Mun fara binciken Dogara da Jibrin – EFCC
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta ce ta fara bincike kan badakalar cogen da ake zargin an yi a kasafin kudin bana.Kakakin Hukumar EFCC Mista Wilson Uwujaren, ya shaida wa BBC cewa sun aika takarda ga majalisar inda suka nemi a ba su wasu bayanai, kuma za su gayyaci dukkan wadanda […]
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta ce ta fara bincike kan badakalar cogen da ake zargin an yi a kasafin kudin bana.
Kakakin Hukumar EFCC Mista Wilson Uwujaren, ya shaida wa BBC cewa sun aika takarda ga majalisar inda suka nemi a ba su wasu bayanai, kuma za su gayyaci dukkan wadanda ke da hannu a lamarin domin bincikarsu.
Tsohon Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Abdulmumini Jibrin ne ya yi zargin cewa Shugaban Majalisar Yakubu Dogara da wadansu shugabannin majalisar sun cusa Naira biliyan 40 a kasafin kudin.
Jibrin ya bayyana haka ne, bayan cire shi daga shugabancin kwamitin, kuma ya yi zargin cewa an sauke shi ne saboda yana adawa da shirin kafa dokar kariya ga shugabannin Majalisar Dokoki ta kasa.
Batun ya jawo takaddama a cikin majalisar da kasar nan, inda wadansu ’yan majalisar da kungiyoyin jama’a suka bukaci a yi bincike a kan Dogara da Jibrin.
Jibrin dai ya mika wasu takardu ga hukumomin tsaro da suka hada da EFCC da ’yan sanda da DSS, inda ya nemi a binciki Dogara da wadanda yake zargi da hannu a badakalar.
Mista Wilson Uwujaren, ya ce nan gaba za su gayyaci shugaban majalisar da duk ’yan majalisar da ake zargi da hannu a lamarin. Ya ce Hukumar EFCC za ta hukunta duk dan majalisar da aka samu da hannu a badakalar.
A wani labarin, Fadar Shugaban kasa ta bukaci masu takaddamar da kada su sanya sunan Shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin hayaniyarsu ta coge a kasafin kudin.
Mai ba Shugaban kasa Shawara a kan Harkokin Majalisar Dattawa, Sanata Ita Enang ya ce babu ruwan Shugaba Buhari da hayaniyar cogen.Ya fadi haka ne bayan ya gana da shugabannin Jam’iyyar APC a ofishinta da ke Abuja a ranar Talata, inda ya ce fadar Shugaban kasa ba ta san komai ba game da badakalar.
“Mun zo nan ne bisa gayyatar shugabannin Jam’iyyar APC tare da abokin aikina domin mu amsa tambayoyin da jam’iyyar ta yi kan batun kasafin kudin na bana, kuma muna tare da jam’iyyar akalla na awa uku, kuma mun yi bayani kan kowane batu, babu abin da muka sani, babu coge a kasafin,” inji shi.
Ya ce: “Kasafin kudin da Shugaban kasa ya sanya wa hannu shi ne wanda majalisar ta amince kuma shi ake aiwatarwa.”