Mun bankado sunan jariran da ake biya albashi daga lalitar Borno – Zulum
Ya ce an gano hakan ne bayan aikin tantance ma’aikatan da aka yi.
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce an bankado sunan jarirai a jerin wadanda ake biya albashi daga lalitar Jihar.
Ya ce an gano sunayen ne a Karamar Hukumar Shani ta Jihar, bayan aikin tantance ma’aikata a Jihar.
- ‘’Yan bindiga suna aikata ta’addanci amma ba a ’yan ta’adda ba ne’
- Yadda siyasa take hana Kano ci gaba
Ana dai zargin cewa wasu jami’an gwamnati ne ke wawure albashin ma’aikatan bogin da ake da su a fadin Jihar.
Ya bayyana hakan ne yayin bikin al’adu na Menwara a garin Shani, ranar Asabar.
Gwamna Zulum ya ce tun da farko an kirkiro shirin tantance ma’aikatan ne domin gano na bogi daga cikinsu, amma masu adawa da hakan a Karamar Hukumar suka shirya zanga-zangar rashin nuna goyon baya.
Ya ce, “Ina sanar da ku cewa bayan kammala tantancewar, mun bankado sunayen jarirai a jerin ma’aikata, yayin da muka kuma gano cewa a duk wata, akan kashe Naira miliyan 19 wajen biyan ma’aikatan bogi a kowanne wata a Karamar Hukumar Shani.
“Akwai iyali daya da muka gano sunan ma’aikatan bogi 300. Ina fargabar in hakan ya ci gaba, akwai yiwuwar Karamar Hukumar ta gaza biyan albashi a nan gaba kadan,” inji Gwamnan.
Ya kuma yi zargin cewa guraben ayyukan da ya kamata a ba mutanen Karamar Hukumar ana sayar wa wasu akan N250,000, lamarin da ya ce yana hana matasan da suka yi karatu samun aiki.