Mummunan hadarin motoci ya kashe mutum 5 a Kalaba

Rahotanni na bayyana cewa, an samu mummunan hadarin motoci biyu na karamar motar shiga kirar Audi da kuma kirar Toyota Camry wanda ya sanadiyyar rasuwar mutum biyar nan take. A cewar wani ganau ya ce, hadarin ya faru ne da misalin karfe 2 na tsakar daren yau Laraba a hanyar Marian kafin iyakar Atekong a […]

Mummunan hadarin motoci ya kashe mutum 5 a Kalaba

Rahotanni na bayyana cewa, an samu mummunan hadarin motoci biyu na karamar motar shiga kirar Audi da kuma kirar Toyota Camry wanda ya sanadiyyar rasuwar mutum biyar nan take.

A cewar wani ganau ya ce, hadarin ya faru ne da misalin karfe 2 na tsakar daren yau Laraba a hanyar Marian kafin iyakar Atekong a Kalaba babban birnin jihar Kuros Riba.

Bayan aukuwar hadarin Jami’an ‘yan sandan sun kwashe motocin da suka yi hadarin da gawarwakin mutanen.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar kiyaye hadura ta Najeriya FRSC na jihar Godsgift Uwem ya tabbatar aukuwar lamarin.

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta