Mun daura wa masu cutar sida 167 aure a Bauchi -Usman Ziko

Alhaji Usman Abubakar Ziko shi ne shugaban kungiyar masu dauke da cutar sida na Jihar Bauchi, yana dauke da cutar fiye da shekara 16. A tattaunawarsa da wakilinmu ya yi bayani game da matsalolin da suke fuskanta a lokacin da suke gudanar da harkokinsu na yau da kullum. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: Za […]

Mun daura wa masu cutar sida 167 aure a Bauchi -Usman Ziko
Mun daura wa masu cutar sida 167 aure a Bauchi -Usman Ziko

Alhaji Usman Abubakar Ziko shi ne shugaban kungiyar masu dauke da cutar sida na Jihar Bauchi, yana dauke da cutar fiye da shekara 16. A tattaunawarsa da wakilinmu ya yi bayani game da matsalolin da suke fuskanta a lokacin da suke gudanar da harkokinsu na yau da kullum. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Za mu fara tarihin kungiyarku?
Ziko: Mun kafa ta a shekarar 2000 kuma ni ne shugabanta na uku. Madam Rose Yusuf ita ce ta fara shugabancin kungiyar, sai aka zabi Hajiya Murjanatu Usman, sai kuma ni Usman Ziko da nake rike da shugabancin kungiyar a halin yanzu.
Aminiya: Tun yaushe ka kamu da cutar sida?
Ziko: Na kamu da cutar sida ne shekara 16 da ta gabata, kuma ina da mata biyu a halin yanzu, dukkansu suna dauke da cutar, amma suna shan magani kamar yadda nake sha, kuma dukkan matana babu wadda za ka kalli fuskarta ka ga wata alama ta damuwa, ina da ’ya’ya shida.
Aminiya: Mutum nawa ne suke dauke da cutar sida a Bauchi?
Ziko: Ba zan iya ce maka ga adadinsu ba, amma akwai wadanda har gobe sun ki fitowa fili su nuna kansu, saboda tsangamar wadansu mutane. Daga cikin mambobinmu mun daura wa mutum 167 aure, daga cikinsu 104 sun haifi ’ya’ya, kuma babu wanda ya harbu da cutar, domin akwai wani tsari da jami’an kiwon lafiya suka yi wa masu dauke da cutar. Jihar Bauchi muna da kananan hukumomi 20 ne, kuma dukkan kananan hukumomin muna da jami’an da suke aiki domin wayar da kan al’umma game da wannan cuta.
Aminiya: Shin wannan cuta raguwa take yi a Bauchi ko karuwa?
Ziko: Jihar Bauchi tana daya daga cikin jihohin Najeriya da ake samun raguwar masu dauke da cutar, sakamakon wayar da kan al’ummar jihar da hukumar BACATMA take yi ba dare ba rana. Abin da ya sa take raguwa shi ne, daga cikin masu dauke da cutar na shan magani.
Abin da nake so in fada wa al’umma shi ne, don Allah duk wanda zai yi aure ya je ya yi gwaji, domin gwaji shi ne hanya daya tilo da mutum zai iya fahimtar ko yana dauke da cutar sida, akwai mutane da dama a Bauchi wanda sun san cewa suna dauke da cutar, amma suka ci gaba da yada ta. Kuma ya kamata a fahimci cewa cutar ba ta kisa sai dai idan mutum ya yi watsi da shan magani ko kuma garkuwar jikinsa ba ta da karfi.
Aminiya: Tsakanin maza da mata su wa suka fi kamuwa da cutar?
Ziko: Ya kamata ka fahimci cewa cutar sida ta shafi maza da mata, kuma babu wani jinsi da za ka nuna ka ce ya fi kamuwa da cutar, amma kowa ya san cewa cutar ta fi jimawa a jikin mace, domin tana zubar da jini duk karshen wata idan ba ta da ciki. Amma bincike ya nuna cewa mata sun fi saurin kamuwa da cutar.

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi