Mulkin soja ba shi da amfani

Sojoji ne sanadiyyar duk halin da muke ciki a yanzu, shi yasa ake ganin Soja da PDP da Shuga Jonathan duk sun kasa. ‘Yan majalisun Tarayya da Hukumar shari’a sun kasa; ga tsofaffin shugabannin kasa su bakwai (7) da ake da su yanzu sun kasa; wakilan Arewa sun kasa; Malaman addini da na boko duk […]

Mulkin soja ba shi da amfani
Mulkin soja ba shi da amfani

Sojoji ne sanadiyyar duk halin da muke ciki a yanzu, shi yasa ake ganin Soja da PDP da Shuga Jonathan duk sun kasa. ‘Yan majalisun Tarayya da Hukumar shari’a sun kasa; ga tsofaffin shugabannin kasa su bakwai (7) da ake da su yanzu sun kasa; wakilan Arewa sun kasa; Malaman addini da na boko duk sun kasa; tsofaffin shugabannin Jami’a biyu (2) sun ba mu kunya, dangane da kisan gilla da satar mutane da ta kudin gurbataccen mai har Dala biliyan 49 ($49.8bn+#2.7tril).
Ga wasikar da Obasanjo ya rubuta wa shugaban kasa Jonathan, mai shafi 18, har yanzu babu wadanda suka dauki wani mataki akai. Ya rage ga talakawa masu imani da mutunci idan har akwai su, su fara tunanin yadda magabata suka yaki zalunci, har aka samu ‘yanci da hakki. Tilas Turawa suka bada mulkin kai, a shekarar 1960. Talakawa ne  suke mulki a halin yanzu  daga matakin kananan Hukumomi da Jihohi har izuwa Tarayya.
Maimakon fata da wasu ke yi, sojoji su yi juyin mulki, idan ba gyaran gangar Abzinawa ake fatan gani ba, kamata ya yi kowa ya dawo daga rakiyar sojoji. Kowannen mu ya ba da gudun mawa, gwargwadon iko, har sai mun kori duk azzaluman masu mulki. Iyayenmu ne suka kori Turawa daga mulki, mu muka kori Soja. Babu abin da zai hana mu hadu mu kori miyagun masu mulki talakawa farar hula. Sai dai idan ba da gaske ake ba. Mu fara  tuba ga Allah, mu daina aikata zunubai manya da kanana. Shi ne kadai zai yaye mana duk wata annoba, Ya kuma dora mu a kan makiyan mu, makiya Allah.
Idan kunne yaji, jiki ya tsira! Allah ya hada kawunanmu, ya ba mu iko mu gyara dukkan abin da ya lalace, ameen!!!
Anas Saminu Ja’en Makera, Kano 07033882307.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno