DAGA LARABA: Mun fi son mulkin sojoji —Al’ummar Nijar
Me ya sa ECOWAS ke neman dawo da mulkin dimokuraɗiyya a Nijar, amma ’yan ƙasar ke son sojoji su ci gaba da mulki
Sati hudu bayan juyin mulkin Jamhuriyar Nijar inda ake ta kai ruwa rana tsakanin sojojin da suka hamɓarar da Shugaba Mohamed Bazoum da ƙungiyar ECOWAS da ke neman dawo da shi kan kujerarsa da kuma tsarin dimokradiyya a ƙasar.
Amma dubban ’yan Nijar sun sha yin gangamin goyon bayan juyin mulkin da kuma neman sojojin su ci gaba da mulkin ƙasar.
- NAJERIYA A YAU: Wuraren Da Wike Ke Shirin Rushewa A Abuja
- DAGA LARABA: Mece Ce Ribar Kai Gwamnati Ƙara
Shirin Daga Laraba na wannan mako, ya duba dalilin da ECOWAS ta nace a dawo tsarin dimokraɗiyya da kuma abin ya sa ’yan kasar ke neman sojoji su ci gaba da mulke su.
Domin sauraren shirin, latsa nan