Mun bude gidan rediyon Unity Jos ne don hada kan al’umma – Dasuki Nakande

Alhaji Ibrahim Dasuki Salihu Nakande tsohon Minista a Ma’aikatar Sadarwa a zamanin marigayi Alhaji Umaru Musa ’Yar’aduwa, shi ne ya bude gidan rediyon Unity a Jos da ake jin sa a sassan Jihar Filato da sassan jihohin Kaduna da Kano da Bauchi. A tattaunawarsa da wakilinmu ya bayyana manufofinsu na bude gidan rediyon da irin […]

Mun bude gidan rediyon Unity Jos ne don hada kan al’umma – Dasuki Nakande
Mun bude gidan rediyon Unity Jos ne don hada kan al’umma – Dasuki Nakande

Alhaji Ibrahim Dasuki Salihu Nakande tsohon Minista a Ma’aikatar Sadarwa a zamanin marigayi Alhaji Umaru Musa ’Yar’aduwa, shi ne ya bude gidan rediyon Unity a Jos da ake jin sa a sassan Jihar Filato da sassan jihohin Kaduna da Kano da Bauchi. A tattaunawarsa da wakilinmu ya bayyana manufofinsu na bude gidan rediyon da irin nasarorin da yake ganin sun cimma:

Aminiya: Me ya karfafa maka gwiwar kafa gidan Rediyon Unity?
Dasuki Nakande: Shi dai gidan rediyo yana da fuskoki daban daban. Amma mafiya yawa ana bude gidan rediyo ne don a wayarwa da kan jama’a ta hanyar bayar da labarai da ilimantarwa da nashidantarwa da sauransu. Wannan gidan rediyo na Unity na fara tunanin kafa shi ne tun a 1997, na sayi fom don neman izinin kafa shi, Allah da ikonSa ba a samu lasisin kafa shi ba, sai a shekarar 2010.
Daga nan muka himmatu muka nemo tallafi da taimako muka biya kudin lasisin, muka zo muka bude gidan rediyon a shekara ta 2012. Yanzu dai mun gode Allah domin gidan rediyon ya fara tsayawa da kafafunsa, muna fatar in Allah Ya yarda zai ci gaba har zuwa iyakar rayuwarmu. Kuma babban abin da ya karfafa mini gwiwar bude gidan rediyon shi ne don mu taimaka wa al’ummarmu su samu muryar da za su bayyana koke-kokensu da ra’ayoyinsu.
Aminiya: Daga bude gidan rediyon zuwa yanzu wadanne nasarori kake ganin kun cimma?
Dasuki Nakande: To, babbar nasarar dai ita ce yanzu gidan rediyon yana iya biyan kansa. Domin a farkon bude shi, mun yi wata shida kullum ni ne nake zuwa na himmatu a wasu harkoki don nemo kudin da za a biya ma’aikatansa albashi da sayen man da ake zuba wa janaretocin da muke amfani da su. Amma yanzu gidan rediyon na iya biyan ma’aikatansa albashi da kudin wutar lantarki da kudin mai da sauransu.
Amma babbar nasarar da muka samu a bude gidan rediyon, shi ne mun taimaka wa al’ummarmu wajen samun muryar da suke amfani da ita wajen isar da koke-kokensu, kuma mun samu nasarar ilimantar da al’ummarmu. Fatarmu ita ce mu ci gaba da yin wannan aiki har ya kai mu inda za mu sake bude wasu gidajen rediyon a wasu jihohin kasar nan.
Aminiya: Yaya ka ga yadda jama’a suka rungumi gidan rediyon?
Ibrahim Dasuki: Ai jama’a sun rungumi gidan rediyon hannu bibbiyu musamman saboda shirye-shiryen da muke gabatarwa da suke wayar da kan al’ummarmu.
Aminiya: Kamar a wasu wurare ne ake kama gidan rediyon?
Ibrahim Dasuki: To an ba mu lasisin kafa shi ne a iyakar wannan gari na Jos, amma saboda yanayi irin na na’ura, akalla ana kama gidan rediyo a kananan hukumomi kamar takwas da ke Jihar Filato. Bayan haka ana kama shi a sassan jihohin Kaduna da Kano da Bauchi.
Aminiya: Mene ne babban burinka game da gidan rediyon?
Ibrahim Dasuki: Burina shi ne gidan rediyon ya ci gaba da zama gidan rediyo har bayan rayuwarmu. Kuma burina na biyu shi ne mu ci gaba da bude wasu gidajen rediyon a duk inda ya kamata a cikin kasar nan. Kuma muna da burin mu bude gidan talabijin wato mu hada gidan rediyo da talabijin ta yadda idan an ji murya kuma a ga fuskarmu.
Aminiya: Me ya sa gidan rediyon ya yi ta gabatar da tallar Jam’iyyar APC da zababben Shugaban kasa Janar Buhari a lokacin yakin neman zabe?
Ibrahim Dasuki: Akwai babbar alaka tsakanina da Janar Buhari da kuma ita Jam’iyyar APC, domin tun muna Jam’iyyar ANPP mun yi tafiya da Janar Buhari har zuwa CPC da kuma APC. Saboda haka ni cikakken dan Jam’iyyar APC ne, don haka dole ne mu bayar da tamu gudunmawar ta gidan rediyon, shi ya sa muka yi ta bayar da tallace-tallacen Janar Buhari kuma ina alfaharin cewa sakamakon wannan gudunmawa ba tare da an biyu ko kwabo ba an samu gagarumar nasara.
Aminiya: Wace irin gudunmawa ce kake ganin gidan rediyo ya bayar wajen samar da zaman lafiya a Jihar Filato?
Ibrahim Dasuki: To, ai dama sunan gidan rediyon shi ne Unity wato hada kan al’umma don a samu zaman lafiya, kuma wannan suna da muka sanya wa gidan rediyo mun yi nazari kafin mu sanya shi. Saboda halin da muka samu kanmu a wannan jiha ta Filato musamman mu Musulmi an mayar da mu saniyar ware a gwamnatocin da suka gabata. Amma mu addininmu na Musulunci bai ba mu izinin mu nuna bambancin addini ko kabila ba. Don haka tunda muka bude gidan rediyon a kullum muna magana ne kan zaman lafiya kuma mun rungumi kowa da kowa a gidan rediyon, Musulmi da wanda ba Musulmi ba, suna nan suna aiki a gidan rediyon, domin mu hada kan al’umma. kudurinmu ke nan wato a samu zaman lafiya, ba ma yin wani abu da zai kawo bambance-bambance ko tashin hankali. Don haka daga lokacin da muka bude gidan rediyon zuwa wannan lokaci mun bayar da gagarumar gudunmawa wajen samar da zaman lafiya a Jihar Filato.
Aminiya: Wane kira kake da shi zuwa ga masu sauraronku da sauran al’umma?
Ibrahim Dasuki: Muna kira ga dukkan masu sauraronmu da sauran al’umma kan su taya mu da addu’a kuma su tallafa mana. Domin wannan gidan rediyo ya dore kan aikin da ya sanya a gaba na taimaka wa al’umma ta hanyar ilimantarwa da nishadantarwa da bai wa jama’a damar su fadi koke-kokensu.