Mulkin Jihar Kano da kalubalen da ke ciki

To dai yanzu Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya jefar da kwallon mangwaro.

Mulkin Jihar Kano da kalubalen da ke ciki

Fadar Gwamnatin Kano

Gaskiya mulkin Kano sai mai kwazo da hakuri da hangen nesa, wanda ba zai yi sako-sako da ingarmar dokinsa ba.

Mutane da dama a Jihar Kano sukan rasa gane mece ce gwamnati kuma kadan daga wadanda suke da masaniya, suna bi son zuciyoyinsu ko don ba su samu biyan bukatunsu ba!

Wannan kan ba su damar shiga layin masu sukar gwamnati har wasu su daura muguwar tsana a kan gwamnan da ke rike da ingarmar mulkin jiha mai albarka wato Kano.

Idan ka bi a hankali za ka iske cewa babu wani gwamna da ya mulki Kanon Dabo ba tare da tsangwama ba.

Na san Gwamnan Kano na farko shi ne Marigayi Alhaji Audu Bako, kuma na ga ire-iren abubuwan alherin da ya yi wa Kano, inda lokacin ne aka mayar da ita jiha cikin jihohi goma sha biyu da aka kirkiro su a 1967, ‘yan shekaru kadan kafin fara yakin Basasa.

Alhaji Audu Bako ya yi rawar gani, ganin yadda ya kawo ci gaban Kano ta kowane fanni, kususan noma da kiwo da kuma kasuwanci na zamani. Kusan lokacinsa ne masana’antu suka yawaita, harkar ilimi ta inganta.

Ya gina dam kusan goma sha shida (16) domin Kano ta samu sukunin samun ruwa, kususan don noman rani.

Dubi dai yau Kura, Dambatta, Karaye, Bunkure, Rano da dai sauransu.

Duk da wannan wasu mutane sun kasance makiya ga wannan bawan Allah, Allahu Akbar ka ji dai duniya Malam!

Hakazalika, gwamnan farko na farar hula, Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi ya kwatanta duk wani abu da Audu Bako ya yi kokarin yi, kuma har gobe akwai ayyukan da Gwamna Rimi ya yi a Jihar Kano.

Duk da haka shi ma ya sha suka. To Malam ka ga ashe ba wai a kan Ibrahim Shekarau ko Gwamna Ganduje wannan tsana ta fara ba, Allah cikin ikonSa Ya ba wa Kanawa kasa mai kyau kwarai da gaske ga kuma albarka, sai dai kyashi da rashin fahimtar duniya sai Kano ta kasance wurin cin mutuncin masu mutunci har samari suka ara suka kuma yafa bayan ma ba su tsaya sun ankara da yadda rayuwarsu za ta kasance ba!

Ko da kasuwa ka shiga zancen dai daya ne, na daga zagin shugabanni bayan ba haka abin ya kasance ba.

Cikin kasuwa maimakon shi dan kasuwa ya ji da abin da ke gabansa na ganin ya samu halal cikin abin da Allah Ya hore masa sai ya hango sama wacce ta yi wa yaro nisa.

Malam bari ka ji, shi ba a samun gwamna da ya juri cin mutunci kamar Gwamna Ganduje ba, domin irin cin kashin da aka yi masa a gidajen rediyo kuma abin mamaki daga karshe har wadanda suka mori gwamnati a shekara takwas da ta yi mulki a Kanon Dabo, akwai wani sakaran bawa da ya juya baya yana caccakar Gwamna Ganduje saboda an samu sauyin gwamnati.

To dai yanzu Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya jefar da kwallon mangwaro ya huta da kuda saura me?

Bari mu ga yadda za ta kaya da gwamnati mai ci. Shin za ta amince da waccan dabara da ‘yan adawa suke kalubalantar gwamnati a gidajen rediyo?

Daga naku: Kwamrade Ibrahim Abdu Zango, Chairman: Kano Unity Forum. Najeriya, 08175472298.

Tags