Mun asassa makarantar dare ce don kawar da hankalin ‘ya’yanmu daga wasan dandali – Malam Alfa
Makarantar Ulumul Arabiyya da ke Unguwar Kwakwa Uku a garin Agege a Jihar Legas ita ce, makarantar dare ta farko a jihar wacce aka kafa ta shekara 35 da suka shude. A karshen makon jiya ne makarantar ta yaye dalibai 17 maza 10 da mata bakwai wadanda suka sauke Alkur’ani Mai girma a biki karo […]
Makarantar Ulumul Arabiyya da ke Unguwar Kwakwa Uku a garin Agege a Jihar Legas ita ce, makarantar dare ta farko a jihar wacce aka kafa ta shekara 35 da suka shude.
A karshen makon jiya ne makarantar ta yaye dalibai 17 maza 10 da mata bakwai wadanda suka sauke Alkur’ani Mai girma a biki karo na 17 da makarantar ta yi tana yaye dalibai tun daga 1990.
Aminiya ta zanta da daya daga cikin malaman makarantar Malam Usman Ahmad Alfa, wanda ya ce makasudin kafa makarantar shi ne a kawar da hankalin ’ya’yan Hausawan wancan lokacin daga zuwa dandali inda ba komai ake yi ba, sai tatsuniyoyi da wasannin dandali na gargajiya. Ya ce wadansu daga cikin dattawan Agege da suka hada da Khalifa Badmasi Yaron Baba da Malam Ahmadu Azare da Alhaji Sanin Ala da Alhaji Sunusi Madobi ne suka hadu suka kafa makarantar a karkashin shugabanci Malam Muhammad Is’hak wanda shi ne shugabanta na farko, kuma aka sanya mata sunan Darul Ulumil Kur’an wacce aka fi sani da sunan makarantar dare. Ya ce ana yin karatu bayan Sallar Isha’i zuwa karfe 10 na dare daga ranakun Asabar zuwa Laraba. Malam Alfa ya ce a cikin shekara 35 makarantar ta taka rawa wajen bai wa yaran Hausawan Agege ilimi da tarbiyya saboda lokacin da ake karatu, lokaci ne da ake dauke hankalin yara daga barin shiririta kuma lokacin karatu ne na musamman hadda Kur’ani ke zama a kan yara.
Malam Usman Alfa, ya ce babban kalubalen da makarantar ke fuskanta shi ne yadda iyaye ke yin sakaci wajen biyan hakkin malaman da ke koyar da ’ya’yansu. Ya ce zuwa yanzu ana aikin gina matsugunin makarantar na dindindin domin fadada ta lura da dinbin dalibanta da suka haura 200.
A karshe ya yi kira ga iyaye da su rika tallafa wa malaman wajen tarbiyyar yara kuma su rika kokarin biyan hakkokin malaman da ke kula da karatun ’ya’yansu, kuma ya yi kira ga masu iko su bai wa makarantar gudunmawarsu domin kammala aikin ginin makarantar.