Mun dakatar da jami’inmu kan zargin roƙon kuɗi — NIS

An dakatar da jami’in da ake magana a kai ba tare da wani ɓata lokaci ba har sai an samu sakamako na ladabtarwa.

Mun dakatar da jami’inmu kan zargin roƙon kuɗi — NIS

Kwanturola-Janar ta Hukumar Shige da Fice ta Najeriya, Kemi Nandep

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) ta dakatar da Okpravero Ufuoma, wani Mataimakin Sufeto kan zargin roƙon kuɗi daga wani matafiyi.

Kwanturola Janar ta hukumar, Kemi Nandap ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Mista Kenneth Udo ya fitar ranar Alhamis a Abuja.

Bidiyon da ya ɗauki jami’in yana roƙon kuɗi daga wani matafiyi a halin yanzu yana yawo a shafukan sada zumunta, mai taken “Haka jami’an shige da fice ke ɗaukar masu yawon buɗe ido a Najeriya.”

Yayin da take bayyana nadamar kan abin da jami’in ya aikata, Nandap ta ce, wannan rashin ɗa’a da aka ɗauka a wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, ba ya nuna ɗabi’u da ƙa’idojin ƙwarewa da hukumar NIS ta yi.

“Wannan abin kunya ba ya nuna ƙwarewa da jajircewarmu na karɓar baƙi ballantana karramawa da kuma ladabi.

“Saboda haka, an dakatar da jami’in da ake magana a kai ba tare da wani ɓata lokaci ba har sai an samu sakamako na ladabtarwa,” in ji ta.

Nandap ta nanata ƙudurin NIS na ganowa tare da kawar da gurɓatattun jami’an da ke cikin muƙamanta da kawar dasu game da cin hanci da rashawa.

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar BRICS