Mun dakatar da neman tsige Ganduje —Matasan Arewa ta Tsakiya 

Kungiyoyin sun ce za su jira taron jam’iyyar na ƙasa don ganin matakin za a ɗauka.

Mun dakatar da neman tsige Ganduje —Matasan Arewa ta Tsakiya 

Gamayyar Ƙungiyoyin Matasan Arewa ta Tsakiya sun dakatar da fafutukarsu ta neman tsige Abdullahi Umar Ganduje daga kujerar Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa.

Shugaban gamayyar, Abdullahi Sale Zazzaga ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da sashen DCL Hausa a ranar Laraba.

Zazzaga, ya ce manyansu ne suka ja hankalinsu don dakatar yunƙurin nasu.

Ya ce, “Komai da ake yi ana yi ne saboda wani dalili. Shi ya sa muka [shiga] siyaysa don neman wannan ’yanci muna yi ne don cimma nasara.

“Dalilin shi ne cigaban yankinmu da al’umarmu da zaman lafiyar al’umarmu da bunƙasar tattalin arziƙi.

“Kowa da yake faɗin ƙasar nan ya san mun yi gwagwarmaya kuma ba za mu daina ba.

“Muna wannan fafutuka ne saboda cigaban al’umma. Amma duk abin da muke yi muna yi da manya.

“A cikin wannan tafiya da muke yi manyanmu sun kira mu sun zauna da mu, kuma sun ce lokaci ya yi da za mu dakata da wannan fafutuka saboda duk wanda ya kamata ya ji mu, ya ji mu, wanda ya kamata ya yi magana ya yi magana.

“Sun umarce mu da dakatar da wannan fafutuka tunda taron kwamatin zartarwar na jam’iyya na ƙaratowa nan da kwanaki.

“Sun ce mu jira mu ga me kwamatin zai yi a kai, duk abin da NEC ya yanke daga nan, sai mu san matakin da za mu ɗauka na gaba.”

Amurka za ta dawo wa Najeriya N80bn da ta ƙwato daga Diezani

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’

Zambar Intanet: EFCC ta kama ’yan China 4 da wasu 101 a Abuja