“Mun ga canji a hukumar Kwastam”

Shugaban kungiyar masu sayar da motoci na Jihar Kaduna, Alhaji Ahmad Abdullahi Nabrazil ya bayyana cewa sun fara ganin canji mai ma’ana tunda Kanar Hamid Ali (Mai ritaya) ya kama ragamar shugabancin Hukumar Kwastam ta kasa. A cewar shugaban, a halin yanzu an samu ci gaba a abubuwan da suke fitowa ta Hukumar Kwastam. Ya […]

“Mun ga canji a hukumar Kwastam”
“Mun ga canji a hukumar Kwastam”

Shugaban kungiyar masu sayar da motoci na Jihar Kaduna, Alhaji Ahmad Abdullahi Nabrazil ya bayyana cewa sun fara ganin canji mai ma’ana tunda Kanar Hamid Ali (Mai ritaya) ya kama ragamar shugabancin Hukumar Kwastam ta kasa.

A cewar shugaban, a halin yanzu an samu ci gaba a abubuwan da suke fitowa ta Hukumar Kwastam. Ya kuma bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai a makon da ya gabata. “Saboda haka muna yaba masa kan wannan matsayi da Allah Ya ba shi, domin mun fada masa a lokacin da muka zauna da shi cewa mun fara ganin canji daga gare shi; domin soja ya rikide ya zama Kwastam.” Inji shi.
A game da zama da suka yi da shugaban na Kwastam, sai Nabrazil ya ce: “Ya bayyana mana cewa kasa ta samu canji, don haka mu ma ta bangaren sana’armu wajibi ne a samu canji. Kuma mun yi masa fatan alheri, mun bayyana masa mu ma ’yan kasa ne nagari masu kishi.
Da yardar Allah za mu tsaya wajen ganin mun yi abin da ya kamata a harkarmu ta saye da sayar da motoci.” Inji shi. Ya kuma kara da cewa sun roki Hamid Ali da ya saukaka masu harajin shigo da motoci, domin a gaskiya idan kudin harajin shigo da motoci ya yi tsada, to al’umma ba za su samu sauki wajen sayen motoci ba.
Ya kuma yaba wa Gwamna Nasir el-Rufai game da yadda ya yi tunanin samar da motoci domin samar da saukin zirga-zirga a tsakanin jama’a a jihar.