Mummunan shugabanci ya jawo faduwar PDP a karamar Hukumar Keffi – Shugaban APC

Shugaban riko na Jam’iyyar APC kuma Sakataren jam’iyyar a karamar Hukumar Keffi da ke Jihar Nasarawa Alhaji Garba Ruwan Sada ya bayyana faduwar Jam’iyyar PDP a zaben shugaban karamar hukumar da aka gudanar kwanakin baya a matsayin rashin samun karbuwa a wurin al’ummar Keffi ba wai kuskure a tsakanin magoya bayan PDP ba.Alhaji Garba Ruwan […]

Mummunan shugabanci ya jawo faduwar PDP a karamar Hukumar Keffi – Shugaban APC
Mummunan shugabanci ya jawo faduwar PDP a karamar Hukumar Keffi – Shugaban APC

Shugaban riko na Jam’iyyar APC kuma Sakataren jam’iyyar a karamar Hukumar Keffi da ke Jihar Nasarawa Alhaji Garba Ruwan Sada ya bayyana faduwar Jam’iyyar PDP a zaben shugaban karamar hukumar da aka gudanar kwanakin baya a matsayin rashin samun karbuwa a wurin al’ummar Keffi ba wai kuskure a tsakanin magoya bayan PDP ba.
Alhaji Garba Ruwan Sada yana mayar da martani ne kan da’awar dan takarar neman shugabancin Jam’iyyar PDP a karamar hukumar, Alhaji Muhammed Aliyu Babayo ya yi ta cewa kuskure aka samu PDP ta fadi zabe a yankin a kwanakin baya.
Alhaji Garba Ruwan Sada ya shaida wa Aminiya a makon jiya cewa, guguwar canji ta yi awon gaba da PDP ne sakamakon mummunan shugabanci da Jam’iyyar PDP ta dade tana gudanarwa a karamar hukumar da jihar.
Alhaji Ruwan Sada ya musanta zargin da Alhaji Babayo ya yi na cewa APC ta kasa cika alkawuran da ta yi wa al’ummar karamar Hukumar Keffi a lokacin yakin neman zabe, inda ya ce duk da cewa gwamnatin APC ta tarar da matsaloli da dama a karamar hukumar, amma kawo yanzu ta samar wa matasa da dama sana’o’i tare da ba su tallafin karatu da jari da sauransu don inganta rayuwarsu.
Ya ce batun daukar jama’a aiki ba nauyi ne da ya rataya a wuyan gwamnatin karamar hukumar kadai ba, aiki ne da a cewarsa yana kan wuyan gwamnatin jihar da ta tarayya da kamfanoni da sauran jama’a.
Ya ce akwai asibitoci da rijiyoyin burtsatse da dama da gwamnatin APC ta samar wa al’ummar karamar hukumar, inda ya bayyana zargin da dan takarar na PDP yayi da siyasa kuma marar tushi.
Alhaji Ruwan Sada ya kara da cewa tunda aka kirkiro karamar Hukumar Keffi al’ummarta ba su taba samun ribar dimokuradiyya a zahirance kamar yadda suke samu a karkashin shugabancin APC a yanzu ba.
Game da zargin cewa shugaban karamar hukumar, Alhaji Muhammed Dikko ba ya jin shawarwarin da za su kawo ci gaba a karamar hukumar, Alhaji Garba ya ce shi shaida ne cewa Dikko mutum ne da a koyaushe yake shirye ya yi amfani da kyawawan shawarwarin da za su kawo ci gaba a karamar hukumar, inda ya ce sai dai Dikko ba zai taba aiki da muguwar shawara ba.
Daga nan ya yi amfani da damar inda ya shawarci al’ummar karamar hukumar su yi watsi da zargin da Alhaji Babayo ya yi, inda ya ce ya yi haka ne kawai don ya ja ra’ayin jama’a su zabe shi a matsayin shugaban PDP na karamar hukumar. Ya bukaci al’ummar yankin su ci gaba da bai wa Jam’iyyar APC cikakken goyon baya don ci gaba da samar musu da ribar dimokuradiyya a karamar hukumar da jihar baki daya.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne dan takaran shugaban Jam’iyyar PDP a karamar Hukumar Keffi, Alhaji Muhammed Aliyu Babayo ya zargi gwamnatin APC a karamar hukumar da cewa ta kasa cika alkawuran da ta yi wa al’ummarta a lokacin da take yakin neman zabe.