Mun daidaita tsakaninmu ni da Alpha – G-Fresh

G-Fresh ya ce nan da mako huɗu zai angwance da amaryarsa.

Mun daidaita tsakaninmu ni da Alpha – G-Fresh

G-Fresh Al-amin, ya bayyana cewa yanzu sun dawo jituwa da sabuwar masoyiyarsa, Alpha Charles Borno, bayan rashin fahimta da suka samu.

A bidiyon da suka wallafa a shafinsu na sada zumunta, suna rungume da juna, G-Fresh, ya nemi afuwar masoyansu kan maganganun da ya yi a baya.

Ya nemi afuwar waɗanda suka ɓata musu rai, tare da sanar da su cewa an sanya ranar bikinsu a ranar Asabar.

A ranar Talata, G-Fresh ya fito a bidiyo, inda ya nuna cewa lamarin aurensu da Alpha yana cikin matsala, kuma akwai yiwuwar a dakatar da shi.

Wannan ya haifar da muhawara a soshiyal midiya, inda wasu ke ganin cewa ba auren da za su yi ba, sai dai neman hankalin jama’a.

Sai dai a ranar Laraba, G-Fresh, ya kawo ƙarshen wannan magana, inda ya bayyana cewa yanzu komai ya dawo daidai.

“Mun samu daidaito tsakanina ni da amaryata. A baya an samu wata tangarda, amma yanzu komai ya gyaru.

“Don haka, duk wanda muka ɓata masa rai, muna neman afuwa. In sha Allah, bikin zai kasance tsakanin sati huɗu zuwa wata ɗaya.

“Zamu sanar da lokacin. Yanzu Alhamdulillah! Ina cikin farin ciki,” in ji G-Fresh.