Mun ci ribar Naira biliyan 414 a cikin wata 6 a Najeriya – Kamfanin MTN

Kamfanin sadarwa na MTN ya sanar da cin ribar Naira biliyan 414 a watanni shida na farkon shekarar 2025 a Najeriya.

Mun ci ribar Naira biliyan 414 a cikin wata 6 a Najeriya – Kamfanin MTN

Kamfanin MTN

Kamfanin sadarwa na MTN ya sanar da cin ribar Naira biliyan 414 a watanni shida na farkon shekarar 2025 a Najeriya.

Kamfanin ya bayyana hakan ne a rahotonsa na karshen wata shidan da ya gabatar a gaban Hukumar da ke Kula da Kasuwar Hannun Jari ta Najeriya a ranar Alhamis.

A cewar rahoton, kamfanin ya kuma tafka asarar da ta kai ta Naira biliyan 90 saboda musayar kudaden kasashen waje.

Rahoton ya kuma ce jimillar abin da kamfanin ya samu a tsawon lokacin kafin a cire riba ya kai Naira tiriliyan daya da biliyan 200.

Kazalika, MTN ya ce kudaden shigar da ya samu daga kiran waya a watannin sun kai biliyan 887, yayin da na data kuma suka kai tiriliyan 1.23.

Kamfanin dai ya alakanta nasarorin da ya samu da ingantuwar yanayin kasuwanci a Najeriya, ciki har da daidaita farashin Naira da kuma saukar farashin kayayyaki.