‘Mun ba jihohi N32bn domin yakar COVID-19’

Babban Jami’in Kwamitin Kar-ta-kwana da Shugaban Kasa ya kafa kan yaki da cutar COVID-19, Dakta Sani Aliyu ya ce Gwamnatin Tarayya ta bai wa jihohi 32 Naira biliyan daya domin yaki da cutar. Sani wanda ya bayyana hakan yayin jawabin kwamitin a Abuja ya kuma yi kira ga jihohin wadanda bai ambaci sunayensu ba da […]

‘Mun ba jihohi N32bn domin yakar COVID-19’

Dakta Sani Aliyi

Babban Jami’in Kwamitin Kar-ta-kwana da Shugaban Kasa ya kafa kan yaki da cutar COVID-19, Dakta Sani Aliyu ya ce Gwamnatin Tarayya ta bai wa jihohi 32 Naira biliyan daya domin yaki da cutar.

Sani wanda ya bayyana hakan yayin jawabin kwamitin a Abuja ya kuma yi kira ga jihohin wadanda bai ambaci sunayensu ba da su yi amfani da kudaden kan dalilin da aka ba su.

Ya ce, “Mun fitar da kudade kwanan nan ga jihohi 32, kuma kowacce daga cikinsu ta samu Naira biliyan daya domin ci gaba da yaki da cutar. Saboda haka muna kira gare su da su yi amfani da su wajen kara yin gwaje-gwaje”.

Sai dai Dakta Sani ya ce har yanzu bai gamsu cewa an shawo ka cutar ba a Najeriya, yana mai kokawa kan karancin gwaje-gwajen da ake samu.

A ranar Alhamis din da ta gabata ce Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma shugaban kwamitin, Boss Mustapha ya yi ikirarin cewa kasar ta shawo kan cutar.

Sai dai Dakta Sani Aliyu ya ce za a iya yin wannan ikirarin be kawai idan an yi gwaje-gwajen yadda ya kamata.

Ya kuma yi gargadin cewa yin sakaci na iya yin barazana ga nasarar da aka samu yanzu haka.