Mun bai wa jami’anmu umarnin bincikar gwamnonin da ke kan mulki — EFCC

Za mu binciki gwamnonin da ke kan mulki amma sai bayan wa’adinsu za mu ɗauki mataki.

Mun bai wa jami’anmu umarnin bincikar gwamnonin da ke kan mulki — EFCC

Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede. (Hoto: EFCC)

Hukumar Yaƙi da Rashawa ta Najeriya EFCC ta umurci jami’anta su ɗauki matakin binciken hatta gwamnonin da ke kan gado kan aiyukan almundahana da yi wa tattalin arzikin ƙasar zagon ƙasa.

Shugaban EFCC, Ola Olukoyede ne ya bayyana hakan yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar Cibiyar Dimokuraɗiyya da Ba da Agajin Zaɓe reshen Afirka —International Institute for Democracy and Electoral Assistance — ta kai ziyara ofishinsa a wannan makon.

Ya bayyana cewa wannan na daga cikin matakan da hukumar ta ɗauka bayan nasara a Kotun Ƙoli kan gwamnonin nan 19 da suka ƙalubalanci hurumin kafa hukumar da kuma samar mata kuɗin gudanarwa.

Shugaban hukumar Ola Olukoyede ya ce hukuncin kotun da ya kori bukatar gwamnonin 19 da gwamnan Kogi Usman Ododo ya ke kan gaba wajen neman Kotu ta soke hukumar ya ƙara ba su ƙwarin gwiwa.

Olukoyede ya ce jami’an EFCC suna da dama su tattara bayanan tuhumar gwamnonin da ke kan kujerar mulki amma ba za a dau wani mataki a kansu ba na gurfanarwa a gaban kotu ko makamncin haka har sai bayan wa’adin gwamnonin ya ƙare.

A dalilin kariyar da doka ta bai wa gwamnonin ya sa a bayan nan mai bai wa shugaba Tinubu shawara kan sadarwa Bayo Onanuga, ya ɗora alhakin ɓoye tsohon gwamna Yahaya Bello wanda yanzu yake fuskantar sabuwar tuhuma ta zargin badaƙalar Naira biliyan 110 akan gwamna Ododo mai ci yanzu.

Mahaifiyar Gwamnan Jigawa ta rasu

Najeriya ba ta cikin ƙasashen da suka fi cin bashi a Afirka – IMF

Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Babiana

An horar da mutum 500 dabarun adana ruwa don inganta muhalli a Gombe