Mun ga abin tsoro a hannun Boko Haram – Matan Sambisa

Wadansu daga cikin matan da sojoji suka kubutar da su daga dajin Sambisa inda ‘yan Boko Haram suka yi garkuwa da su sun bayyana wa Aminiya cewa sun ga abin tsoro a yayin zamansu a karkashin ‘yan Boko Haram din. A ranar 16 ga watan Disambar 2015 ne dai ‘yan Boko Haram suka shiga kauyen […]

Mun ga abin tsoro a hannun Boko Haram – Matan Sambisa

Wadansu daga cikin matan da sojoji suka kubutar da su daga dajin Sambisa inda ‘yan Boko Haram suka yi garkuwa da su sun bayyana wa Aminiya cewa sun ga abin tsoro a yayin zamansu a karkashin ‘yan Boko Haram din.

A ranar 16 ga watan Disambar 2015 ne dai ‘yan Boko Haram suka shiga kauyen Gumsiri da ke jihar Borno suka tafi da mata da yara kanana zuwa dajn Sambisa a inda ake kyautata zaton ‘yan matan Chibok na wannan dajin.
Wakiliyarmu ta zanta da wadansu matan da sojoji suka ceto daga hannun ‘yan Boko Haram din, inda suka bayyana cewa ba su hadu da ‘yan matan Chibok din ba amma suna jin labarinsu a bakin ‘yan Boko Haram din, inda suka tabbatar musu cewa ‘yan matan Chibok din na tsakiyar dajin Sambisa, amma su suna bakin shigar Sambisa ne. Wadansu daga cikinsu kuma sun ce sun samu labarin an aurar da wadansu ‘yan matan Chibok din, sannan kuma an mayar da sauran bayi.
Wakiliyarmu ta ruwaito cewa, da yawa daga cikin matan manya ne, kadan ne kawai matasa. Kuma kusan kowanne daga cikinsu na dauke da danta ko ‘ya. Haka kuma wadansu daga cikinsu sun samu rauni sakamakon harbe-harben da aka yi a tsakanin ‘yan Boko Haram da sojojin Najeriya, inda harsashe suka same su.
Aminiya ta lura cewa, lallai wadannan matan sun jikkata, domin akwai alamun yunwa da gajiya a jikinsu. Wadansu kuma har lokacin aka zanta da su ba su dawo cikin hayyacinsu ba.
Kodayake da yawa daga cikin matan sun ce ‘yan Boko Haram din ba su yi lalata da su ba, amma da wakiliyarmu ta ziyarci asibitin gwamnatin tarayya da ke Yola domin zantawa da wadanda suka samu rauni ta lura akwai wadanda babu alamar harbin bindiga a tare da su, amma duk da haka an kwantar da su a asibitin.
Wata mai suna Hauwa, wadda ta ce ita ‘yar Dambowa ce, ‘yar shekara 28, ta ce ‘yan Boko Haram din sun kai musu hari ne a rannar Jummu’a 16 ga watan Disambar 2015. Ta ce ta ga abin tsoron da ba ta taba zato ba, domin an kashe mutane hudu ‘yan uwanta na jini a gabanta, daga ciki akwai mahaifinta da yayyinta uku.
“A gaskiya sun ci mana mutunci, domin sun bar mu babu kyakkyawar kulawa, sannan abincin ma idan an ba mu yau sai bayan kwana biyu suke sake kawo mana wani. Mu muke girkawa da kanmu. Suna auna mana garin masara da kuka. Babu wani kayan hadi, daga wannan kukan sai ruwa sai gishiri.” Inji ta.
Hauwa ta kara da cewa, “ mun yi watanni uku da mako daya a Gwoza, daga nan sai ‘yan Boko Haram suka samu labarin cewa sojoji na zuwa, sai suka sa muka tako daga Gwoza zuwa kauyen Bita, a inda muka yi makonni uku. Suka sake cewa sai dai mu je daji domin sojoji sun kusan zuwa. Sai muka je daji. Ba mu sani ba ko sun yi lalata da wadansu daga cikinmu, amma mu kam ba su yi lalata da mu ba. Mun samu labarin ‘yan matan Chibok suna tsakiyar dajin Sambisa, an aurar da shida, an rabar da wadansu kuma an mayar da wadansu bayi.”
Wata kuma mai suna Fatima Usman, cewa ta yi, “ni ‘yar Gumsiri ce, amma ban san shekaruna ba. Da suka kama mu sun kai mu Gwoza ne, sannan sai suka kai mu Beita suka ajiye mu a wani daji muka yi kusan wata daya a karkashin wata bishiyar dinya. A yayin wannan tafiyar da muka yi da yawa daga cikinmu sun rasu, kuma idan sun rasu haka ake barin gawarsu mu cigaba da tafiya. Muna cikin tafiya sai suka ce sun manta hanya, haka a cikin gajiya muka sake komawa baya sannan suka samu wani kogi sai suka ajiye mu a nan. Suka sake cewa bai kamata mu kwana a wajen ba, sai muka sake ci gaba da tafiya sai dajin Sambisa. Munyi wata daya a wajen. A kalla yara shida sun rasu a wannan dajin saboda rashin abinci da kuma rashin kula.”
Fatima ta yi bayanin cewa, an kama ta tana da ciki wata takwas, bayan wata goma da kwana goma sai ta haihu. Sai dai da yake akwai alamar tana da ciwon jeji a mamanta, don haka ’yar da ta haifa na tsawon mako daya ne kawai ta sha nono. “Idan mun tambaye su madara haka suke ba mu kowane irin madara mu dura mata. Ga ciwon nono ya dame ni. Wata mata ta taimaka mini a dajin da itatuwa, idan ta daka ta kwaba mini da ruwa. Ga daci ga yunwa, haka zan sha domin in samu sauki. Yanzu ‘yar tawa watanninta biyu da kwana sha hudu.”
Ta ce ba ta sani ba ko mazajensu na nan da rai ko babu. Domin bayan sallar la’asar ne suka ji karar bindigar ’yan Boko Haram, suna harbi suna kabbara, a hanyarsu ta guduwa ne suka hadu da su suka kama su.
Wata kuma wadda bat a so a bayyana sunanta ta ce, lallai ‘yan Boko Haram sun ci musu mutunci kuma sun yi lalata da wadansunsu.
Ita kuwa Kolo Jitiya, cewa ta yi sunan mijinta Talba, kuma tana da yara bakwai. “Na bar yara uku a gida, lokacin da aka dauko mu ina da yara uku a hannuna sannan kuma ina da ciki wata hudu tare da ni. dana daya ya bata cikin ribibi, dayan kuma dan shekara uku jiya Allah Ya yi masa cikawa saboda yunwa. Suna bamu abinci amma dan nawa ba ya iya ci. Wanda ya batan kuma sunansa Girema, dan shekara biyar ne, ko yana wajen sojoji ban sani ba.”
Wata kuma mai suna Falmata, wadda ta samu rauni ta ce, harsashe ne ya shige mata kafa, kuma akwai yaro a kwance kusa da ita wanda aka sanya masa ruwa ta kai, amma ta ce bata san me ke damun dan nata ba. Ga dukkan alamu dai har yanzu ba ta dawo cikin hayyacinta ba.
A garin Makalho kuma inda aka ajiye ‘yan matan na Sambisa, wakiliyarmu ta zanta da wadansu daga cikinsu, inda wata mai suna Aisha ‘yar jihar Adamawa ta bayyana cewa, “ina Madagali ne sai ‘yan bindigan suka zo suka zauna a cikin garinmu, sai suka tara mu wuri guda, suka ce wa mazajenmu su fito su je wajen karatu. Da suka fito sai suka ce, ‘wa ke da uzuri a cikinku?’ Wanda yake da uzuri ya fada, wanda kuma ba shi da uziri ya fada. Wadansu masu nisan kwana suka ce su ba su da uzuri, sai suka ce su shiga layin nan, ku da kuke da uzuri kuma ku zauna a bangaren nan. dari shida suka ce suna da uzuri, dari biyar kuma suka ce ba su da uzuri. Sai suka harbe wadannan dari shidan da suka ce suna da uzuri ba tare da tambayar uzurinsu ba. Sai suka ce masu uzurin arna ne, domin ba za su yi aikin Allah ba.”
Ta ce, tun da safe aka dauki mazajensu. Yadda suke ganewa ko an kasha mazajensu shi ne, idan bayan issha mazan ba su dawo gida ba to alama ce na cewa an kashe su.
Ta ci gaba da cewa,“da suka samu labarin sojoji na zuwa sai suka dauke mu daga Madagali zuwa Gwoza. Daga nan suka kai mu Bita, wani kauye a Gwoza, daga nan sai Sambisa. Amma ni watanni uku na yi a hannunsu. Rannan muna zaune sai muka ga jirage na saukowa tare da harbi, sai muka shiga gudu. Daga baya muka gane cewa sojoji ne, sai suka ce da mu, mu kwanta ba za su taba mu ba. Bamu hadu da ‘yan matan Chibok ba, domin su kauyensu na gaba da namu.