Mulkin Jihar Kaduna: kalubalen da ke gaban Gwamna Mukhtar Yero

Mun samu wannan sako daga alkalamin Aliyu S. Usman Rigachikun, No. AC 26, danmasani Bello Sani Road, Rigachikun-Kaduna (08093349542):A yau ina son in ba Gwamna Muktar Yero wasu shawarwari a kan aikin da ke gabansa na shugabancin jihar Kaduna.Shugabanci mahimmin abu ne, shi ya sa duk wata al’umma da ka ga ta ci gaba, ko […]

Mulkin Jihar Kaduna: kalubalen da ke gaban Gwamna Mukhtar Yero
Mulkin Jihar Kaduna: kalubalen da ke gaban Gwamna Mukhtar Yero

Mun samu wannan sako daga alkalamin Aliyu S. Usman Rigachikun, No. AC 26, danmasani Bello Sani Road, Rigachikun-Kaduna (08093349542):
A yau ina son in ba Gwamna Muktar Yero wasu shawarwari a kan aikin da ke gabansa na shugabancin jihar Kaduna.
Shugabanci mahimmin abu ne, shi ya sa duk wata al’umma da ka ga ta ci gaba, ko ta samu ci baya, duk ya ta’allaka ne da shuwagabannin da suka mulke ta. Shi ya sa saboda mahimmancin wannan shugabanci, mu ka ga misali daga sahabban Annabi Muhammadu (SAW). Lokacin da ya rasu, ba su rufe shi ba sai da ya dauki wani lokaci, suna can suna tattauna wa zai shugabance su? Ba su aikata haka ba sai don sun san rayuwar al’umma mai neman ci gaba sai da shugaba nakwarai. Shi ya sa wani malami ya ce, muhimmancin siyasa ya fi Sallah. Hakika, in ka kalli abin da sahabbai suka aikata a kan wa zai shugabance su; za ka hango maganar malamin gaskiya ce.
An yi gwamnoni a Jihar Kaduna, tun daga sojoji da farar hula, wasu a raye wasu sun mace. A yau ba abin da ya rage wa al’ummar jihar sai tuna su da alhairan ko sharrin da suka aikata. To, kai ma Gwamna Mukhtar Yero, dole sai ka kasance daya daga cikin abin da za a tuna da kai, ko alherinka ko rashin kirkinka. In ko haka ne, ya kamata ka ba mara da kunya, domin kuwa ban taba ganin wani gwamna a jihar nan da wayau na ba da ya hau mulki, al’ummarsa ke yi masa fatan alheri kamar kai ba. Sa’annan ya kamata ka fitar da mutanen birnin Zariya kunya. Kai ne Gwamna na farko da ya fito daga cikin birnin, sauran duk ’yan wajen birnin Zariya ne. Hausawa dai sun ce, da na gaba ake gwada zurfin ruwa.”
Gwamna, kana da kalubale a kan ilimi. Hakika na je Katsina na ga yadda Marigayi Umaru Musa ya gyara makarantu, musammam na firamare. Ya kamata a ce an yi irinsu a nan. In son samu ne, kai ka wuce nan zuwa manyan makarant, don ka kawo wani irin ci gaban da ko ba ka za a tuna da kai. Kalli dai Gwamna Makarfi, ko ba komai za a tuna da shi a Jami’ar Jihar Kaduna da ya samar. Kana da kalubale ta bangaren hanyoyin cikin gari. Ya kamata a ce an samu karin hanyoyi masu kyau da kayatarwa, irin wadanda na gani a Kano. Ya kamata a ce tun daga Kawo har zuwa mahadar Kwaman (Command Junction), a fadada titunan yadda motoci uku za su wuce a lokaci guda, zuwa da dawowa. Yanzu ka duba Kawo, titin Zariya, ba magudanun ruwa masu kyau, in an yi ruwa kwanciya yake yi. Hakika hakan bai dace da matsayin garin Kaduna ba, garin Sardauna da manyan mutane. Garin da yai suna sosai a ciki da wajen Najeriya. Har kirari ko take ake yi wa garin – ‘Kaduna Garin Gwamna’ ko ‘Daga Duniya Sai Kaduna’ ko ‘Kaduna Kan Duniya.’ Amma a ce ba wasu kayatattun hanyoyi sai irin wadanda aka gada da dadewa.
Haka kuma ya kamata a ce an mayar da Titin Yakubu Gawon tagwaye. Titi ne na hada-hadar jama’a da ababen hawa. Ko gidan Rediyon Tarayya na Kaduna a wannan titi yake. Haka titi mai sunan Janar Muammadu Buhari, ya kamata a ce an mayar da shi tagwaye. Haka daga shataletalen kasuwar reliwe, titin da ya nufi Barnawa; ya kamata a mayar da shi tagwaye. Don hakika da safe in za ka fito Barnawa ko da yamma za ka shiga anguwar sai hankalinka ya tashi saboda cinkosan ababen hawa. Haka titin da ya tashi daga Bakin-Ruwa ya ratsa Rigasa, a mayar da shi tagwaye ba gyra kawai ba. Yana da wuya a Najeriya ka samu anguwa mai ci gaba irin Rigasa. Ga yawan jama’a da ababen hawa, musammam da yamma in ’yan kasuwa za su koma gidajensu. Kai, ba ma wadannan hanyoyi da na ambata ba, akwai hanyoyi masu yawa a Kaduna da ya kamata a ce an mayar da su tagyaye. Yanzu ko ba komai za a tuna da Gwamna Yakowa da ya yi hanyar Kamazo da Gwamna Makarfi da ya mayar da titin zuwa Mando tagwaye daga Kawo zuwa babban shataletalen nan. Haka nan za a dinga tunawa da Makarfi saboda gadar sama da ya yi. Hakika a yanzu haka garin Kaduna na bukatar gadojin sama masu yawa kamar irin wadanda na gani a Kano a na yinsu. Hatta kofofi, ya kamata a ce Gwamna Muktar Yero ya yi wa garin Kaduna kamar yadda Zariya da wasu garuruwa ke da su. Batun hanyoyi ba garin Kaduna ya tsaya ba, har Zariya da Kafanchan da sauran kananan hukumomi.
Gwamna, kana da kalubale a kan farfado da masana’antu na Gwamnatin Jiha da suka durkushe. Kamar masana’antar yin sirinji a Zariya da ta sarrafa tumatir a Ikara da ta citta a Kachiya. Haka sauran masana’antu da suka durkushe ta dalilin rashin wutar lantarki da wasu dalilan. Ya kamata a ce gwamnati ta ba da himma wajen ganin ci gaba da rayuwarsu. Yanzu kalli masakar UNTL ta durkushe, masakar da dinbin jama’a ke cin abinci ta dalilinta, masakar da a nahiyar Afirka Ta Yamma ba kamarta. Wannan ba karamin ci baya ba ne a kasarmu da jaharmu. Ya kamata Gwamna ka yi himma kwarai ganin an farfado da wadannan masana’antu. Yanzu al’umma ba za su mance da Yakowa ba, irin yadda a lokacinsa aka samu masana’antar yin Indomie ta farko a Arewacin Najeriya (Nothern Noodles Limited).
Gwamna, kana da kalubale a kan aikin gona da kasuwanci. Yana da kyau ka kawo hanyar ci gabansu. Ya kamata a samar da isasshen takin zamani, musamman a inganta hanyar raba takin. Da yawa takin bai kai wa ga manoma talakawa sai ’yan kasuwa da ’yan siyasa. Haka kasuwanci a garin Kaduna, yana da kyau a ce an samu gagarumin ci gaba. Kamar kasuwar Sheik Abubakar Gumi, ita ce babbar kasuwa a garin Kaduna. Yana da kyau a ce an hada masu sayar da abu iri daya wuri guda, kamar yadda masu sayar da gwal a kasuwar suke wuri daya. Haka nan yana da kyau a taimaka wa manyan ’yan kasuwa, yadda Kaduna za ta kasance garin da ko’ina ana zuwa sarin kaya, masamman jihohin Arewa da suke kudu da jihar.
Wasu kalubale din su ne kiwon lafiya, yadda Gwamna zai samar da asibitoci da kwararrun likitoci da kayan aiki a Jihar Kaduna. Haka akwai maganar tsaro, musammam kai kanka Gwamna da sauran al’umma, mun san halin da tsaro ke ciki a Arewacin Najeriya. Haka akwai samar da ruwan fanfo mai tsafta da maganar gyaran ruwan Zariya. Haka nan akwai maganar daidaito wurin daukar ma’aikata a jihar na. Ganin cewa wasu al’umma suna ganin suna da yawa amma an danne su. Haka nan wurin shiga aikin soja, a rika yin daidaito wurin dauka daga kowane shiyyar uku da ake da su a jihar nan. Haka nan akwai samar wa da matasa sana’o’in da za su dogara da kansu da sha’anin wasanni da motsa jiki.
***
Sanarwa: Akwai daurin auren tsohon PRO na Gizagawan Jihar Katsina, Kabir Ibrahim Maisallah 08069823833 da shugabar mata ta Gizagawan Jihar Katsina, Bilkisu Mustapha, wanda za a daura a titin dandume, Sabon Layi Funtuwa Jihar Katsina, a gobe Asabar da misalin karfe 2:00 na rana.
Haka ita ma Bagizagiya A’ishatu S. Aliyu, za a daura nata auren a gobe Asabar da misalin karfe 11:00 na safe, a Gidan Yayan Dudu, Unguwar Yayaji, Kafin Madaki, Ganjuwa L.G.A. Jihar Bauchi.
Shi kuwa sabon shugaban Gizagawan Abuja, Musa Aliyu Na-Musamman 08031970000, ya samu karuwar haihuwar da namiji a makon day a gabata.
A yayin da Alhaji Safiyanu Usman Kwali 08065292374, Shugaban Joint Islamic Aid Group Abuja kuma Darakta na Fityanul Islam na Abuja, ya samu karuwar da namiji a makon da ya gabata.
Bagizage Abdullahi Ibrahim Kogi (GZG525KOG) 07065170188, shi ma za a daura aurensa a jibi Lahadi, a garin Jogana na karamar Hukumar Gezawa Jihar Kano.
Muna yi wa dukkan Gizagawan da za su yi aure ko suka samu karuwar haihuwa addu’ar alheri. Allah Ya dayyaba, Ya sa albarka a cikin zuri’a, amin. – GZG.
A labarin jajantawa kuwa, Sakataren Gizagawan Abuja, Sani Umar Zubairu (GZG011ABJ) 08036589834, mahaifinsa na kwance a Asibitin Gwagwalada ba lafiya.
A yayin da Sawailu Muhammad Gwari (GZG115NSR) 08067809783, zababben Shugaban Gazagawan Jihar Nasarawa, mahaifinsa ya rasu a makon da ya gabata.
Muna rokon Allah, dukkan wadanda ke fama da rashin lafiya, Allah Ya ba su lafiya, mu kuma ya kare mu da ingantattar lafiya. Wadanda suka riga mu gidan gaskiya, Allah Ya yafe musu, mu kuma da muka rage, Allah Ya ba mu ikon cikawa da ingantaccen imani, idan lokacinmu ya zo. Amin! – Gizago.