najeriya gagarumar ci gaba – Jabbi Shagari

Shugaban karamar Hukumar Shagari kuma shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomin Jihar Sakkwato Alhaji Muhammad Jabbi Shagari ya ce mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kawo wa kasar nan gagarumin ci gaba da kuma hadin kai mai dorewa.
Alhaji Jabbi Shagari ya bayyanan haka ne lokacin da yake ganawa da wakilinmu a Sakkwato, inda ya ce za a samu haka ne saboda tausayin jama’a da Buhari yake da shi, musamman idan aka lura da yadda ya ba da umurnin a fitar da makudan kudi don biyan jihohi da kananan hukumomi bashin da suke bin Gwamnatin Tarayya domin a ceto su daga halin matsi da karyewar tattalin arziki da ya sanya wasu jihohin kasa biyan albashi.
Shugaban ya ce Shugaba Buhari zai daga martabar kasar nan ta sake zama jagora a Afirka,
“Gaskiya wannan hobbasa da ya yi zai kara hadin kai da son juna a tsakanin mutanen kasar nan domin albashi jigo ne na rayuwar ma’aikaci, kuma za mu tabbatar an yi amfani da kudin yadda ya kamata a kowace karamar hukumar Sakkwato, don hakan zai kara mana ci gaba duk da ba mu taba shiga halin rashin biyan albashi ba a baya,” inji shi.
Ya yaba wa Gwamna Aminu Tambuwal kan kokarinsa na ganin an samu walwala da kwanciyar hankali a jihar. Kuma ya roki kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta jihar ta taimaka musu da hadin kai don ciyar da jihar gaba. Ya ce a shirye suke su karbi gyara ko korafi don su zabin jama’a ne kuma su ake yi wa aiki.