Mun cimma nasarar kashi 92% na rancen awaki ga mata -Gwamna Badaru
shirin tallafa wa mata da rancen awaki, a matsayin rance maras nauyi a jihar.
Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar na Jihar Jigawa, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta cimma nasarar kashi 92% a shirinta na tallafa wa mata ta hanyar ba su rancen awaki, a matsayin rance maras nauyi a jihar.
Da yake magana kan batutuwa daban-daban da suka shafi jihar, ta cikin wani shiri mai taken ‘A Fada A Cika’ da Gidauniyar MacArthur, ta shirya ranar Alhamis a Abuja, gwamnan ya ce rancen wanda a cikinsa ake tallafa wa mata ta hanyar ba su awaki ya samu gagarumar karbuwa a tsakankanin matan jihar.
Sa’annan shirin tallafa wa matasa da sana’o’i shi kuma ya samar da ayyukan yi ga matasan fiye da dubu 150 a kananan hukumomin jihar 21.
Game da alkawarin da ya dauka yayin yakin neman zabensa – gina gidaje 50 a kowace karamar hukumar jihar, gwamnan ya amince cewa shirin ya samu tasgaro, sai dai ya tsaya kai da fata cewa an yi nasarar gina gidajen a yankuna 10 cikin 21 na jihar.
Sa’annan ya ce gwamnatin jihar na kokarin samar da dokar da za ta zartar da hukuncin daurin rai da rai ga wadanda aka kama da laifin aikata fyade.
Gwamnan ya kuma ce gwamnatin na kokarin haramta almajiranci a jihar ta hanyar hada tsarin karatun allo da kuma na zamani tare da karfafa wa iyaye gwiwa wajen daina tura yaransu almajiranci karkashin tsarin da ake yanzu.
Da yake magana kan samar da ruwan sha, gwamnan ya ce gwamnatinsa ta kashe fiye da naira miliyan 500 kan aikin ruwan Dutse ta hanyar kara yawan ruwan da ake samarwa daga lita miliyan 140 zuwa miliyan 245.
Hakan, a cewarsa yana daidai da kashi 80-90 na al’ummar jihar suke samun ruwan sha mai kyau. Wannan a cewar gwamnan ya sanya jihar zama ta biyu a fagen samar da ruwa ga al’ummarta a fadin Najeriya.
Da yake amsa tambaya kan munin yanayin da hanyar Basirka zuwa Gwaram mai nisan kilomita 60 a cikin jihar, gwamnan ya ce aikin gina hanyar na daga cikin manyan ayyukan da suka masa tsaye a rai.
ya bayyana cewa aikin hanyar na cikin kasafin kudin bana na jihar wanda annobar coronavirus ta yi wa mummunan mahangurba.
“Ina son tabbatar da cewa za a yi aikin nan da karshen shekara,” inji shi.
Game da batun nan da ake yawan ce-ce-ku-ce a kai inda gwamnatin jihar ta mallakar da gonaki masu fadin kadada dubu 12 ga wani kamfanin kasar China ba tare da an biya diyya yadda ya kamata ba ga manoman da aka kwace filayen nomansu, Badaru ya ce, “Ina tabbatar muku cewa fiye da kashi 80% na wadannan manoman sun yi na’am da abin kuma an biya su diyya.”