Mun ceto Najeriya daga faɗa wa mummunan yanayi — Tinubu

Tinubu ya ce dole ce ta sa gwamnatinsa ɗaukar matakai masu tsauri domin ceto Najeriya.

Mun ceto Najeriya daga faɗa wa mummunan yanayi — Tinubu

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce da tuni Najeriya ta faɗa cikin mummunan yanayin matsin tattalin arziƙi ban da gwamnatinsa ta ɗauki matakan da suka dace a kan lokaci.

Da yake jawabi a fadar gwamnati da ke Abuja, Tinubu ya bayyana wa wata tawagar tsofaffin ’yan majalisa cewa dole ne gwamnatinsa ta ɗauki matakai domin tabbatar da kyakkyawan makoma ga ƙasar.

“Tsawon shekaru 50, Najeriya na kashe kuɗin ’ya’yanmu wajen samar da man fetur ga maƙwabtan ƙasashe. Dole ce ta sa muka tsara makomar yaranmu,” in ji shi.

Shugaban ya amince da cewa ana fuskantar ƙalubale a fannin tattalin arziƙi tun farkon mulkinsa, amma ya jaddada cewa matakan da aka ɗauka suna da muhimmanci.

“Muna cikin mawuyacin hali lokacin da na karɓi mulki. Idan ba mu ɗauki matakan da suka dace ba, tattalin arziƙin Najeriya zai durƙushe,” in ji Tinubu.

Ya kuma tabbatar wa ’yan Najeriya cewa abubuwa na ƙara gyaruwa, “A yau, muna kan turbar da ta dace. Farashin canjin kuɗi yana daidaituwa, farashin abinci yana raguwa, musamman a lokacin azumin Ramadan. Akwai nasara a tafiyar.”

Sanata Emmanuel Chiedoziem Nwaka, wanda ya jagoranci tawagar, ya yaba wa matakan Tinubu, musamman shirin bai wa ɗalibai rance domin tallafa wa iliminsu.