Mun amince da tazarcen Tinubu da Namadi a 2027 — Dattawan APC a Jigawa

An cimma wannan matsaya ne a ranar Lahadi yayin wani taron kolin kwamitin, wanda ake ɗauka a matsayin mafi girman hukuma ta yanke shawara a jam’iyyar a matakin jiha, wanda ya samu halartar manyan jiga-jigan APC daga yankunan sanatoci uku na jihar.

Mun amince da tazarcen Tinubu da Namadi a 2027 — Dattawan APC a Jigawa

Kwamitin Dattawa na Jam’iyyar APC a Jihar Jigawa ya bayyana goyon bayan tsayawar Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Umar Namadi, takarar neman wa’adi na biyu babu hammayya a zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna na shekarar 2027.

An cimma wannan matsaya ne a ranar Lahadi yayin wani taron kolin kwamitin, wanda ake ɗauka a matsayin mafi girman hukuma ta yanke shawara a jam’iyyar a matakin jiha, wanda ya samu halartar manyan jiga-jigan APC daga yankunan sanatoci uku na jihar.

Da yake karanta sanarwar bayan taron, Shugaban APC na jihar, Ahmed Garba MK, ya ce an ɗauki matakin ne bayan tattaunawa mai zurfi da shugabannin jam’iyyar suka yi, inda aka amince baki ɗaya kan batun. A cewarsa, kwamitin ya amince Shugaba Tinubu ya sake tsayawa takara, tare da goyon bayan Gwamna Namadi domin neman wa’adin mulki na biyu a 2027.

A cewarsa, dattawan sun kuma ɗauki alhakin tafiyar da dukkan matakan tsayar da ’yan takarar biyu, har da saya musu fom ɗin takara. “Kwamitin dattawa ya amince cewa za su sayi fom ɗin takara ga shugaban ƙasa da kuma gwamnan jihar,” in ji Garba.

Ya ƙara da cewa jam’iyyar a jihar ta zaɓi hanyar sulhu maimakon gudanar da zaɓen fidda gwani, domin tabbatar da haɗin kai gabanin zaɓen. “Mun amince baki ɗaya da amfani da tsarin sulhu wajen zaɓen ’yan takararmu a zaɓen da ke tafe,” in ji shi.

Domin aiwatar da wannan matsaya, kwamitin ya amince da kafa tsare-tsare a matakin jiha da ƙananan hukumomi, domin jagorantar yadda za a fitar da ’yan takara a sauran mukamai.

Ya bayyana cewa masu neman takara a majalisun dattawa, wakilai da na jiha za su bi matakan tantancewa, inda za a fitar da ɗan takara guda ɗaya ta hanyar sulhu a kowane matsayi.

Wannan matsaya ta samu cikakken goyon baya daga wakilan yankunan sanata uku na jihar.

Da yake magana a madadin yankin Jigawa ta Tsakiya, Hon. Farouk Adamu Aliyu ya sake jaddada goyon bayan yankin ga shugabannin biyu, yana mai alƙawarin bayar da gudunmawa wajen sayen fom ɗin takara.

Haka kuma, Alhaji Isah Muhammad Gerawa na yankin Jigawa ta Arewa maso Yamma ya bayyana cikakken goyon bayan yankinsa ga Shugaba Tinubu da Gwamna Namadi a matsayin ’yan takara guda tilo.

Shi ma Sanata Muhammad Ibrahim Kirikasamma, mai wakiltar Jigawa ta Arewa maso Gabas, ya bayyana matakin a matsayin wanda aka amince da shi baki ɗaya, yana mai nuna ƙwarin gwiwa ga jagorancin shugabannin biyu.

Masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin wannan mataki na nuna yunƙurin shugabannin APC a Jigawa na ƙarfafa haɗin kai da shirin tunkarar zaɓen 2027 cikin tsari da haɗin kai.