Mun bai wa Akpabio sa’o’i 48 ya dawo da Sanata Natasha — SERAP
Dakatar da Sanata Natasha ba komai ba ne illa tauye mata ’yancinta na faɗin alabarkacin baki.

Ƙungiyar SERAP, mai fafutukar haƙƙin ɗan Adam da yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya, ta buƙaci Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio da ya gaggauta janye dakatarwar da majalisar ta yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
SERAP ta ce dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha ba komai ba ne illa tauye mata ’yancinta na faɗin alabarkacin baki, wanda Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya ba ta.
Cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da ta fitar a ranar 8 ga watan Maris, SERAP ta ce muddin ba a kiyaye wannan gargaɗi ba za ta ɗauki matakin shari’a nan da sa’o’i 48.
Wasiƙar mai ɗauke da sa hannun matamaikin shugabanta, Kolawole Oluwadare, SERAP ta ce kasancewar Natasha a matsayin Sanata ba zai haramta mata ’yancinta na faɗin albarkacin baki ba
SERAP ta nanata cewa dakatar da Sanata Natasha ya saɓa wa duk wasu tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya da kuma Dokokin Duniya da suka sahale mata ’yanci a matsayinta na bil Adama.
Ƙungiyar ta kafa hujja da sashe na 39 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya da kuma sashe na 9 na Kundin Kare Haƙƙoƙin ɗan Adam na Afirka, inda ta ce matakin da Majalisar Dattawan ta ɗauka ba bisa ƙa’ida ba ne kuma ya saɓa doka.
Ƙungiyar ta kuma yi Allah wadai da take haƙƙin da aka yi wa Sanata Natasha ta hanyar haramta mata wakilcin al’ummar mazaɓar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawan ƙasar.
A makon da ya gabata ne dai Majalisar Dattawa ta sanar da dakatar da Sanata Natasha Uduaghan tsawon watanni shida bayan kwamitin ladabtarwa na majalisar ya zarge ta da karya wasu daga cikin dokokinta.
Kwamitin ya yi zargin cewa Sanata Natasha ta yi magana ba tare da izini ba, kuma ta ƙi komawa sabon wurin zaman da aka sauya mata a zauren majalisar.
Har ila yau, an dakatar da albashinta da sauran haƙƙoƙinta na kuɗaɗe har tsawon lokacin dakatarwar, kuma an hana ta gabatar da kanta a matsayin Sanata.