Mun dora daga inda Ali Kwara ya tsaya —Halifansa

Kanin Ali Kwara ya ce Shugaban ’Yan Sanda da hukumomi sun amince ya ci gaba da ayyukan marigayin

Mun dora daga inda Ali Kwara ya tsaya —Halifansa

Marigayi Alhaji Ali Kwara, mai kama barayi a Najeriya

Ahmad Muhammad Kwara kanin marigayi Alhaji Ali Muhammad Kwara ne uwa daya uba daya, kuma shi ne ya gaje shi wajen yaki da ’yan fashi da barayi.

A makon jiya ne Kungiyar Matasan Arewa ta shirya taron lacca don tunawa da marigayi Ali Kwara kan irin gudunmawar da ya bayar wajen inganta harkokin tsaro da kasuwanci da taimakon al’umma a garin Azare.

Aminiya ta zanta da Ahmad Kwara kamar haka:

Me za ka ce kan wannan taro na tunawa da dan uwanka?

Gaskya lokacin da yayanmu yake raye ya yi ayyuka da dama kuma ya tsaya wa mutane da dama, ya taimaki al’umma kuma shi ma ya samu goyon bayan jama’a manya da kanana, don haka wadanda suka shirya wannan taro sun kyauta mana domin mu suka karrama shi kam ya yi nasa ya tafi ya bar mu da kewa da darussa masu yawa.

Mu ne muka ga abin da aka yi masa a yau sai dai addu’o’in da aka yi za su isa gare shi muna godiya kwarai da gaske.

Kai ke jan ragamar gidanku da kuma sana’arsa mafi wahala ta yaki da ’yan fashi da barayi. Ina aka kwana?

Alhamdulillahi tunda marigayi ya rasu ni ne aka bai wa ragamar wannan tafiya; kafn mu fara sai da muka nemi izinin manya a kasa kamar Shugaban Kasa da Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya.

Mun je mun zauna da shi na kuma samu izinin hukuma kan in ci gaba daga inda wana ya tsaya.

Kuma cikin shekara guda da rasuwarsa mun yi kokari sosai mun yi ayyuka da yawa tare da jami’an tsaron da muke aiki tare kuma an samu nasarori, ba wai a nan Jihar Bauchi kawai ba, har ma da wasu jihohin don mun shiga wasu yankuna a jihohin Kaduna da Katsina, kuma duka Allah Ya ba mu nasarori don mun kama barayi mun mika wa hukuma.

Yaya hadin kanku da jami’an tsaro?

A gaskiya sai godiya ga Allah domin muna tare da su, ka san wannan aiki kamar yadda marigayi yake fada muku kullum, aiki ne na taimaka wa jami’an tsaro don kama masu aikata laifi, don haka tare muke da su, su ne suke yin aikinsu mu dai muna taimaka musu ne.

Muna tare da ’yan sandan da muke aiki da su a ko’ina gida da waje, kuma lokacin da muka zauna da Sufeto Janar ya ba mu goyon baya sosai ya ce duk jihar da muka je za mu yi aiki za a kara mana karfin jami’an tsaro da za mu shiga daji da su mu yi aikin farautar barayin, in mun kammala kuma mu dawo da wadanda aka hada mu aiki da su gida.

Ka ga muna aiki da su ba wata matsala suna ba mu goyon baya sosai.

Gwamnatocin jihohin da kuka je yin aiki fa yaya dangantakarku take?

Alhamdulillahi su ma suna ba mu goyon baya da hadin kai sosai, duk da cewa aikin da muke yi akwai sirri a ciki, za mu iya samun bayanan wadanda ake zargi da aikata laifi, mu shiga gari mu yi aiki mu fito ba wanda ya sani.

Kuma wani lokaci kamar yadda wasu gwamnatocin jihohi suke neman gudunmawarsa lokacin yana raye, don a yaki ’yan fashi da makami muna samun hadin kai a kan haka.

Ka san muna amfani da wadanda suke ba mu bayanai kan maboyar barayin ne wani lokaci, mu yi musu kwanton-bauna mu rutsa su mu kama su.

Shi ya sa sai mu shiga mu yi aiki mu fita ba wanda ya sani.

Arewa tana fama da gungun masu garkuwa da mutane da suke zaune a cikin dazuzzuka. Shin kuna wani yunkuri na shiga dazuzzukan don yaki da su?

Gaskiya mun yi sosai musamman a yankinmu na kasar Katagum, ba wanda zai ce maka akwai wani mai garkuwa da mutane ko gungunsu a cikin dazuzzukanmu.

Mun yi yaki da su, Allah Ya taimake mu mun kore su daga ciki, ka san an ce yana da kyau mutum ya fara daga gida, don haka daga gida muka fara, kuma mun fita, don zancen da nake maka muna aiki a cikin dajin Jihar Katsina, muna kokarinmu a wajen, daga nan kuma za mu yi gaba.

Dajin Lame/Burra a nan Jihar Bauchi ma ana kukan cewa miyagun barayi sun buya a dajin ko ka kai sumame wurin?

Gaskiya ba mu shiga cikin wannan daji ba, amma mun yi magana kan wannan dajin na Lame/Burra da jami’an Gwamnati.

Kuma za mu shirya masa domin mu ba da gudunmmwa a tsarkake dajin cikin ikon Allah.

Mutum nawa kuka kama tunda kuka fara?

Gaskiya mun kama da yawa, a karamin lissafi mun kama barayi fiye da 50, kuma ka san kamar yadda marigayi yake yi in mun kama barawo muka tatsi bayanansa sai mu bar wa ’yan sanda su kai shi ya fuskanci hukunci a kotu.

Marigayi ya sha kokawa cewa yakan kama barawo sai ’yan sanda ko kotu su sake shi. Shin kai ma kana samun wannan matsala?

A yanzu dai ban samu wannan matsala ba, domin dukkan wadanda muka kama ’yan sanda da kotunan suna ba mu goyon baya, saboda duk wadanda na kama suna tsare a gidan gyaran hali.

Wace shawara za ka bai wa jama’a?

Gaskiya ba abin da muke nema a wajen jama’a kamar goyon baya da hadin kai da addu’a.

Muna bukatar addu’a kwarai a wajen jama’a, su kuma barayi muna shawartar su da su tuba su daina don ba abu ne mai kyau ba.

Masu iya magana sun ce rana dubu ta barawo rana daya ta mai kaya, saboda haka ko su tuba ko wata rana Allah zai ba mu nasara a kansu za a kama su a hukunta su da ikon Allah.