Mun fara biyan marasa karfi dubu biyar-biyar duk wata- Yemi Osinbajo

  Mataimakin Shugaban Kasa Ferfesa Yemi Osinbajo ya ce Gwamnatin Tarayya ta fara biyan marasa karfi dubu biyar-biyar a duk wata kamar yadda suka alkawarta.   Ya ce gwamnatin tana biyan wannan kudi tare da hadin gwiwa da Bankin Duniya a cikin shirinta na rage radadin talauci.   Osinbajo ya fadi hakan ne a ranar […]

Mun fara biyan marasa karfi dubu biyar-biyar duk wata- Yemi Osinbajo

 

Mataimakin Shugaban Kasa Ferfesa Yemi Osinbajo ya ce Gwamnatin Tarayya ta fara biyan marasa karfi dubu biyar-biyar a duk wata kamar yadda suka alkawarta.

 

Ya ce gwamnatin tana biyan wannan kudi tare da hadin gwiwa da Bankin Duniya a cikin shirinta na rage radadin talauci.

 

Osinbajo ya fadi hakan ne a ranar Litinin a lokacin da ya ziyarci Makarantar LEA a Abuja domin murnar ranar Littafi da satar fasaha ta duniya.

 

A jawabin, wanda mai taimakawa mataimakin shugaban kasar kan harkokin yada labarai, Laolu Akande, “Abin da muke yi yanzu na rage radadin talauci shi ne mu biya muliyan daga cikinsu dubu biyar-biyar a duk wata.

 

“Yanzu haka mun farad a mutum 300,000 inda muke biyansu dubu biyar-biyar a duk wata tare da hadin gwiwar Bankin Duniya bayan mun gano masu fama da tsananin talauci.

 

“Akwai matalauta da yawa. Mun yi kokari, kuma muna da shirin fadada shirin.”