Mun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta Jeddah — Dakarun RSF

Rundunar Sojin Sudan ta bayyana dalilan da suka hana ta halartar taron zaman lafiyar da aka yi a Geneva.

Mun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta Jeddah — Dakarun RSF

Dakarun RSF a Sudan masu fafata yaƙi da gwamnatin ƙasar sun bayyana shirinsu na aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka yi a Jeddah a Mayun 2023, wadda ta buƙaci janyewa daga gidajen fararen hula da wuraren al’umma.

“Muna ƙara nanata amincewarmu da tabbatar da yarjejeniyar Jeddah da muka yi alƙawari ga mutanen Sudan,” in ji Muhammad Al-Mukhtar, Kakakin Wakilan Tattaunawa na Dakarun RSF a wani taron manema labarai a birnin Geneva na Switzerland a ranar 25 ga Agusta.

Dakarun RSF ne suka yada bidiyon taron a kafar X.

Rundunar Sojin Sudan ta bayyana rashin tabbatar da yarjejeniyar a matsayin ɗaya daga cikin dalilan da suka hana ta halartar taron zaman lafiyar da aka yi a Geneva, wanda aka fara a ranar 14 ga Agusta, aka kammala a ranar 23 ga Agustan, ba tare da an cim ma wata matsaya ba.

Sai dai masu shiga tsakani sun sanar da cewa sun samu amincewar ɓangarorin domin “tabbatar da amfani da yarjejeniyar ta Jeddah.”

A ranar 24 ga Agusta Kwamandan RSF, Laftana Janar Mohamed Hamdan Dagalo (Hemedti) ya zargi Rundunar Sojin Sudan da kawo tsaiko ga ƙoƙarin tsagaita wutar, inda ya yi gargaɗin cewa hakan zai iya ƙara ta’azzara yaƙin.