Mummunan shugabanci ke jawo rikici a Nasarawa – Dokta Agabi

Dokta Yusuf Agabi yana daya daga cikin ’yan takaran neman kujerar gwamnan Jihar Nasarawa a zaben badi karkashin Jam’iyyar PDP. A tattaunawarsa da wakilinmu a garin Lafiya, dan takarar ya bayyana cewa rikicin da jihar ke fuskanta a yanzu musamman na kabilanci sakamakon mummunan shugabanci ne. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: Wa ne ne […]

Mummunan shugabanci ke jawo rikici a Nasarawa – Dokta Agabi
Mummunan shugabanci ke jawo rikici a Nasarawa – Dokta Agabi

Dokta Yusuf Agabi yana daya daga cikin ’yan takaran neman kujerar gwamnan Jihar Nasarawa a zaben badi karkashin Jam’iyyar PDP. A tattaunawarsa da wakilinmu a garin Lafiya, dan takarar ya bayyana cewa rikicin da jihar ke fuskanta a yanzu musamman na kabilanci sakamakon mummunan shugabanci ne. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Wa ne ne Dokta Yusuf Agabi?
Dokta Agabi: Kamar yadda ka bayyana sunana Alhaji Dokta Yusuf Agabi (Durbin Lafiya). A yanzu ina neman takarar gwamnan jihar nan wato Jihar Nasarawa a karkashin jam’iyyar PDP.
Aminiya: Ya ya zaka bambanta nasarorin da gwamnatinku ta PDP da ta shude ta cimma da na jam’iyyar APC mai ci yanzu jihar nan?
Dokta Agabi: Da farko dai k aga bawai maganar ra’ayi ko domin ni dan jam’iyyar PDP ba ne, duk wanda ya san tarihin jihar nan zai gaya maka cewa gwamnatotin PDP da suka shude wato na Alhaji Abdullahi Adamu da kuma Alhaji Aliyu Akwai Doma ba shakka sun gudanar da ayyukan ci gaba masu daurewa da dama da zai dauki tsawon lokaci kafin wata gwamnati ta iya cimma wadannan nasarori. Yau idan ka lura wasu jihohin kasar nan da aka kirkiro su a lokaci daya da jihar nan, jihar nan ta darasu a bangaren ci gaba da bunkasar tattalin arziki da sauransu duk da cewa kudin shigar wadannan jihohi sun fi ta jihar nan. Kuma duka wadannan nasarorin sun samu asali ne daga gwamnatotin PDP da suka shude. Saboda haka ba za a ja wannan batu, nasarorin da gwamnatotin PDP da suka shude suka cimma a fannonin rayuwa daban-daban a jihar nan ba su kwatantu da wadanda gwamnatin jam’iyyar APC suka cimma a halin yanzu wato na jam’iyyar PDP sun dara na APC. Domin ai shi gwamna Umar Almakura abin da yake yi yanzu yana kammala wasu ayyukan gwamnatotin PDP da suka shude ne a jihar nan.
Aminiya: Mai ya baka sha’awar fitowa neman takarar kujerar gwamnan jihar Nasarawa?
Dokta Agabi: Da farko dai abin da ya ba ni sha’awar fitowa takarar kujerar gwamnan jihar nan na ga na cancanta ne wato ina da duka abin da ake bukata mai neman kujerar gwamna a kasar nan ya samu. Na kuma yi aiki a fannin tattalin arziki ina so na yi amfani da wannan kwarewana ne in kawo wa jihar nan dimbin ci gaba da ba wanda ya taba tunanin haka. Na biyu kuma shi ne na lura cewa al’ummar jihar nan yau sun tsinci kansu a wani irin hali da ke matukan bukatar taimako da agaji. Ba inaso in fito takarar saboda tara dukiya wa kaina da iyalena ko wani abu makamancin haka ba. Kaji kadan daga cikin abubuwa da suka bani sha’awar fitowa neman takarar gwamnan jihar nan ke nan a zaben shekarar 2015.
Aminiya: Jihar nan na daya daga cikin jihohin kasar nan da suke fuskantar rikicin kabilanci. Me kake ganin yake jawo wannan ?
Dokta Agabi: Ni dai na fada kuma zan sake yi amfani da wannan damar na nanata cewa wadannan rikice-rikicen musamman na kabilanci da wasu sassan jihar nan suke fuskanta a halin yanzu suna faruwa ne sakamakon mummunan shugabancin jam’iyyar APC. Shugabanci ne da ake yi babu tsari. Shi ya sa al’ummar jihar nan a halin yanzu suke matukar bukatar shugaba mai hangen nesa kamar irinmu da za su kwatosu daga halin kunci da suka sami kansu ciki yau. Kuma wani abu da ya sa tashe-tashen hankulan suka ki ci, suka ki cinyewa shi ne yadda gwamnati mai ci ta Almakura ba ta dauki kwararren matakai wajen kawo karshen wadannan rigirgimu. Yakamata ace gwamnati ta daukar kwararren matakai da suka wajaba wajen kawo karshen wadannan rigirgimu gaba daya, amma ba ta yin hakan. Shi ya sa ake ci gaba da fuskantar matsala a jihar nan kusan kullum. Ka ga shugabannin APC suna fada ne a baki kawai cewa suna kaunar talakawa. Amma ba sa nuna haka a fili. Saboda haka kamar yadda na bayyana a baya wadannan rigirgimu musamman na kabilanci da suka ki ci suka ki cinyewa a jihar nan sakamakon mummunan shugabancin gwamnati mai ci yanzu ne na Almakura. Kuma idan ba al’ummar jihar nan sun fito kwansu da kwarkwata sun canja gwamnati mai ci yanzu ba babu shakka za a wayi gari wata rana a manta da jihar nan baki daya a tarihin kasar nan.
Aminiya: To, amma sau da yawa gwamnati mai ci yanzu a jihar nan takan bayyana cewa ta gaji wadannan rigirgimu daga gwamnatotin PDP da suka shude ne. Me zaka ce game da haka?
Dokta Agabi: Ni dai zan iya karyata wannan batu da babbar murya na cewa wadannan rigirgimu masu tsanani sun samu asali ne daga gwamnatotin PDP da suka shude a jihar nan. Kodayake, babu shakka a lokacin da wadannan gwamnatotin PDP ke mulki a jihar nan an fuskanci rigirgimun kabilanci da sauransu. Amma ba su yi zafi irin yadda muke gani a yau ba. Wannan shi ne karo na farko a tarihin jiharmu ta Nasarawa da al’ummar jihar nan suka rasa rayukansu fiye da misali sakamakon rikicin kabilanci da sauransu. Haka suma jami’an tsaro ba su taba rasa rayukansu da dama a kasa ma baki daya kamar yadda suka yi a jihar nan kwanakin baya. Hakan ya lalata mana suna a idon duniya baki daya. Dazarar an sami irin wadannan rigirgimu a lokacin mulkin PDP za ka ga gwamnonin sun dakile su cikin gaggawa ta hanyoyi da suka dace za ka ga an kawo karshensu cikin gaggawa. Amma ba haka abin yake ba a yau. Saboda haka mun san an samu rigirgimun kabilanci da sauransu a lokutan gwamnatotin PDP da suka shude a jihar nan, amma ba ta yi zafi kamar yadda take a yau ba. Kuma ba ta dauki lokaci mai tsawo irin wannan karo ba.
Aminiya: Ya ya gaskiyar batun cewa duka ‘yan takara tara na PDP kuna shirin janye wa mutum daya?
Dokta Agabi: Ba shakka muna tunanin yin hakan. Muna nan muna tattaunawa da masu ruwa da tsakin jam’iyyarmu akan batun. Muna so mu tantance mu ga wane ne cikinmu zai iya karawa da gwamna mai ci yanzi. Amma a halin yanzu inaso in tabbatar maka cewa bawai yabon kai ko wani abu kamar haka ba. Ni Alhaji Dokta Yusuf Agabi ne kawai cikin mutum tara nan zan iya karawa da gwamna Umar Almakura, na kuma karbe mulki daga gunsa.