‘Mun ga canji a wannan gwamnati’
Shugaban Jam’iyyar APC na Kagarko ta Kudu, Habibu S. Baka ya bayyana cewa duk da halin matsi da ake ciki a kasar nan, idan aka auna nasarorin da gwamnatin APC ta samu ta fuskar samar da zaman lafiya za a ga cewa ba karamin ci gaba aka samu ba, domin sai da zaman lafiya ake […]
Shugaban Jam’iyyar APC na Kagarko ta Kudu, Habibu S. Baka ya bayyana cewa duk da halin matsi da ake ciki a kasar nan, idan aka auna nasarorin da gwamnatin APC ta samu ta fuskar samar da zaman lafiya za a ga cewa ba karamin ci gaba aka samu ba, domin sai da zaman lafiya ake iya yin komai.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin zantawarsa da Aminiya a garin Kagarko da ke Jihar Kaduna, inda ya ce a lokacin wannan gwamnatin ne manoma kan yi noma su sayar da na sama da Naira miliyan 10 su amshi kudinsu su koma gida su kwanta su yi barci har da minshari saboda kwanciyar hankalin da aka samu. “Sabanin lokacin gwamnatin da ta gabata inda da zarar mutum ya sayar da kayan amfanin gonarsa koda ta Naira dubu 100 ne, to ba ya da kwanciyar hankali saboda zullumin za a bi shi har gida a yanka shi a kwace kudin,” inji shi.
Da ya waiwaya kan zaben kananan hukumomin Jihar Kaduna, ya ce abin da ya kamata mutane su fahimta shi ne kudin da za a kashe ba kadan ba ne saboda kudin da Gwamna zai ware ba kawai jam’iyyarsa zai bai wa ba, har da jam’iyyun da suke da ’yan takara don haka jama’a su yi hakuri da zarar an samu kudi za a gudanar da zabubbukan.
Shugaban ya yi kira ga gwamnati ta rika kokarin biyan ma’aikata albashi a kan lokaci duk da halin da ake ciki.
Shi kuwa Ciroman Kagarko kuma Hakimin Gwakuru, Alhaji Aliyu Tanko ya bayyana godiya ce ga gwamnatin jihar kan gyara musu makarantu da ta yi. Sai dai ya koka kan rashin isasshen taki ga manoma, inda ya ce sun yi noma sosai amma tsadar taki ta sa sun rage abubuwan da ya kamata su noma. Ya ce da tun farko gwamnati ta samar da wadataccen taki to da na ’yan kasuwa ya fadi kasa, don haka ya shawarci gwamnati ta taimaka musu da taki tunda har yanzu lokaci bai kure musu wajen noman citta ba.